← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 138

Sashe 68

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saka sababin kaya ba yau ya fara ba, sannan ba sai ana wani abin yake sakawa ba, sai dai na yau din a sabinma bugagu ne wa'inda suka amsa kiransu

Da hannunsa ya ciro su da sabon rawaninsu hade ya ciro duka ya ajiye gefen gadonsa

Zama ya yi ya dauki karamar wayarsa ya danna kira

Tana fara ringin aka daga ana mai aiko da salama da neman fara kirari

Da sauri ya furta" yi shiru, abinda nake so da ke ki saka a yiwa yan mata kamar goma kwaliya ya kasance an laya su a matsayin amaren nan da ake yi, ina so ku ringa gardamar ba zaku bayar da amarya ba,
Ina so ki saka mata simple shiri ki bata hijab da nikaf ta fara fita ta tsaya ki a cikin kwanar gidanku kafin ki sandi mutane ki fito
Akoy dan sahun da zai dauko ku ya kawo ku
Idan kun zo yau gidan ba'a hanna shiga ko fita, zaku samu hanyar shigowa
Idan kun shigo zan wakilta macen da zata sada ku da bangarenta sai ku gabatar da abinda zaku yi

Dan shiru ya yi yana sauke ajiyar zuciya kafin ya dago yar yatsarsa guda ya ce" ku kiyaye, rayuwarta ko nace rayuwarku baki daya ke cikin hadari, idan har kuka kuma falasa wani abin ko me ya biyo baya ku kuka da kanku

Yana gama fada ya datse kiran sannan ya dan dane lebensa na kasa

Kuma mikewa ya yi da tawul din dake jikinsa ya nufi wajen window din

Abubuwa da dama sun shiga idannuwansa, irin yanda ake waje waje ana kuskus daga inda yake ba zai fahimci komai ba sannan a yau ba zai fitar da droon ba har sai an fara hawa dokunna domin a yanzun ana cen ana hawan kaho ne ana ta zubda maza

Suturarsa ya ringa sakawa cikin adu'a da iya daukan wanka
Sai da ya saka abinda zai kara rufa asirinsa duda wandon shadar ba karami bane aman gwara a kara daurewa dan kar a ji kunya
A lokacin da ya dora babar rigar shi da kansa sai da ya tofawa kansa walahaula wala kuwata ila bilah domin dinkin ya dauke shi ya amshe shi sosai haka kuma kalar ta karbe shi sosai

Sai da ya saka farin yadi mai haske a fuskarsa mai shara shara kafin ya yiwa masu jiransa umarnin shigiwa dan gabatar da nadin rawanin da suka takanas dominsa

Su biyu ne, kwararu ne, aikinsu ne, nadin za'a hauda shi daidai yanda zai bada kalar tsuntsun da aka yi dinkin irin kalarsa wato Dawisu mai hasken fari kar kar kar sai dan kalar blue mai haske jefi jefi

Sosai suka gabatar da aikin nadin da ya dauki lokaci kusan minti talatin kafin su saka masa safa fara kar su saka masa takalmi kafa ciki shima farin ne kar kar mai kyan gaske domin fata ce akaiwa adon fari tas tas

Dawisu ya gama bayana a lokacin da suka miko masa sandar sarautarsa,
Sandar baka ce mai adon zeba daga sama
Sandar wata irin sanda ce mai shegen kyau ga tsada
Rike sandar da ya yi a hannunsa na dama a lokacin da ya mike tsaye ya kara masa wani irin cika da girma
Baki daya ya haske wajen har ya kasance su da kansu suka shiga kirarin dole domin kuwa wani yabon zaka yi shi ne a lokacin da kai kanka baka sani ba

Irin yanda karamar wayar da zai rike ta sha masa kai da ringin ya saka shi dubawa

Idannuwansa ya lumshe, bai san yaya aka yi suka cika takura ba , auntyn Nadia ce wace take kanwar mamanta uwa daya uba daya, da kansa ya amshi numberta bisa kwakwaran gargadin kar ta yarda wasu su san yana magana da ita sai Nadiar sai mamanta

Dagawa ya yi ya kara a kunnensa bai yi magana ba

Sai da ta kara sada kanta sosai sannan ta yi tambayar zuwa wani lokaci ne?

Idannuwansa ya daga ya kai wajen agogo, daurin auren a yanzu bai fi saura minti goma na, dan haka sai ya sada idannuwan nasa a hankali ya ce" bayan awa biyu da komawar *GUDGE MOCTAR*

Amsawa ta yi ya kashe wayarsa

Dubanta ta maida wajen yayarta da suka yi tsuru tsuru ita da Nadia sunna jiran amsar

Amsa ta basu dan haka suka shiga neman nikaf da bakin hijab domin kaf a cikin gidan babu ba mai sakawa!

Cike da kasaita ya ringa tafia
Yana fitowa dogaran dake laye a cikin katon falonsa suka kwashi wani irin kirari mai saka tsigar jiki tashi
Busa ce ta karade wajen irin ta sarakai hakan ya saka shi lumshe idannuwansa kafin ya bude ya sauke dubansa kan sarakai hudu da suka halarci taron da manya manyan mutanen da suka zo dan taya shi zaman wannan ranar

Da kansa da kuma idannuwansa ya yi anfani wajen gaisar da kowa ta hanyar dan sada kansa da kuma idannuwansa sai baban dogarin dake isar da sakonsa ya isar yana jinjina da hannayensa, sauran kuwa sai su kwashi kawo gaisuwa sunna fadin Sarkin garin maradi ya amsa gaisuwar *MAI WUKAR YANKA*, yana yiwa *GURNANIN ZAKI* fatan alkhairi

A haka dai har suka kara cinye wasu lokutan masu mahinmanci kafin a fita baki daya a bijiman dawakan dake dauke kwaliya ta mamaki da wata bazara a gefe dogarai majiya karfi suna ririke da ita

Sai da ya taka hannun Amintacensa kafin ya dora kafarsa daya a abin dokin sannan ya hau da kyau indo dogarai suka kare hawan nasa

Sai da ya zauna ya rike sorsin dokin sannan da kafarsa ya dan daki gefe da gefen dokin a hankali, nan fa dokin ya shiga wata tafiar kasaita domin yanda yake tafe fari kar da shi ga irin yanda yake daga wutsiyarsa mai dauke da yalwatacen gashi itama tana sama tana yawo irin ya koshin nan ya gaji da koshi kamar ya fashe tafiarsa ta koma ta kasaita

Haka aka layu anna ta rangada buda ga busa ga yan rakiya har suka fice daga fadar wada ba wanda bai fito gannin kwaliyar sarki da fitar sarki ba

Yayar Zinaria ta juyo tana gyada kanta ta ce" a gaskiya, da kamar wuya SULTAN SHAHEED ya iya zama da mace daya, koda bai je nema ba za'a zo neman alfarmar aurensa
Zinaria, ki duba ki ga yanda baki daya ya haske wajen cen, da ace nice ke, zan yi kwaliya irin tasa na bashi goyon bayan da zai saka ko wa ya karo sai dai ta biyo bayana! To ke Zinaria yaya kike tunanin mutun har haka ya zauna da ke daya? Kin yarda da kanki har haka ne? Wace irin kula kike bashi wace zata saka shi haka? Kar ki manta Aba da Abihnsa suka maku auren hadi, kar ki manta a zamanin nan mutun ko dan rufin asiri yake da shi shikenan ya kama hange hange bare wannan? Zinaria mijinki sarki ne, kuma mai kudi ne....yaya zaki kasa yiwa kanki adalci ki ringa summa dan zai yi aure?

Mahaifiyarsu ce ta daka mata wata irin tsawa ta hanyar fadin" kilishi anya kuwa ke jinni na ce? Baki san mulkinsa da dukiyarsan ne ya saka lale lale zamu tanadesu dan kanmu da y'ayanmu ba? Baban bakin cikina ace har yanzu babu wani abu da take da shi da zan iya fara dora rai a kansa, kilishi, ko ki min shiru, ko na hautsina kwonciyar hankalinki sakarai ke da kika ne kike yiwa kishiya bauta ai ke kika gani!

Shiru ta yi ta koma ta zauna domin ba zata furta wani abin ba kuma cibi ya zama kari, gani take da wannan zaman da suke sunna sake sake da kiraye kiraye da tsare tsare, da mikewa suka yi suka saka akai mata shiri irin na wanda ake yi, suka tarbi amaren nan da kansu da sai sun fi girgiza mutane, aman sun tare a nan sun hadu sunna ta abu kamar wasu jahilai
Ita kam gaskiya ko yanzu zata mike ne ta je wajen kiahiyarta domin tare suka zo da mijinsu sarkin tsatsunburun ne su shirya a tarbi amare da su, ita kam Alhamdulilah tana zaune da kishiyarta lafia, ita ta je ta sameta a gidanta da y'ayanta , matar tana da hali na datako hakan ya saka cikin nutsuwa suka hada kawunnansu suke zaune kalau, ko irin asiran da Gimbiya ke bata ta zuba a abinci dan ta raba su ita kam bata taba anfani da shi ba, tana amsa dan su zauna kalau da mahaifiyarta aman ko nisa bata yi take zubarwa ya bi iska domin ita dai bata dauki duniyar da zafi ba, kuma iliminta ya fi gaban wannan gaskiya, ta gane cewar idan ba kanka ka sauke, ka nemi zaman lafia da kowa ba to da dan da ka haifa ma sai dai ya bika dan dole!

Ana gama salar azahar aka gabatar da daurin aure
Auren da aka fara daurawa shine auren da ya saka zukata da yawa zabura da jin tamkar an dika masu guduma a kansu

A lokacin da aka furta kalmar sunnan nan wato *NAJEEBA MUTALAB* sosai zukata suka rikice, da yawa kuwa suka hangame baki cike da mamaki

HUZAIFA bai iya tsayawa ya ji sauran daurin auren ba ya fita daga cikin tanfatsetsen masalacin yana jin tamkar numfashinsa zai bar gangar jikinsa
Kuka ya fashe da shi a cikin abokansa yana son sai sun barshi ya doka kansa da madubin motarsa

Yana kukan yake fadin" ta cuce ni, ashe dama bata so na? Ashe dama mai gida zata aura shine ta yaudare ni? Dama ashe aurenta za'a daura na dinka sabuwar shada na zo ni ga sirikin sarki? Dama ashe aurenta za'a daura na zo nan? Nadiama ta cuce ni, ashe ta san haka ne ta barni nake ta fama da soyayar Najeeba a zuciyata?
Chapter 68 · 0% Book details