Sashe 66
Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da ta gama lumdeta sannan aka kuma tayar da ita aka rufa mata wani abin rufa aka saka wani mahaukacin turaran wuta mai wani irin sanyayan kamshi ya shiga ratsata domin a saman wata kujera ce mai hudoji direct ya ringa ratsa jikinta yana hawa ko'ina na jikinta yana kamawa sosai da sosai har ya gama sannan aka ciro wata wata riga fara kar aka bata ta saka mai dan tsayi kafin a bata safar kafa da ta hannu duka ta saka sai hula aka rufe mata kanta da ita mai dan gashishika mai laushin gaske
Anmy ce ta shigo tare da dayar matar wace ita kuwa aikinta shine hade haden tsumi kala davan daban
Tunn da ta ga Anmy sai ta ringa binta da kallo
Anmy kuwa tana kiyaye abinda zai saka su kadaice har sai da ta amshi abinda matar ta daho tantabaru ne da wani sirri ta dawo kusa da ita ta zauna
Budewa ta yi ta saka hannunta ta ringa bismillah tana ciyar da ita tana kiyaye bata da kasusuwa har ta cinye sannan ta saka cokali tana bata romon nan a hankali har ta shanye shi
Wata madara mai dan dumi ce Anky ta miko mata cike da bol mai dauke da sinadarai ta bata ta shanye
Sai da ta shanye tas ta mika mata
Mikawa matar ta yi ta juya ta koma domin rubutu ne take a allo tana rubuta yusufa da kanta dan hadin kankanar da zata yiwa Najeeba
Anmy zama ta yi a kusa da ita ta kamo hannayenta tana gannin yanda fatar Najeebar har ta wani irin daukan harama ga abin man nan ya saka hannayenta sunna santsi
Idannuwanta ta lumshe a sanyaye ta ce" Najeeba, zaki yi hakuri da abinda Allah ya hukunta?
Najeeba ta ringa kallon fuskar Anmy hakan ya saka Anmy jin wani iri, so take ta san me take tunani a zuciyarta, kar ta dauketa mai son kanta da yawa
Matar nan ce ta dawo ta ja abin zama ta zauna tana kallonsu
Murmushi ta yi ta nuna anmy da hannunta ta ce" ki rungumeta a jikin ki, ki fada mata dadadan kalamai
Ta kai dubanta wajen Najeeba ta sakar mata murmushi ta ce" kunya, da tsananin soyaya su rinjayi rigimarki a irin wannan lokacin
Anmy a hankali ta rungume Najeeba a jikinta tana dan taping din bayanta ta furta" i love u Najeebana, kin san me? Mamanki na hanya yau ko gobe zata zo
Najeeba ta rintse idannuwanta wasu hawaye masu dumin gaske suka zubo mata, mamanta? Zata zo? Ta zo ta yi me? Rabonta da Niger shekarun da dama, ahine yanzu zata zo ta mata me?
Bata dai ce komai ba har Anmy ta gama ta shinfideta da kanta sannan ta mike ta fita
Wani baci ne kai nauyin gaske ya dauketa na gajiya da kuma rudani
Bacin bata yi mafarkai a cikinsa ba, hasalima kamar wace ta mutu bacin kawai take du jikinta a gajiye
.......
Haka ya kasance a wuni za'a yi mata irin gyaran nan sau biyu, da dare kuwa za'a ringa koya mata yannayin magana da kuma yannayin cin abinci, da komai da komai wanda a gannin Najeeba kallonsu kawai take bata san cewa tana daukan yannayinsu ba domin su sun ga sosai tana daukan darusan su duda ba amsa take basu ba
Bayan kwana hudu mahaifiyarta ta zo, sai dai tun da ta zo ko da wasa idannuwansu basu hadu ba domin kuwa idan ta shigo dakin Najeeba koda a zaune take zata lumshe idannuwanta ne, ita kuwa zata tsaya ta yi murmushi daga nesa kafin ta juya
Tana azabtuwa da yannayin yarinyar nata
Sai dai bata da wani iko na tirsasata,
Ta samu DAYABU ta roki idan an fitar da ita ya rokar mata sasauci, Abih kuwa sam baya son abinda zai hada shi da ita domin matar tana da tasiri a rayuwarsa, zata haye masa ne a lokacin da bai shirya ba
Yau sauran kwana uku daurin aure
A yau da sasafe ya saka aka kira masa Zinaria
Sai da ya gabatar mata da tarin abubuwan arziki irin na fitar kishiya kafin cikin nutsuwa ya bata hakuri dan gannin ya samu bata yi irin na wancen karon ba sannan ya shaida mata cewar zai daura aure da mace biyu nan da kwana uku
Wani abin aka ce ya girmi hawaye, sai kawai ta ji zuciyarta ta dauki wani irin suka da zafin da ta yi gagawar dukewa
Hannunta na dama ta dora daidai wajen ta damka sai kawai ta tafi numfashinta ya dauke
Sosai ya shiga wani yannayi na ganninta a haka, meye wai a su kishiya? Meye dan zai yi aure sai ta ringa fmhayacinta? Ta san bata so ya yi aure aman sam bata iya bashi kulawar da yake da bukata? Subahannalah, subahannalah shine abinda ya ringa furtawa a kasan zuciyarsa
Sai da ya kira docter ta dubata ta bata taimakon gagawa kafin take dawowa hayacinta
Wannan karon kam ta kasa dane kukanta da ihunta, sosai take kuka ta rikice masa tana neman a hayacinta ta zauna jikinta du yana bari ta ce" me na rasa? Me na gaza? Mutuncina, darajata zasu zube ne a kasata, me ya sa kake son sai ka zubar da dukan wani tinkaho namu a duniya? Mahaifiyata ka ja gaban yiwa kishiya, yanzu zaka kara yi min du a cikin shekara daya? Kishiyarma ba daya ba har biyu? Ba zan iya lamunce raba mulkin garin nan da wata ba, ba zan iya lamunce tunaninka da wata ba
Sai kawai ta sauka da gudu ta fita ta yi bangarenta tana jin kamar zata mutu dan bakin ciki
Wayarta da ta kashe ta kunna hannunta na bari ta shiga neman layin mahaifiyarta
Tana dagawa muryarta a hade ta shiga koro mata bayani
Mikewa tsaye mamanta ta yi daga zaunen da take har tana gannin wata innuwa innuwa na son rufe idannuwanta
Me ya shirya yiwa rayuwarta ne da ta y'ayanta? Tana nan tana fadi tashin yanda zata kawar da maganar auren danta daya kwal namiji da wannan bakar yarinyar, da kuma yanda zata yi da yarinyar da rabinta da ta ganta tun shara'ar da aka yi masu da Yarima domin ganninta ya zama aiki a gidan baki daya, sam bata zuwa gaisheta bake ta samu ta wannan hanyar ta gama da ita shine zancen za'a yiwa Zinaria kishiyoyi har biyu ya fado?
Kashe wayar ta yi ta nufi dakinta da wani irin sauri a bayane ta furta" *ka ci nasara a mu ta hanyar shigar da wasu cikinmu, sai dai baka isa ka sako mana wasun ba ta bangarenka, ko wadinnan din zan fitar da su ne ko ta wani hali!..............
Ta wuni cikin tashin hankalin da ko abinci bata ci,
Yayarta ce ta zo ta tare a wajenta suka shige daka sunna tsare tsaren yanda zasu fitowa lamarin
...........................................
Bayan salar Isha yana zaune da jarida a hannunsa Amintacensa ya shigo masa da wata ambulope
Dukawa ya yi ya bashi sannan ya fita daga dakin ya koma wajen da ya rasa me suke yiwa yarinyar nan a ciki, hasalima bai san wajen na meye ba bayan kuma a cikin gidan yake ba wanda zai ce ga abinda ake yi a wajen
Sai da ya gama komai sannan ya buda ambulope din nan mai girma
Hotunna ne birjik, hade da takardar haihuwa, da adress complet
Hoton yarinyar ya kurawa ido, masha Allah Nadia akoy cikar mama sosai domin ko a hoton ana ganewa
Ajiye hoton ya yi gefe ya dauki takardar da aka yi bayani a ciki
Tabas kawarta ce, kawarta kuma ta yarinta domin tun makarantar secondary suke tare
Murmushi ya yi ya ninke komai ya mayar kafin ya dauki wayarsa
Mesage din da ta bara masa sun fi karfin irgensa dan haka ya goge su baki daya kafin ya yi shiru da wayar a hannunsa
Irin yanda take zumudi da kayan da aka kai na aurenta du ta yada maganar duniya wanda sam bai so haka ba, sosai an dauka cewar itane matar da zai aura uwa uba irin yanda take neman aminiyarta ido rufe dan ta shaida mata wannan dadadan labarin sai dai kash ta rana ina *NAJEEBA* ta shiga
Sai da dare ya raba sosai sannan amintace ya yi satar hanya ya fice
Bai zame ko'ina ba sai fadar da HUZAIFA ke zama
Yana zuwa ya yi masu salama kafin ya nemi ganninsa
Mikewa ya yi suka yi nesa da mutane sosai
Wata yar karamar wuka ya shafa masa a gefen cikinsa cikin kakausar murya ya ce" ina wayarta? Wayar zata bani, ka kiyaye idan ka yi wani yinkuri na rantse zan huhuda hanjin cikinka na yanke harskenka har sai ka ringa rokon mutuwa ta daukeka!
Kasancewar du inda zai je da wayar yake yawo yana kirta iskanci da ita har ya yi saken da Sultan ya saka aka yi tracenshi aka san wajen zamansa da komai bisa tirsasawar Anmy ya saka a amso wayar a hannun Huzaifan
Jikinsa na bari ya ciro wayar ya bashi
Kafin ya ankara ya masa wani bugu a keyarsa hakan ya saka ya tafi kasa summe sannan shi kuwa ya juya ya hau babur din da ya yi bada sau yana tuki yana sin fahimtar abinda ke faruwa,
Kwata kwata Sultan yana nisanta kansa da shi domin shi kansa yanzu bai san shigarsa ko fitarsa ba, abinda ya sanni shine wani abin na faruwa wanda sarki yake boye masa
Bukatarsa ta gaba shine sannin meye? Sai al'amuran auren nan, sam bai san yaya za'a tafiar da komai ba! Abinda ya dace ya sani dan sannin abinda zai yi!
Yau ta kama sauran kwana daya jal daurin aure, wato gobe za'a daura auren
Cikin nutsuwa ake takawa da ita ita kanta bata san inda za'a kaita ba
A rurufe komai sannan ba waje aka nufa da ita ba ta wani lungu ake ta tafia mai nisa da ita har aka isa inda za'a kaita
Sanyin safia ne, su hudun nan ne suka sakota tsakiya hakan ya saka kanta ke kasa suke jan hannunta a cikin wata irin tafia tamkar yar yaye