← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 138

Sashe 120

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsoron hakan ya sakata idannuwanta a rufen nan muryarta a zafafe ta ce" Ni balakin nake so na tayar, ta yanda zamu rufta a ramin nan kasa ta rufe kawunnanmu kowama ya huta " ! Sai kuma ta sanyaya muryarta a hankali ta kai kanta saman kirjinsa, wanda ke rufe da riga ta ciki da malun malun sai fitar da dadadan kanshin nan yake, muryarta a sanyaye wannan karron ta ce" Kana shigo min da garaje, kana taka ni da takama, shin meye ya sa kake son nunan takama ne bayan ni ban san wani sarki ba a miji? SHAHEED na san cewa kake bani da kunya, na cika tsauri, bana so ka daina tunanin hakan domin bana tunanin zan kasance mai yi maka kirari" a sanyaye ta idasa tana mai dora dayan hannun nata a saman kirjinsa wanda hakan ya saka shi lumahe idannuwansa yana jin kalamanta,

Wani irin yannayi yake jin kansa, tun daga kan kwakwaluwarsa har zuwa zuwa cen kasan zuciyarsa, lamarin mai girma ne mai tafe da abin kunce balakin da yake mata ikirarin ta barshi ya yi baci, wannan lamari ya kire ahi balaki ne tun daga ranar da ya samu fasarar abinda ke damunsa game da wannan yarinya mai halayen yan nanaye, sai ya dauki lamarin nan ya yi wani irin katon akwati mai matsatsen ciki ya saka shi, ya saka katon makuli ya rufe shi, ya yi ta kara jibga masa jibga jibgan laifukanta ta yada zai kara matsanancin nauyin da babu mahalukin da zai iya tashinsa harma ya bude shi ua falasa sirrin da ya boye a cikinsa

Sai dai kash, gashi nan rana tsaka, a irin lokacin da bai shirya ba bayannuwarwa a rufe ruf ya watsar da kaso saba'in a kan dari na laifukanta, hakan ya sa du wani kusanci nasu ke girgiza laifukan nan harma ya fara jin barazanar dake son mayar da shi wani dan yaro,

Lebensa na kasa ya dan cije a hankali yana jin yanda take sauke ajiyar zuciya, a hankali ya dan lumshe idannuwansa da sukai masa ja, ya kara bata kyakyawar rungumar da ta sakata yin lamo a jikinsa

Bai ce da ita komai ba, sai mikewa da ya yi da ita a jikinsa
Idannuwansa ya sauka a kan iyayen mazaunanta, masu wani irin tudu da fadi hakan ya saka shi lumshe idannuwansa a hankali ya kara riketa a jikinsa ya shiga dan tafia da ita ba tare da ya dauketa ko ya takura tafiar tasu ba

Batai masa musu ba, haka kawai ta kasa yi masa musu din, ta yarda da binsa cikin zuciya daya har suka shige hanyar da zata sada su da bangarensa

Bai zame ko'ina da ita ba sai saman kujera mai zaman mutun daya
Shi ya fara zama kafin ya dorata saman cinyarsa ya kuma likata da kirjinsa ya mayar mata da kanta irin yanda ta yi da farko ba tare da ko ya cire malun malun din jikinsa ba

A hankali ya ringa shafa ualwatacem gashin kanta, muryarsa ciki ciki ya ce" Yaya kike tunanin zan yi wasa wajen kawowa rayuwarki cafka?, ido rufe abokiya nake nema, koda kuwa zamu ringa fada ne, wace zata dube ni ta ce da ni SHAHEED nake marari, rashin kunyar NAJEEBA sai ta ringa sakani...........,
Sai kuma ya yi shiru na dan lokaci wanda har shirun nasa ya sakata dan fara budaumsasun idannuwanta tana dan son dago da fuskarta dan ta kale shi, sai dai bai bata damar hakan ba ta hanyar mayar da kan nata a hankali ya ce" Ki yi komai ba komai yarinya "

Dan murmushi ne ya subuce mata wanda daga cen kasan zuciyarta ne ya fito, harma aka ji dan sautinsa

A hankali ta ce" zaka sakar min abokina? Bashi da wani laifi a fadan da aka yi ka sake shi, domin shi ke ciyar da mahaifiyarsa "

Shiru ne ya biyo baya na lokacin mai dan tsayi harma ta cire rai da zata ji amsarsa sai ji ta yi ya ce" na tura shi daukan soja, idan ya fito sai na aura masa mata hudu, kin san ina son mutun mai son farantawa iyalina rai "

Baki ta saki dan mamaki harma ta dago baki dayanta, irin yanda yake binta fa kallon kasa kasa ya sakata turo bakinta a fili ta ce" yanzu dan daudun ne ka kai daukan soja?"

Bai bata amsa ba, a yanda yake kawai yake bin du wani motsinta da kallo har ta idasa mikewa gaba dayanta ta kara turo bakinta sosai a fili ta ce" Ba dai rigima kake so da ni ba? Zamu yi, zan fadawa Ammina a sako min aboki haka kawai? Malan walahi ni bana son tashin hankali, bana son fada da maza haba, ni kaucewa mutun nake aman ana bi na, garinka a dake yake a tankade daga kai har Nadiar , hasalima ba zan iya zama da mijin kawata ba! "

Murmushi yake ta dokawa a kasan zuciyarsa, a hankali ya dan muzguta dan yana son cire babar rigar nan ya samu damar kallon drama girl din nan tasa hankali kwonce, sai dai hakan ya tsoratar da Najeeba a tunaninta mikewa ne zai yi a kanya sai kawai ta juya ta fala da gudun balaki ta shige dakinsa tana kokarin danno kofa

Yar daria ce ta subuce masa ya raba bayanta da kallo har ta shige tana son rufewar, kansa ya ci gaba da dan jujuyawa a hankali a kasan zuciyarsa kuwa fadi yake 'yarinyar ba dai kujera ba, ka ga sun hanna mata gudu yanda ya dace sai kwana take abinta yar rigimamiyar'

Yana kokarin tashi ne wayarsa ta kuma daukan tsuwa

Sai da ya cire rigar ya ajiye ya koma ya gyara zamansa a hankali ya ce" NAJEEBA, ki fito ki ciyar da ni na shigo da yinwa "

Bakinta ta turo daga wajen da take, tana ta ayanna yanzu tsakani da Allah magana ne ya mata a hankalin nan kamar zata ciro daga bakinsa? To ita ta yayama yake so ta fito ta bashi wani abinci bayan yanzu ta gama zanenta hankali kwonce? Sai kawai ta yi mukus tana sauraron irin yanda ya amsa salama cikin nutsuwa kafin ya dan saurara

Cen ya mike tsaye domin baya so ko da wasa su ji wani damuwa tsakanin junnansu, dan kawai yana gudun lamari na kishin mata ne

A hankali ya ce" Allah ya ja da kwana, haka ne, kwarai laifin Zinaria ya kai wajen da ta ja har na bata saki "

Ajiyar zuciya da wani huci mai dan zafi na takaicin gurbataciyar tarbiyar da y'ayan nasa mata suka samu daga wajen mahaifiyarsu,
Muryarsa a dake ya ce" Gimbiya ki daina min ihu a kaina, idan ba haka ba zan dauki mumunan mataki a kan ki! "

Shiru SHAHEED ya yi, domin ya fahimci muryar kukan da magana sama sama da yake ji na mahaifiyar Zinaria ne

Sarkin Agadez ya ce" Alhamdulilah, Allah ya sa hakan ya zame mata izna da ita da dukan wani mai halayanta ko wanda halayenta ke baiwa sha'awa,
Dan saurarawa ya yo kafin ya dan kara karya muryarsa ya ce" ina rokom Alfarmar a sasauta fushin, idan har da hali ta koma dakinta koda nan da shekaru ne "

Sai da SHAHEED ya dan saki dan murmushi a hankali ya ce" in sha Allah, burina ta gane rayuwa, ta gane abubuwa kamar haka : Dan adam ba abin wulakantawa bane komai rashin arzikinsa ko mumunan kamaninsa, ina so ta bambance mahinmancin zaman aure da zama domin ta birge kawayenta, ina so ta koyi sannin cewa mulki ko sarauta kafin ta hau dubanta sula hau, kuma suka sauka suka bari, a yanzu a matsayinta na yar sarki matar sarki tana iya amsa kiran mai duka, za'a kaita ne daga ita sai farin likafani sai hali sai sallah, ta gane ita ba kowa bace ko a wajen Allah daga bakin sa'in da ta dage kai da fata ita ba zata bi dokokin Allah ba, ina so ZINARIA TA SAN RAYUWA : , ya dan nisa ya dora da fadin " hakan ne ya saka ni mikata ga gidan horo na ahalin cikin gida "

Murmushi ya saki mai sanyi , kafin ya furta" Dama na san kai din adali ne, mai nazari ne, mai sowa dan uwansa abinda yake soea kansa, tabas na yi imani da cewa da ba dan ta samu gurbataciyar tarbiya ba da ta jima da fahimtar cewa adali, zababe, managarci ne Allah ya wanke ya bata, da ta jima da fahimta ta karba harma ta koyar da wata waye mijin da take aure, sai dai kash, sannan a gaskiya ka yi hakuri SULTAN SHAHEED, gidan horon Damagaran yar karamar aljannar duniyar mabukaci ne, ba zata taba shan wahala ba domin kuwa abubuwan da ta rasa kadan ne a ciki, zata dan hakura ne har a fitar da ita ta ci gaba da daukan banzayen hudubobi, ama idan har ta samu kyakyawan horo, zata je ta hada labari ne harma ta kwabi bakin du wani mai sakata aikata mugun abin, dan haka daga bakin lokacin da za'a samu sakamakon bincike cewar ba hannunta a rasuwar marigayiya da kuma kokarin son kashe yar uwarta za'a miko mana ita ne sai mu bata horon da ya dace ga marar kunya! "

Wani murmushin SHAHEED ya yi, kafin ya shiga mika godiyarsa cikin jin kunyar sakar masa y'a da ya yi aman kuma shine har ya fahimce shi haka

SARKI na ajiye kan wayarsa ya maida dubansa wajen mahaifiyar Zinaria dake ta rufe bakinta dan kar ta saki kuka tun karfinta domin kuwa bata so ko da wasa kishiyoyinta su yi gaba da ita

Kai ya girgiza a kausashe ya ce" wato bawa ba zai taba yin asara irin ta yayi asarar uwar y'ayansa managarciya, tabas asarar kudi ko wata kadara ba zata taba kamo asarar rasa mata ta gari ba "
Chapter 120 · 0% Book details