← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 138

Sashe 46

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ihun da take kwalawa ya saka a tare suka nufi hanyar, sai dai irin tsawar da ya daka masu na cewar su yi baya ya saka su saurin yin bayan aman kamar zasu summe su biyu sai kama sunnanta suke sunna ihun meye??

Wayo na shiga uku, wayo na mutu na lalace, tana ihun ne tana jan numfashinta dake sama sosai

Yana shigowa ya hangeta tana daka tsalen albarka baki daya jikinta na tafia da ita hannayenta saman kanta kafin ta duke tana kallon wajen da ya yi gagawar zarewa ba tare da ko ya samu ya kawo ba aman mai afkuwar ta gama afkuwa domin dai a yau ya mayar da UMMU cikakiyar mace ta hanyar ratsata da gararia first night din yayarta ita ta kawo budurci

Da sauri ya karasa ya saka hannunsa ya dagota, muryarsa a cinkushe ya buda bakinsa zai tambayeta uban me take ma ihu
Sai dai bakinsa ya yi dif a lokacin da ta kamo hannunsa ta dora saman kirjinta gefen zuciyarta ta hagu wanda ya yi daidai da saman mamanta das ta dora da karfi ta damki wajen tana ihun fadin" zata fashe wayo zuciyata zata fashe, wayo ya kashe mu, ya kashe mu, wayo yayata ya wulakantata ya halakata
Sai kuma ta idasa zubewa dif ta gama sumewa

Inda ya ji alamun motsi ya kai dubansa

Da sauri ya rintse idannuwansa da wata irin faduwar gaba mai balakin karfi ga kuma NAJEEBA a jikinsa ta sume inda ya talabeta baki dayanta a hannunsa daya, idannuwansa kuwa tun da ya ga abinda ya gani ya rintse da karfi yana fatan Allah ya sa ba abinda yake ganni bane wato Yarima tsugune gaban UMMU zigidir baki daya jikinsa na rawa harta da hannayensa da dukan gabai nasa da irin kalaman da yake fadi yana talabota da hannayensa yana fadin"

Barka da safiya🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

26

"Innalilahi wa'ina ilaihi raj-une! Wacece wannan? Daga ina ta fito? Na halaka kaina na halaka yar mutane, wayo Allahna na kashe rayuwar yar mutane na kashe kaina, wayo na shiga ukuna yau na tafka kuskure mafi muni a rayuwana, wayo ni ba mazinaci bane zanen k'addarata ne, wayo matata ce ta janyo min ta hana min kanta bayan ina da ita, na shiga uku na lalace."

Hannunsa na dama ya saka ya tare hanyar da Ummulkhair ke son lekowa sakamakon kalamansa da suke daukaka girman fitowar furucinsa

Wani ihun ta saka itama hakan ya saka shi daukan NAJEEBA dauka irin na jarirai ya fito

Hannunta ya damka kafin da idannuwansa ya yiwa ZAHRA nuni da ta biyo bayansa

Gaba daya bari jikinta yake
Dukan gabanta kamar ba nata ba haka ta ringa hada hanya ita tama rasa me take ciki har suka idasa shigowa falonta ya shinfide NAJEEBA nan kasa saman cafet sanan ya yi masu nuni da su zauna

Juyawa ya yi da sauri ya koma, lokaci daya mazan dogaran sun fara farga har an fara nufi wajen sannan tuni an kaiwa sarki kabarin ana jin murya na kuka sama sama kamar ta yarima da kuma wata mace hakan ua saka shi fitowa da saurin gaske bayan ya warto sharbebiyar wukarsa ta yaki mai sunna Babarbara

Yana komawa ya saka hannunsa ya karbeta a hannunsa, kafin yake rufa mata mayafin da ya shigo da shi a wajen sirrinta

Haske ya kunna hakan ya saka Yarima saurin wartar wandonsa jikinsa na bari ya shiga kokarin sakawa

Wajen wuyanta ya shiga dora hannunsa, lokaci daya yana waigen bayan da yake sama ne suke yana hangen yanda gidan ke ta kai kawon dogarai wasu na tambayar daga inda ihun yake sai kokarin karasowa suke

Matan sarki ne suka fito a firfirgice du sunna kokarin yin inda ake fadin ihu na fitowa

Giftawarsa da dogarai majiya karfi sai kirarin yaki suke a bayansa ya saka jikin matan nasa kwasar rawa

Da sauri suka bi bayansa kowace da irin abinda take sakawa a kasan zuciyarta, fatan Gimbiya ta tarar da amarya ce ta mace!

Dakatawa ya yi duba da falon amaryarsa ne za'a shiga ya tsayar da baki daya dogaran waje daya sannan ya shige da saurin tsiya

Saurin kawar da kansa ya yi daga kansu gannin du jikinsu da shigar baci ne sannan sun zagaye yar uwarsu

Wajen da yake jin muryar yarima baban dansa ya nufa da sauri babarbararsa a hannunsa

Yana hankada kofar wajen ya shige da sauri yana tambayar abinda ke faruwa da yaren buzanci

Abubuwan da yarima ke kara maimaitawa da irin yanda SHAHEED ya gyara mata kwonciya tamkar mataciya ya saka sarki zaro idannuwansa baki daya jikinsa ya kama bari

Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une

Da wani irin bacin rai ya nufe shi da wukar nan yana dagawa a fili ya furta" tirr da kai FARID, gwara na kasheka da hannuna na huta

Da sauri ya yi wata irin dira ya tari gaban mai martaba kafin yake saka hannunsa ya tare wukar nan da hannu daya ya janyeta daga hannunsa ya riketa taf a hannun nasa

Ihun kukan da ta saka tana dora hannayenta duka biyu a saman kanta ne ya ankarar da fitowarta hakama mahaifiyarsa gaba daya jikinta ya dauki wani irin bari itama ta dora hannayenta saman kanta tana jin abinda ke shirin riskarta duka a zuwa bakaken halitar nan! A yau ta ga balakin da ko mutuwar ubanta bai girgiza mata kwakwaluwa irinsa ba
Tashin hankali ya risketa na mamaki kafin ta gama fahimtar wani ko baci ya ki daukanta ga wani ya sameta yau itace tsaye a gaban tarin abin kunyar nan
Sai kawai ta dafe kirjinta ta silale kasa

Muryarsa a dake ya furta" idan har magana ta daukaka ta fita tsakar gida ba abinda zan iya yi maku baki daya! Ku sanni sirrin masu mulki, da manyan malamai ya fi tarwatsa al'umah, ya fi lalata tarbiya! Ku sani idan har waje ta dauka haka ya faru da yariman garin agadez to kuwa matasan garin agadez zasu dauka su mayar da hakan abin yi! Ana iya tankwasa rigima idan bata yi yawa ba!

Yana gama fada karasawa ya yi ya sungumeta ya fito da ita

Dakin Zahrau ya nufa da ita kafin ya kuma fitowa ya sungumi NAJEEBA itama ya nufi dakin da ita sannan ya yiwa sauran alamun su biyo shi

Saman bed du ya jera su kafin ya yi tsaye ya kura masu ido
Ta ina zai fara? Me zai ce? Tabas sun shiga rudani mai girman gaske, shi kansa ji yake kamar zuciyarsa zata samu matsala a irin lamari

An dauki kamar mintunna ashirin sai ga bugawar kofar, du a zaune suke sunna ta kuka su biyun, Ummu ta dawo hayacinta aman bata iya komai waje daya kawai take kallo sai hawayen dake bin gefen kumatunta
Shi kuwa yana tsaye ya kura ma waje daya ido

Karasawa ya yi ya bude kofar

Likita ce ta shigo Sarki kuwa na tsaye daga baki baki bai shiga ba domin ya san ko a yanzu basu saka kaya ba, irin yanda yake zufa sai abin ya baka tausayi ya koma ya jingina da kofar yana kallon yanda iyalansa suka rikice

NAJEEBA dake sume ta fara baiwa taimakon gagawa
Ai kuwa ta farka a rikice tana ta waige waige, sai ta kwala ihu mai karfin gaske ta fashe da matsanancin kukan da ya saka yan uwanta suma fashewa da wani irin kuka mai cin zuciya da zafin gaske sunna ririke junna

Karasowa ya yi ya saka hannunsa ya bambare hannun Zahrau daga jikin Najeeba kafin ya kuma saka hannunsa ya k'ara cicib'arta.

Bai zame ko ina da ita ba sai cikin bayi direct ya idasa wajen bath da ita.

Zaunar da ita yayi sai ihun take tana kuka kamar ranta zai fita ga gazar gazar din gashin idannuwan nan nata sai kara far suke.

Bata tsamaci jin ruwa ba sai saukarsa ta ji a kanta hakan ya saka gashin kanta gaba dayansa ya yi lingib a bayanta da wani karfi ta so zabura ta tashi sai dai ya saka hannunsa ya maida ita cikin ruwa ya zaunar da ita sannan ya riketa tam a ciki.

Tun tana gunjin kukan har ya zama ta ringa rage sautinsa tana yi sannu sannu har ya dawo na zuci ne take yi sai hucin da take furzarwa.

A hankali ta langab'e a saman damtsen hannunsa shima ruwan ya jik'a masa jalabiyar jikinsa
cikin wata shak'ak'iyar murya dake cen ciki ta furta" Ya halakamu, ya wulak'antamu, ya goga mana penti, me mukai masa? Ya ketawa yar uwata hadi."

Gani yake ta d'aukaka firgicinta, gani yake ta zurfafa firgicinta bayan ba haka ya dace ta nuna ba duba da ita din aikinta kennan, harkar maza ya zame mata abinda ta fi k'warewa a kai, akan me zata ringa irin wannan abu? Sai yake tunanin tana pretending ne, sai yake gannin kamar so take ta raina masa hankali
Jin rawaninsa na son jik'ewa ya saka ya ringa janye jikinsa a nata
Idannuwansa ya sauke a kanta da niyyar yi mata magana sai dai da kansa ya kawar da kansa da wani irin sauri yana mai rintse idannuwansa domin ruwan nan da ya jik'a mata jiki da shi baki daya ya lafe mata da rigar nan mai santsi a jikinta a yanzu ne hallitar k'irjinta ta wani irin bayanuwar da ta saka shi ji gaba d'aya jikinsa ya d'auki rawa.

*(mai damagaram yana ruwa, kusa da kada inji breaker🤣)*

Mik'ewa yayi da sauri ya juya ya fita a bayin.

Yana fitowa ya tarar da su sun saka suturun da suka rufe masu suturarsu, sannan sunna zazaune gefen kanta likitar kuwa ta bata maganin da zata sha dan rage rad'ad'in dake damunta na bak'on lamarin daya ziyarceta bayanshi bata samu wani mugun raunin da zai saka a kaita asibiti ko a mata d'inki ba, tana shiga ruwan zafi komai zai dawo normal sai dai abinda aka yaye din da ba za'a iya maido shi ba.

Tawul ya d'auko ya mik'awa Ummu ya nuna mata bayi hakan ya ganar da ita abinda yake nufi.

Wasu kayan ta d'aukar mata ta nufi bayin da su.
Chapter 46 · 0% Book details