← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 138

Sashe 75

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsarin falon nan ya sakata yin saranda cewar lalle sarkin Damagaram ba karamin mutun bane

Sanyin Ac din ya sakata yin lakwas tana sauraron yanda cikinta ya dan fara neman agaji domin a gaskiya yinwa take ji rabinta da abincin kirki har ta manta, sai kima mata abubuwa suke,

Dubanta ta maido wajen Jakadiya

Kanta a kasa tun gurfanar da ta yi,
Hakan ya bata mamaki tana dubanta ta ce" aman mama ki daga ki huta mana

Da sauri Jakadiya ta kara sada kanta ta shiga Fadin" ALLAH ya taimakeki ai ban gaji ba, Allah ya kara maki lafiya Gimbiyar Gimbiyoyi, sannunki da zama uwar gidan Mai damagaram

Murmushi Najeeba ta yi tana kara kallonta ta ce" to tashi ko tafi idan ya zo zan ce da shi kina gaishe shi

Jakadiya kam abin ya gama kasheta da mamaki, kai? Tana gaishe shi? Ita wa?

Kara sada kanta ta yi ta ringa neman afuwa da fadin ba sai an ce tana gaishe shi

Wannan lamari ya baiwa Najeeba Nishadi har kara kallonta take tana so lale lale sai ta dago kanta kamar wara wace take gaban sirikinta?

Ita dai Jakadiya cike take da tsoro da al'ajabin Najeebar, so take ta bata damar da zata kara gurfanawa aman Najeebar ta hanna

Najeeba ta kara sakin murmushi ta ce" ki tashi ko ki bata min rai fa? Na salame ki

Ai kuwa da sauri ta kara gurfanawa tana Allah ya huci zuciyarta, kafin ta mike ta yo waje da sauri

Najeeba ta zaro idannuwanta a fili ta furta" kai? To meye dan kin bata min ran? Lalle gifan sarauta na tare da wani lamari mai girma

Komawa ta yi ta kara zaunawa da kyau ta shiga tunanin rayuwa
Saloon dinta, yaya yake tafia?
Kudadenta ina aka kilace mata?
Kayan aikinta shin ana kular mata da su?
Domin fa, zata koma bakin aikinta, zata nemi kudinta kamar yanda ta fara, auren sarki ba zai hannata nema ba!

Kamar wasa zama ya sameta
Tun tana daga kanta tana kallon agogo har karfe dayan dare ya yi bata ga alamun kowa ba, bata ji motsin kowa ba

A hankali ta cire kafafuwanta daga cikin lalausan takalmin da aka saka mata na baci ta dora kafafuwan nata saman kujerar nan ta juya ta yi kwonce ta mike kafafuwan nata sannan ta sauke alkuabar daga jikinta baki daya dan ta ji dadin baci

A kasan ranta ta furta" ai da gannin jajayan idannuwan nan nasa na mashaya ne, mai yiwuwa an labe wani wajen ana aiki marar kyau
Kafadunta ta daga tana ayanna ta fi nono fari, sannan ita kuwa da ta mareni sai na fadawa Abih!

A hankali ta lumshe idannuwanta tana mai neman baci, baci take so ta yi ta huta, ta ajiye matsalolinta gefe zata waiwayesu ne daya bayan daya domin a yanda ta fahimci rayuwa zuwa yanzu idan ba ita da kanta zata daukarwa kanta mataki ba, to fa bata da wanda zata fadawa ya shige mata gaba

A hankali ta ringa lumshe idannuwanta tun tana cike da tunanin duniya da matsalolinta har ta fara gyangyadi

Cen cikin gyangyadinta ta ji wani ihu daya tak wanda ya sakata zabura a firgice har tana gurdewa ta fado daga saman kujerar da take kwonce
A tsorace ta kai dubanta wajen agogon dakin mai dauke da gilass

Karfe uku har da minti arba'in da bakwai, wato hudu dai ta kusa

A tsorace ta kara saurarawa dan jin shin ihun ta ji ko kuwa mafarki take cike da mamakin har ta yi bacin awa kusan uku?

Murya ce ta shiga kunnenta a galabaice ana furta" *wayo Allahna zan mutu, wayo na tuba ka sarara min haka, wayo dan Allah kar ka kara turawa zafi nake ji kar ka yaga ni biyu, innalilahi wa'ina ilaihi raj'une wahala*

A hankali ta kifta idannuwanta sukai mata dan luuuuuu sannan ta kuma budawa

Irin kalaman da kunnayenta suka kuma tsinto mata sune kamar haka" *ta fi karfina, wayo zan mutu wayo ni Allahna ka taimakeni Sarki*

Wani irin ras, hade da kamewar bayan kai ne ya sameta lokaci daya,
Mikewa ta yi tsaye ta juya wajen da ta fi jin magangannun na fitowa

Muryar kawarta ce, aminiyarta ce, wace take tamkar yar uwarta ce ke fitowa daga cikin dakin cen wanda ya fi kowane nuni da shine dakinsa
Irin magangannun dake fitowa ko mahaukaciya ce ita sun kai su nuna mata ga abinda ake nufi da su, aman sai zuciyarta ke karyatawa take ce mata" ke kuwa, yau din ai ranarki ne

Wata zuciyar ta furta" ranata kuma?

Wata ta bata amsa da cewar" kwarai , ai a gaban kowa aka tsayar da hakan, sannan har aka kawo ki dan karbar ranar taki

To ko dai an cenza ne basu sani ba suka kawo ni?
Kai ina, wani cenji?
Irin kalaman dake kara fitowa suka saka a hankali ta ringa jin hannayenta na yi mata rawa, gaban jikinta na kwasan rawar hakama zuciyarta na yi mata barazana da tarwatsewa

*WULAKANCI NE, HAKA GIDAN SARAUTA YAKE NE, KO KUWA IYAKANTARWA CE?*

a hankali tun tana jin kukan sama sama har ya ringa ragewa

Sam ko sannin cewa a tsaye take ko a zaune bata yi ba, abinda ta sani ita dai kunnayenta na jiyo mata abubuwan da zuciyarta ke bata fasara nan take

An kuma daukan wani lokacin a haka har ta daina jiyo kukan Nadia, da magiyarta

Tana nan tsaye har kunnayenta suka fara jiyo kiraye kirayen sallar farko

Kafafuwanta sam bata jin su a jikinta, abinda ta fi ji a yanzun shine irin yanda zuciyarta ta cinkushe da baki sannan idannuwanta suka rufe da zubar da hawayen da bata san sunna fitowa daga gurbin idannuwanta ba

Kofar take kallo
A lokacin da aka shiga dan kusur kusur din son bude kofar

Kara tsurawa kofar ido ta yi tana kallo har aka gama budewa

Bayan budewarma an dan dauki yan mintuna kafin fuskar ta fara bayannuwa a idannuwanta

Fuskar nan mai haske, mai walwali, mai dauke da kyakyawan saje, mai yalwatacen gashin gida da ido, mai dan fadi , mai dauke da dogon hanci mai dogon karan hanci, mai dauke da idannuwa masu zanen Kwalin Allah ne ta bayana a gabanta

A yanzun, tana tunanin cikin biyu daya, ko ta samu matsalar gani har amininta ya fara yi mata gizo a gidan aurenta, ko kuwa ta haukace, ko kuwa ta samu shanyewar barin jiki

Tun tana hangensa daga nesa, har kusancinsu ya kara tsananta har ya kasance ya bayana gashi gata face to face sunna kallon junnansu a daidai lokacin da ta tabata shi ne a gabanta a tsaye

Lebunnanta ne suka kwashi rawar da hannayenta ke yi a lokaci daya ta dago da yar yatsarta ta yi nuni a kansa

Ta jima tana barin lebe kafin da kyar ta samu kalaman su fito daga bakinta ta ce" *KAI? ME KAKE A GIDAN NAN? WA KE KUKA?*

fuskarta yake kallo tsai har cikin kyawawan idannuwanta masu dauke da eye ball masu shegen kyau da gashin idonta natural domin an cire mata karin sai nata da suke cike da baki sidik, sai lebunnanta dake rawa rawa tamkar ba nata ba da kalaman da suka fito daga bakinta

A zabure kamar an tunzurata ta daga kafarta da ta mata nauyi sannan ta dauki mujirya ta damko hannunsa na dama wanda hakan ya saka shi sada dubansa wajen da ta riko hannun nasa da nata hannun ta dago sosai tana kallonsa

Muryarta a yanzu ta hadu da kamar zata fashe da kuka ta ce" dan Allah, ka taimaka kar zuciyata ta tsaya, ka fada min abinda ya kawoka gidan nan, har dakin nan, har cikin dakin cen, sannan nake jin muryar aminiyata a ciki? *Kai din wanene?*

Da hannayenta bibiyu ne ta rike masa hannunsa guda, tuni jikinta ya dauki wani zafi na firgici da tashin hankali

Idannuwansa ya lumshe kafin ya vude yana kuma kallonta
Wannan karon a hankali ya ringa cenza kallon da idannuwansa ke mata masu laushi zuwa wanda ya saba yi mata

Kasancewar fuskar tasa take kallo, sannan cikin idannuwan nasa, a lokacin da idannuwansa suka rikide zuwa wanda ya jima yana binta da shi, wato kallon tsanar nan sai kawai mai rawani ya fado tar tar a kan hakan

A yanzun kam ba kanta aka soka ba, aa, guduma ce aka duma mata baki dayanta wanda hakan ya sakata yin luuuuuuu tana daukewa kamar injin da ya mutu a mota ana faman sai ya tashi

Tareta ya yi baki dayanta ta fada jikinsa, kamshin turaranta, santsin fatar jikinta da rigar nan wace ta yaye domin dama mai tsaga ce ta yi gefe da irin yanda gashin kanta ya yi luf luf a kan fatarta mai masifar kyau da tsari suka sauka baki daya a jikinsa a lokacin da bai shirya ba

A hankali ya yi kasa da ita saman tiles din dakin ya kasance tana saman hannunsa na dama, hannunsa na hagu kuwa ya kara talabeta da shi

Wani gurnanin kuka ta dan saki kafin ta furzar da iska tsai kuma idannuwansa take kallo

A hankali ta dago hannunta na dama baki daya jikinta na rawa ta kai kusa da fuskarsa

A hankali ta shafa fuskar dan kara tabatarwa idan wai shi din ne? Kafin ta saki wani dan marayan kuka tana jan numfashinta

Baki daya abubuwan da suka ringa faruwa tsakaninsu daki daki suka ringa fadowa cikin zuciyarta

A hankali ta kara shafa fuskarsa wace tuni idannuwansu sun yi ja haka kuma saman goshinsa ya fitar da wata jijiya wace bata san ko ta meye ba

Muryarta a cen ciki, idannuwanta na daukewa , zuciyarta na son yin karfin hali aman ta kasa ta kara damkar hannunsa a hankaki ta furta" *NA TSANE KA*!

Ban yaba jin tsanar mutun irin...........sai kawai hannun nata ya saki luuuuu ta dauke wuta

Fuskarta yake kall9 da wani irin kallo mai cike da son gane wani abu
Kamar wanda yake so ido rufe sai ya ga shinfidar fuskarta ya ga abinda aka hada aka yi fuskar tata
Chapter 75 · 0% Book details