← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 138

Sashe 133

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idannuwanta ta lumshe, so take ita a yi kawai, haka take ji a kasan ranta wanda bata san dalilin da take son ya haukata mata jiki ba,
Muryarta a sanyaye ta ce" haka yake min kusan sati biyar yanzun "

Idannuwansa dake lumshe yana jin yanda ta saka yar yatsarta a bakinta, dumin bakin nata da irin yanda ta shiga tsotsa a hankali a hankali nan da nan jikinsa ya dauki rawa, da sauri ya buda idannuwansa sukai ido hudu da junna, irin yanda ta yi kalar jariri sai ya ji kamar zai summe daga zaunen nan da yake

Da karfi ya sauke nanauyar ajiyar zuciya kafin ya birkitata baki dayanta ya yi mata runfa

Da wani irin sauri yake gurzarta idannuwansa lumshe, idan ya birkitota nan sai ya birkitata cen, jikinsa na wani irin rawa rawa kamar zai hadiyeta ya maidata ita cikin cikinsa ya huta

Hannayensa yake cikawa da mazaunanta sai kawai ya dan saki murmushi a fili ya furta" MASHA ALLAH "

Sai da komai ya kankama ya ji shi tsamtsamtsam ga abu na bin lamarinsa, sai kawai ya rukunkumeta a jikinsa yana fitar da wani irin numfashi muryarsa a ciki ya furta" Da wani ya shigar min da ya halaka min farin cikina har duniya ta tashi, ban taba jin kishin abu, da Kaunar abu, da son kilace abu irin yanda nake jin naki ba NAJEEBA, NAJEEBA ina son ki, ina son ina son ki, ina son ki so na gaskiya da babu yaudara a cikinsa, ki min rai, ki agaza min, ki dube ni"

Hawaye ne masu sanyi da wani irin tsuma ke ratsa fuskarta, fuskarsa da ta yi ja ta kurawa ido, a hankali ta kai hannunta ta shiga goge masa yan guntayen hawayen dake zirarowa ta kurmin idannuwansa
Idannuwansa cikin nata yake furta" ki furtan kalmar so ko zan ji sauki a zuciyata "

Zuciyarta ce ta kara bugawa, ta yarda cewar shi din Namiji ne cikake mai iya motsa zuciyar du wata halita, yannayin sarautarsa na kara masa wani irin girma da kwarjini a idannuwanta, yannayin shigarsa na haukata lamuranta, takan nacewa son kallon shigarsa, takan nacewa kanshin jikinsa harma ta taba gigin siyan irin turaransa ta karar da dan tanadinta, shi din mai tsada ne, komansa mai tsada ne, jajircewarsa, da irin tsayuwa kan kafafuwansa na sakata jinsa a cen kasan zuciyarta, sai dai ba zata furta ba, ba zata iya furtawa a yanzu kai tsaye ba, dole zata ja zarenta na mata wanda zai bashi bambancinta da watarta, dole zata kara tsayawa ya furta idan yana cikin hayacinsa kafin ta idasa aminta da magangannunsa ko ba komai namiji yake ehe

Sun raya daren nan kamar ba gobe, hakan ya sa nanauyan baci yin awan gaba da ita

Cen cikin bacinta ne ta ringa jin ana shafa fuskarta
A hankali ta juya ta ci gaba da bacin tana fan yatsina fuska
Bai hakura ba ya ci gaba da shafawar a sanyaye hakan ya sakata dan buda nanauyan idannuwanta ta sauke a kan ni'imtaciyar fuskarsa

Wani irin murmushi ne a kan fuskar tasa, wanda kana ganni zaka fahimci yana cikin farin ciki

Muryarsa a sanyaye ya furta" BEEBAH, ki tashi ki yi sallah, kin ga na fita tun da duku duki an ce Nadia ba lafia ashe baki tashi ba har karfe tara? Tashi likitan ya dawo na ce ya tsaya ya baki maganin zazabin nan na dare, kuma kin san me Nadia na dauke da junna biyu ki tashi ki ji abin farin ciki"

A hankali ta idasa wara idannuwanta a saman fuskarsa, Allah yana ganni maganar junna biyun Nadia ya sakata sakin wani irin murmushin farin ciki, a hankali ta ringa jin kaunar aminiyar tata da son tayata farin ciki na bijiro mata,

Fuskarta mai dauke da murmushi ya tsurawa ido,

Hannayenta ya rike har ta idasa zama a saman bed din, kafin ta shiga mika tana lumshe idannuwanta
Da sauri ya dan kawar da dubansa dan walahi idan har zai zauna kallon mikarta yanzu zata rikita masa lisafi yana zamansa kalau

Kamata ya yi ta mike tsaye, kuma yanzun jikinta sam ba zafin ko daya, haka kuma bata kama da marar lafia

A kofar bayin ta ja ta tsaya tana dan tura shi irin kar ya biyota

Murmushi ya yi ya tsaya har ta rufe bayin sannan ya samu waje ya zauna yana jiran fitowarta

Shi kadai yake godewa Allah irin baiwar da ya yi masa, Nadia na dauke da ciki har na sati uku , ta fara rashin lafia ne sosai yau har AMMI aka fadawa shine ta kiraye shi ya yi kiran likitar dake duba matansa ta zo ta dauki jinninta da fitsarinta ta koma, har ta dawo ta kawo result shine ya dakatar da ita cewa ta baiwa Najeeba maganin zazabin dare, s nan ne AMMI ta yi nuni da kar a bata ba'ai mata gwaji ba tukuna, domin ita dai ta san abinda take ganni a jikin Najeebar gashi ba kowani magani ba mai ciki ke iya sha ba

Yana nan zaune ya jima sosai kafin take fitowa daure da tawul a kirjinta

Cikin nutsuwa take kokarin karasawa wajen kayan salarta da abin sallah

Duka yana kallonta har ta idasa sallar sannan ya kurawa fuskarta ido da ta yiwa takwaf takwaf tana karasowa inda yake zaune

Sai da ta dare kan cinyoyinsa sannan ta sarkafo hannayenta a wajen wuyansa ta shiga zuba shagwaba tana kara tabe dan bakinta ta ce" Ni kiwuyar zuwa falon AMKI nake yanzun "

Murmushi ya yi yana kallon yanda take yiwa fuskarta a hankali ya ce" Ni kuwa bana tunanin zan iya katabus jin kin jima kina kwana da zafin jiki "

Kara langewa ta yi a kirjinsa ta ki cewa komai sai dan kukan shagwaba da take tana kara shiga jikinsa

Idannuwansa ya lumshe, a yanzun ya fara tunanin yarnan zata zauta shi ne idan ya yi da wasa fa

A hankali ya mike da ita a jikinsa ya shiga takawa yana mai kara gyara rikonta a jikinsa

Idannuwanta lumshe tana shakar dadadan kanshin turaran dake fita a wuyanta har ta ji tsittt kamar hayaniya ta dauke

Da sauri ta dago dubanta, ba shiri ta dirko daga jikinsa tana zazare ido gannin yayunta da kanwarta zazsune kawunnansu a kasa, wata datijuwa a gefen AMMI itama kanta a kasa, sai AMMI da ta kawar da dubanta kamar ba abinda ta gani zuciyarta kuwa wani irin mamakin SHAHEED din ne ke neman halakata, a da takan aunawa a ranta cewa shi din bai yi halayen mahaifinsa ba na kulawa da mace, aman a yanzu sai ta karyata wancen tunanin

Cike da mamakinsa ta kale shi , bakinsa ya dan tabe ya kama hannunta ya ce" Mu je mana "

Da sauri ta juya cike da wata irin kunya ta koma hanyar da ya biyo da su, ita ta yi nisan kiwo a sinsinar wuyansa ashe har ya kawo kofar bata sani ba har ya bude ya shigo da ita a haka tana nanakarsa ita kam me zata cewa yan uwanta da ta gama kurantawa bata son sa, da wani ido zata kalli AMMI ta ganta kwonce rashe rashe a jikinsa

"BEEBAH, wai ina zaki je ne haka?" Ya fada yana saurin cin mata dan da gudu ta fala

Birki ta ja ta ci a lokacin da ta saka kanta cikin dakin ta juyo tana dago hannayenta ta ce" Fisabililahi SHAHEED ka san su AMMI na zazaune da su Aunty Ummu ka shiga da ni a nanuke da kai salon su ce da ni munafuka, AMMI kuma ta yi tunanin na zama marar kunya? "

Irin yanda take bayanin tana nunawa tana yawo ta kasa tsayawa waje daya hannayenta a sama ya bashi daria sosai, sai abinda ya kara birge shi gannin fada ake masa yau kuma, ikon Allah kala daban daban a wajen yarinyar AMMi, sai kawai ya hade bayansa da garun wajen ya harde kafarsa sannan ya dage mata girarsa ya kane mata ido daya ya ce" Zo nan "

NAJEEBA ta yi sakalo tana kallon yanda ya yi da fuskar tasa, sannan ta kai dubanta wajen da ya nuna ya kuma daure gida

A hankali ta karasa ta tsaya ta sada kanta, hakan ya kara bashi daria, wai kunya ta ji ko me? Lalema

"Mu je a duba min ke" ya fada yana kallon fuskarta

Tana murza yan hannayenta a hankali ta ce" Dama lafiata kalau nakan yi masasarar dare wani lokacin "

Kansa ya girgiza ya ce" Bana so kina rashin lafia "

Dago da dara daran idannuwanta ta yi tana kallonsa, cikin nutsuwa ta idasa jikinsa tana mai dora kanta a saman kirjinsa, muryarta ciki ciki ta ce" Ni allurar cema bana so a rayuwata, ka barni haka na tuba "

Du idan ta kusanta jikinta da nasa sai ya ji kamar zai tsere domin abin bambarakwai yake zuwar masa, bai saba ba ko kadan bai saba ba ko Nadia bata shiga jikinsa, takan sada kanta a gabansa dai sannan takan damuwa da cin sa ko shan sa, ama Najeeba ta mayar da shigewa cikin jikinsa aikin yinta

Hannun nasa na dama ya dora a bayanta, a sanyaye ya furta" Ki ce kina so na BEEBAH? "

Shiru ta yi na lokaci kankani, hakan ya sa kirjinsa ya yi ta bugawa harma yannayin ya so ya dagule masa

Yar karamar wayarsa ce ta dauki tsuwa , yana dubawa ya san AMMI ce ya daga

Bayan ta yi magana a hankali ya furta" AMMI ta tafi, bata son allura "

Ammi da ta yi zaman son gannin irin farin cikin da zai nuna itama idan aka tabatar mata irin farin cikin da zata ji sai ta yi turus da maganar da ta dauko ta ce" Shaheed, ka kawo kin ita nan, ko ta tsaya yanzu yanzu ana kawo mata abin fitsari maza ta yi a kawo min "

Bai saka komai a ransa ba sai tsayuwar da ya ci gaba da yi da ita a jikinsa har kunnayensa suka tsinkayo masa tafia kafin ya ji an tsaya

Bai bude idannuwan nasa ba ya furta" Bani "
Chapter 133 · 0% Book details