← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 138

Sashe 110

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

NAJEEBA dake tsaye sai a lokacin idannuwanta suka gane mata lale da gasken NADIA ce

Baki daya sai ta ji ta kasa iya rike kanta, a hankali ta silale daga inda take a tsayen nan ta zauna saman cafet din kamar yanda baki daya mutanen falon suke ciki kuwa harda SUKTAN da ya zauna a kasan shima dan ya dubata da kyau

Abih ne da yannayi na tashin hankali ya ce" SHAHEED mu kaita asibiti mana? Menene ya sameta? Meye wannan akai kamar an yanka ne? Me ke faruwa ne?"

Sai da SHAHEED ya dauki kamar minti uku yana mai ci gaba da dan taba yannayin jikinta da yake jin kamar yana cenzawa kamar kuma baya cenzawa sannan ya kalli ABIH, A sanyaye ya ce" wannan din shi ne treatment din da zasu yi mata ko kun je, ku mu saurara kadan, idan har da sauran numfashinta zata farka"

Ai Najeeba na jin haka sai ta fashe da wani kuka kasa kasa tana mai dora hannayenta saman kanta hankalinta tashe da jin kalaman SULTAN, me? Aida? Me ya same ta? Wani irin treatment ne wannan ya yi mata? Bakin jinnin nan na meye? Me ke faruwa ne da gidan nan da shi kansa SULTAN?

Ammi da ta fi kusa da ita ne ta kamo hannunta irin ta karaso jikinta

A hankali ta jarasa ta zauna a karkace ta dora kanta a gefen jikin Ammi, tana mai fitar da wani marayan kukan da ya saka cike da tausayawa, sannan jin irin yanda jikinta itana ya dauki zafi ta ringa dan taping din bayanta dan ta samu ta yi shiru, domin kuwa a irin yanda ya hade ran nan su kansu sun yi shirun ne sunna masu adu'ar Allah ya sa ta tashin

Cen kamar minti goma sha uku sai kofofin fatar jikinta suka fara fitar da alamu da mutun mai rai ta hanyar fara fitar da zufa
A hankali jikin nata ya ringa rage yannayi na sandadan din da fatar matace ke dauka ya fara dan rage sanyin da ya dauka sai dai sam bai dauki dumi irin na fatar yawancin mutane masu lafia ba hakan ya saka shi kai dubansa wajen mahaifiyarta, cikin nutsuwa ya furta" idan tana cikin halin rashin lafia takan yi nawa temperature din fatarta?"

Mamanta cikin shakakiyar muryar wace ta ci kuka ta koshi ta ce" bai taba haura 38 ba, domin ita din sam jikinta baya daukan zafi koda kuwa bata da lafia"

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya furta" da ranta, zata farfado in sha Allah dafin bai ratsata sosai ba"
Dubansa ya kuma kaiwa a karro na shida kan NAJEEBA, ajiyar zuciya ya sauke a karro na ba adadi kafin ya mike yana dubansu kasa kasa ya ce" to ki daina kukan mana?"

Su duka shi suka kalla kafin kuma su kalli inda yake kallon, Njaeeba ce ke ta shashekar kukanta, baki daya abin ne ya zo mata a lokacin da bata tsamata ba, tarin tsoro ya sakata neman sikewa da tuna Bintu

Bai kuma kara wani lokacin ba ya juya ya fice a fallon

Wannan karron ta babar kofarsa ya fita da kansa

Tsayuwa ya yi yana bin gidan da kallo

Muryarsa dake ya kai dubansa kan sarkin zabga, liman, amintacensa, sarkin kofa, da du wani dogarin da ya kwana ya waye a fadar dake tare bisa umarninsa, inda ya saka aka zubo masa polisai suka hau wajen aiyukan ma'aikatansa kafin ya gama abinda zai yi

Ya yi kai kawo kamar sau hudu wajen nan yana kallon du wani wanda ke wajen kansa a kasa

Sai da ya ja ya tsaya ya furta" kowa ya dago kansa ya kalle ni "

Baki dayansu mamaki, tsoro, da al'ajabin a dago kai a dube shi ya dirar masu, wani irin su dago su dube shi? "

Gannin du sun kasa ya yi wani murmushin yake a karro na biyu ya furta" umarni nake baku "

Ai kuwa baki dayansu sai sauka ringa dago kawunnan nasu, sai dai da wani irin sauri suke sada dubans7 sakamakon arba da ainahin fuskarsa a bayane, rawanin ya mayar da shi iya kansa, baki daya kamanin mazan da suke hasashe ya bayana a gabansu, irin yanda suke hasashen daurewa irin na sarkinsu sai abin ya dame tunaninsu ya shanye hakan ya saka da yawansu jikinsu kwasar rawa sai daidaikum da suka kasance jaruman jarumai ne suka sada kawunnansu hankalinsu sam ba a jikinsu ba, baki dayansu sunna cikin fargaba da wannan lamarin da bai taba faruwa ba

Affuwa dai Takawa, Allah ya huci zuciyar MAI DAMAGARAM, ALLAH ya sasauta fushin JIMINA, Allah ya huci zuciyar SARKINMU.......Amintace ya fada yana kara sada kansa cike da biyaya

SHAHEED ya budi bakinsa a sanyaye ya furta " Menen laifin su da ake son daga na kawo su a ringa binsu ana kashewa tamkar kiyashi? Shin daukar fansa ne ko kwacen kujera ne? Menene ribar biyowa ta bayan fage bayan ni ake son kuntatawa gani a bagas ba zan iya yin komai ba ana iya koda gile kaina ne domin nima mutun ne kamar kowa, sai dai maimakun mai aikatawar ya biyo kai tsaye sai yake lungu lungu da ni yana cutar da y'ayan mutanen da basu ji ba basu gani ba"

Dan sasautawa ya yi gannin da yawansu basu san inda zancen ya nufa ba, hakan ya sa sukai sakayau da su, a cikinsu kuwa akoy wa'inda suka san inda zancen ya nufa suma sai kara yi suke irin zancen basu gane inda ya nufa ba

A hankali ya dora da fadin " baka jin tsoron Allah ne? Baka tuna akoy ranar tsayuwa ne? Wa'innan da kake kashewa dan son zuciyarka baka tsoron irin huja da hisabin da Allah zai wanzar a kanka a gobe kiyama ne, ko kai zuciyarka ta kekyashe ka zabi duniyar ne wace baka san iya adadin wa'adin da ya rage maka ka cika ba? Shin idanma Allah ya ara maka nisan kwanan ka tabata ita duniyar da kake tunanin yi domintan zaka samu abinda kake son samun ne? Idan *MACE CE?*, idan *LAFIA* ce, ko tunanin mulkin da Allah ya nada bawansa bai cencenta ba dan kannanun shekarunsa ne? Ko wani lamari naka na kanka da ka barawa zuciyarka?, shin ana anfani da damar da aka sani a kaina cewa ko jama'ar garina da inada hali da na hanna masu saka laya a cikin kasata ne ake son kasara min tunanina ta hanyar kashe min iyalaina?"

*ALLAH ya huci zuciyar maza* aka ringa maimaitawa, kowane na tsarge da dan uwansa, sannan magangannun Sultan karara sun fito fili

SHAHEED ya sauke ajiyar zuciya yana mai furzar da hucin bacin rai yana ayanna irin hukuncin da koma wate ya dace da shi ya ce " Ba zan saka alkur'ani mai girma dan samun mai yi min zafon kasa ba, sai dai ina mai shaida masa mumunan labarin cewa ya mayar da rigarsa ta zuwa makabarta dan birne Gimbiya NADIA bisa abinda ta jiyo, domin kuwa bata mutu ba, da ranta "

Du yawanci mutanen wajen ne suka dago kawunnansu a firgice, mutuwa? Da yawansu tsananin mamaki da tsoron furucinsa ne ya saka masu dagowar nan, cikinsu kuwa mugun da ya aikata ne ya dago a firgice shima da jun wannan lamari, bata mutu ba? Tana ina? Da ranta? Me ta ce? Yaya aka yi bata mutu ba?"

"Yaya wanda ya aikata aikin nan zai min daukan wawan da ban san abinda nake yi ba? Harma ya yi tunanin a lokacin da na wanki gawar matata da kaina na suturtata aka kaita ba zan lura da saran macijin da ya kasheta ba, ko kuwa ya yi tunanin da yake ni din wawa ne zan iyakance binkicena a kan macizai da irin hatsarinsu bayan na kasance jinni ga ABDUL MALIK ALI BUZU BA?, shin kun manta sanadiyar sararsa da maciji ya yi a filin daga ya saka shi zuba kiwonsu har sai da ya lakanci raba gangar jikinsu da hakoransu kafin ya iya fitar da karinsu, ya san yanda ake magance dafinsu idan bai gama shiga jiki ba, ya iya bin rawarsu har kuke tunanin zai iyakance sanninsa a kaina ni SULTAN SHAHEED?" ya karasshe da dan daga muryarsa sannan a kausashe ya kaiwa garun da yake tsaye suka mai karfin gaske sannan ya maido dunkulelen hannun nasa ya daki gefen kirjinsa ya ce" lungu lungu camera ce biyayiya a gidan wada ba kowa ya san da ita ba, sakwani tsakiyar dare, kulawa da kuncewa baki daya a tafin hannayena suke, droon kadai kuka san da shi a tunaninku shine kawai zai ringa aiki idan safiya ta yi ina zaune na ringa bi da shi yana dauko min rahitanni kamar wani gaula?"

Dan murmushin takaici ya kuma yi a hankali ya furta" kunna iya tafia "

Ba wanda ya iya koda kwakwaran motsi ne a cikibsu, shi kuwa a tsayen nan da yake idannuwansa kyam a kan mutun biyu da suka yawaita haduwa da junnansu a cikin masarautar idan dare ya raba, wa'inda yake gannin haduwarsu lokaci zuwa lokaci

Shi ne ya fara juyawa, lokaci daya suka kwashi kirari hade da neman afuwarsa, basu su yi shiru ba har sai da ya shige baban falonsa

Idannuwansa ne suka sauka a kan ZINARIA da ya aika kiranta

Bai yi komai ba sai karasawa da ya yi wajen wayar cikin fada ya yi kiran comandan din da aka ajiye yake jan ragamar bada tsaro wa gidan

A kausashe ya ce" ko karamin yaro ne kar ku bashi damar fita daga kowace hanya, ku zuba ido ku yi taka tsantsan dimin na zunguri wanda ya aikata, kuma ya san da shi nake daga yanzu zuwa dare komai na iya faruwa ciki kuwa harda barazana fadawa"

A dake shima ya amsa kafin ya kuma zagewa ya kara tada jinnin ma'aikatansa ya gingindaya sharudan cewa ko mace ko namiji ko yaro ko tsoho ko a halin rashin lafia ko a halin hauka ko a mace kar a fita fa kowa daga masarautar DAMAGARAM!

Ajiye wayar ya yi ya kuma juyowa gare su

A hankali ya karasa ya zauna
Chapter 110 · 0% Book details