← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 138

Sashe 127

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kanta ta dora saman gwuiwowinta, idannuwanta rintse kukanta take kashirban ta kasa baiwa kanta hakuri
A hankali cikin kukan nata take fadin" Why me?, me na rasa Shaheed da zaka ringa nuna min iyakata? Ka san cewar nima ba da gangan na shigo rayuwarka da matayenka ba, ka san cewar ko da na shigo rayuwarka ban so wata shakuwa ta shiga tsakanina da kai ba, aman shine zaka saka na ringa jin tamkar ni kadai keda kai kana wulakanta ni? Menene na nuna min ka tara da wata bayan ni? Na san dama tunda ka kula matar cushe ai wace ka aura dan soyaya sai inda tunaninka ya tsaya a kanta, na san cewar zaka kulata harma ta ji tamkar ta haukace, aman me yasa zaka nuna min hakan a bayane? ........" Wani kukan ta kuma fashewa da shi har tana girgiza kanta dake sara mata , sai wani irin yamutsawa da cikinta ke

A hankali AMMI da ta baro su da UMMU ta idasa shigowa cikin kicin din

Da sauri ta je ta kashe gaz din dake ci tukunyar ruwan ta tafasa sai bori take tana dan kukan nan dake nuna tukunya ta tafasa

Wajen Najeeba ta karaso da sauri ta duka tana kokarin dagota

Cike da tausayinta ta ce" Sorry baby am, sorry hearty am, ba zai kuma dukanki ba in sha Allahu, ba zai kuma gigin taba min fuskarki ko wani bangare na jikin ki ba"

Kanta saman hannayen Ammi, sai ta shiga tariyo marin, kwata kwata ita bama marin take tunawa ba, mari dai ba yau ta fara sha ba, duda wannan marin sai da ta ji kamar ta fara sakin fitsari sai dai wani takaici da ikon Allah zafin maganarsa ta gyashe zafin marin da ta shigo tana juwa dan jinsa
Bata yarda cewar ta zama jaka a duka ba sai yau

A hankali ta kara lafewa a jikin AMMI tana ta sauke ajiyar zuciya, me ya sa? Me ya yi zafi? Me ya sa yake son yi min haka? Marin nawama da ya yi dan ita ya yi? A kan Nadia?

Idannuwanta ta rintse tana jin dacin hakan a kasan zuciyarta, ba dai matarka ba? SHAHEED na yarda ni bani da wani power ban isa ba, kuma in sha Allah zan tatare tabarmata na daina yaudarar kaina na baiwa masu waje su shinfida, domin bani da karfin kokowa da kai, Shaheed ka gama yi min ilar da idan na tsaya jin bakaken magangannunka ina iya macewa bani da ja da zabinka, in sha Allah zan tsawatarwa du wani banzan tunanina a kanka!

Jin jikinta da zafi ya saka AMMI lalabawa ta mike da ita a jikinta

A hankali ta kama hannunta da kyau ta ce" Na jefa maki dan waken zaki ci? "

Najeeba ta yatsine fuskarta ta girgiza kanta a hankali ta ce" Na daina jin yinwar Ammi, zuciyata ke tashi"

Daidai sun zo fita daga kicin din Ammi ta dan kura mata ido tana kallonta, sai kuma ta cire dubanta tana jaye da hannunta a hankali suka ratsa suka wuce dakinta

Tun da suka fito komai ya tsaya masa, kwata kwata ya daina gane yaren UMMU da irin tataunawar da suke, a hankali yake kallonta har suka bacewa ganninsa kafin ya sauke ajiyar zuciya, Kuka? Kuka ne ta yi fa , kennan marin ya yi mata mugun zafi a jikinta da har ta yi kuka? So yake ya mike ya bi bayanta ama ya kasa wani motsin kirki bale ya iya aiwatar da hakan

Ummu ta ce" SHAHEED "

Dagowa ya yi yana kallonta ya kasa amsawa ta ci gaba da fadin" Ka gane, ba zamu iya tunkarar matarka da wata magana ta gyara ba, bama haka, a nan ba'a haka, aman kai ke aurenta, kaima cikin dabara zaka iya kwatanta mata ba kai tsaye zaka fada mata komai ba, domin idan ka fada mata kai tsaye komai na iya faruwa tana iya daykan maganar ta kaita du inda fahimtarta ta nuna mata, hakan kuwa sam bashi da dadi, sannan ko da wasa ka kiyaye fadawa wata maganar wata, mata matsala ne da mu , kamar yanda ka ga kana fama da shara'ar kishiyoyi kala daban daban wace a kowace safia kafin dare ya yi sai an sha shara'ar abokanan zama to hakan ne, wata rigimar bata taka kara ta karya ba ama take zama baba a yi ta yinta har sai Allah ya yi mata tsawa, baban abinda ke daukaka kiyayar mata idan Mijinsu na nuna bambanci, fifiko, ko ya ringa zancen daya a gaban daya haka kawai, idan kana gaban daya ba ruwanka da takalo maganar kowata mace "

Dagowa ta yi tana kallonsa, kawai waje daya ya kurawa ido, kuma cikin ikon Allah har zuwa yanzu a cikin yannayinsa barin jikin nan ne kawai ya daina aman baki daya yannayinsa ya cenza baya cikin nutsuwarsa

Ajiyar zuciya ta sauke ta mike ta dauko masa ruwa masu sanyi ta mika masa

Ruwan kuwa ya kwonkwade kafin ya kuma dubanta ya ce" Umani ai ita ta ja har na mareta ko? "

Shi fa dama ba damuwa ba ya iya, idan damuwa ta shafi cikin zuciyarsa yakan rasa madafa, idan abu ya shafi AMMI yakan rikice ne, ya iya dakewa a gaban mutane ama idan ya samu wanda zai iya fayacewa damuwarsa fila fila to fa yakan manta waye shi ya kasa rikewa, bare ta tabata Najeeba ta shiga wani hali ne, ta tabata a yanzun Najeeba ta afka a ramin da bata shiryawa hakan ba, ita kanta tausaya masu take su dukansu, dan sun zurfafa tsanar junnansu ne hakan ya haifar da zazafar soyayar da suke aikatawa junna aikin fushi da fasara maganar dan uwa

AMMI ce ta karasa shigowa, rigarsa dake yashe a kasa ta dauke babar rigar sai fitar da fitinanen kanshin turarensa take , dakakiyar shadar mai tsadan gaske ta sha aikin sarakunna milk color ta ajiye gefe ta zauna ta ce" tashi ka je bangarenka SHAHEED "

Duban da yake mata tun da ta fito sai yanzun ya kifta idannuwansa, ya je ina? A cikin wannan halin da ya wankawa Najeeba mari har ta yi kuka?

Ammi ta kuma kallonsa tana hade rai sosai kamar wace bata taba yin daria a rayuwarta ba ta ce" ka tashi ka tafi bangarenka lokacin sallah na gabatowa kuka yaren nan dan wake ne zasu yi ka ga har kwabin nasu ya hadu "

Wajen kwabin ya kai dubansa, robar da Najeeba ke tukawa da kwabeben abin da bai san ko meye ciki ba, sai muciyar da ta saki nan kasa sanadiyar shigar zazafan marin da ya sakar mata, sai kwalbar yaji da abin kwai da mayonaise da lemun tsami da magi

Mikewa ya yi dan bin Umarnin mahaifiyarsa, cikin nutsuwa yake takawa har ya idasa ficewa aman ya bar rawanin nasa da babar rigar tasa a nan

UMMU ta girgiza kanta ta ce" Gaskiya kawata kina takurawa Sultan haba, gaskiya ki daina biyewa wancen sangartaciyar yarinyar, meye lagonsa kuka samu ne zaku fara bashi wahala ko me ? "

Yar daria AMMI ta yi, cike da farin cikin da ta fito da shi, da farin cikin gane idanma SHAHEED na cikin halin matsananciyar soyayar Najeeba to fa itama ta kamu da ita , domin abubuwa da dama sun nuna mata haka tun kafin su samu wannan sabanin, idan ka dauka irin yanda ta yi hakuri da maganar fita saloon, ta yi hakuri da fita yawo, Najeeba ce ke yawan murmushi idan ana maganar shaheed maimakun da, abinda ta fi tsana a yi maganarsa, uwa uba yanzun tana shinfideta saman bed ta bata goro ko zata daina jin tashin zuciyar sai ta yatsina fuska ta ce" AMMI, to ai ba sai ya ringa nuna min ya fi son Nadia ba ko? " sun taru sun sakata a farin ciki, AMMI ta ce" wai kin san wani abu nana, anya yarinyata ba tana da wani abu ba? "

Ummu ta yi murmushi tana gyara zamanta ta ce" Ba yarinyarki kadai ta harbu ba, harta Nadia, dan a zaman da muka yi a dakin cen tare na tabata tana da wata kama "

Idannuwa AMMI ta lumshe sakamakon jin wani irin farin ciki na lulube zuciyarta, Alhamdulilah, Alhamdulilah, Alhamdulilah, ta ringa ambata a fili,
Shekaru nawa sunna dakon jiran samun wannan kyauta?, ashe dai bayan Aliyu marigayi yana da rabon samun wani? Ashe dai ba zai biyota ba daga shi dif haihuwa ta dauke ko sama ko kasa? Najeeba na dauke da junna biyu, hakama Nadia? To ita me zata ce da Allah ne da irin ni'imomin da yake lulube ahalinta da su? Zata kara ninka ibadarta ne, zata ringa barin goshinta a kasa ne tana yiwa mai gaya mai duka kirari, zata ringa kai gaisuwa ga fiyayen halita, sannan ta kara rokar Allah kan ya bara mata yan tayin nan, duda hasashensu ne a matsayinsu na datijan da suka ga yau suka ga jiya suka iya bambance abubuwa da dama na rayuwa

Ammi ta mike tana fadin" Mariam, ki zo mu kira docter ya auna min ita Maryam "

Kamo hannunta UMMU ta yi tana girgiza kanta ta ce" ki kyaleta Bilkissu, idan shi din ne da zai bayana kansa, sam bana so ta san da wani abun a yanzu kin fa san shi kansa cikin baya tashi ciwulwutarsa sai an ambace shi, yanzu zo mu jefa masu dan waken nan sun yi gudun tsira "

Daria AMMI ta yi itama ta shiga tatara kayan tana fadin" Allah ya shiryi Shaheed, ka zo waje maimakun a ringa ihun murnar zuwanka aa, kowa fashewa yake abinsa, kuma ba wata magana yake masu ba da ido ne zai ringa bin su uwa ya samu sabuwar hakita "

Itama UMMU dariar take, nan suka shiga shapter abinda ke faruwa idan yana waje da yaren sunna shan daria

A wannan rana sallah kawai ke tashin Najeeba daga nanauyan bacin da ta ringa yi, sai dan waken nan da ta wuni ci, domin baki daya kwadayinta ya taru ya tare a kan dan wajen
Chapter 127 · 0% Book details