← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 138

Sashe 42

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fili sai ta tsinci kanta da furta" Me ya sa kake saka kwali a idannuwanka sai kace wani dan daudu ko boka?

Kansa ya dago jin yanda ta yi tambayarta kai tsaye , abin sai ya zame masa wani banbarakwai, sai yake jinsa normal mutun kamar kowa
Tambayar baba ce, sannan ta rashin kunya ce
Aman sai ya ga ai tambaya ce dan haka sai ya mayar da dubansa wajen Nusaiba ya ce"

Bonjurno🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

24

Mayar da dubansa ya yi wajen Nusaiba wace ya hudawa Ice cream ya saka dan cokali ya dan dibo ya kai bakinta,

A hankali ya furta" kennan ba bambanci tsakanin abinda Allah ya zana da kansa da wanda mutun ke iya sakawa?

Da sauri ta kuro ido ta yi gagawar furta" astaghrullah

Shima yana kallonta ya ce" sabo na yi? Nifa tambaya na yi

Sai a lokacin ta yi kokarin tsurawa idannuwan nasa ido, sai da ta ji har tsigar jikinta na tashi domin wannan kwalin wani kwali ne mai matukar tasiri, kwali ne mai kayar da gaba da saka mutun sada kansa koda kuwa bai so ba, kwali ne dake matsayin fatar mutun ba wai saka shi aka yi ba , hakan ya sa wajen ke daukan du yannayin da cikin kwayar idannuwan ke da shi
Kwalin a yanzu kyalkyali yake duda hasken duhunsa ya dan risina sakamakon gajiyar dake tatare da shi

Da sauri ta kawar da kanta tana jin wata boyayiyar ajiyar zuciya na kwace mata har ta dan sosa gaban goshinta

Cikin nutsuwa ya kawar da dubansa shima a ransa yana fadin" marar kunya na so na ga shin ke bashi da karfin saka ki kasa kallonsa ne ko me?

Nusaiba dake wasa da ice cream din ta lakato ta nufi wajen bakinsa
Shi kansa bai yi jiran zuwan hakan ba domin ya kuma ciran kilishin nan da ya yi masa dadi a bakinsa yana dan taunawa a hankali
Kawo abin ta yi wajen sajensa tana son lakata masa a bakinsa sai ta lakata masa shi a wajen gemunsa

Idannuwansa ya dan zaro yana gannin abin ya bata daria, dan haka sai ya kalli Najeeba
Gani ya yi kanta na wajen wayarta tana dadanawa

Lakuta ya yi itama ya kai mata bakinta hakan ya sa yarinya ta ringa kaucewa ita wasa ne yake mata

A hankali ya ji zuciyarsa na tunzura shi kan ya yiwa yarinyar wasa, dan haka sai ya bada hankalinsa a hankali ya shiga yi mata cakulkuli

Ihun dariyar da take ne ya saka Najeeba dagowa da sauri tana kallonsu

Ido ta zaro gannin yanda Nusaiba ke zaune dare dare saman cinyar bakon mutumen da bata sani ba sai faman wangala masa daria take

Fuskarta ta hade ta ce" Nusaiba

Da sauri yar ta juyo tana kallonta
Najeeba ta ce" meye haka? Me na ce da ke? Bakya jin magana ko?

Da sauro ta sauka daga saman cinyarsa ta koma jikin Najeebar ta zauna tana kallonta ta ce" aunty ba zan kara wasa da namijin da ban sani ba, ki yi hakuri kar ki fasa yawo da ni

Bata kuma yi mata magana ba sai kokarin mikewa da take ta kama hannun kanwar tata

Bata bi ta kan Ice cream din, da naman da kuma dardumarta ba ta nufi motarta

Sai da ya dan bi su da kallo kafin ya mike cikin izarsa ya dan duka ya dauke kayan harda dardumar aman bai ninke ba domin shi dai zai iya rantsewa yau ya fara yiwa wani aiki bayan mahaifiyarsa, ko mahaifiyar tasa aikin ba wani bane sai irin idan sunna zaune yakan dan masaging din hannayenta, ko ya miko mata abinsha ko abin ci, ko ya gyara mata zaman takalmanta dai haka
Sai gashi ya dauko ledar nama, da su ice cream ya bi bayan yarinyar da yake dakon kamata da abinda yake sane da tana aikatawa haza yake son ganni dan hukuntata a fili ba a boye ba ya bita da kayanta

Bayan motar ya saka hannunsa ya bude ya zuba kayan a ciki yana gannin yanda ta juyo tana kallonsa da mamaki

Bata ce da shi komai ba saima jan motar da ta yi bayan ya rufe ta yi gana tana kara yiwa Nusaiba fadan wasa da maza ko waye

Bayan motar ya bi da kallo har suka bacewa ganninsa

Kansa ya girgiza yana dan murmushi, wato da ake cewa wanzam baka so a jikinka haka ne ko? Ita tana yawonta aman tana yiwa kanwarta fadan kar ta ga tana wasa da maza

Fuskarsa ya kara hadewa ya juya ya nufi wajen zaman domin bai gama hutawar da ya fito yi ba,

Zama ya yi ya dora kafa daya kan daya
Dan gishiri gishirin da ya ji a lebensa ya saka shi dan kallon hannunsa
Da san abin mai a jiki irin maikon kilishin kadan sannan ashe abin ice cream din har a rigarsa

Mikewa ya yi ya nufi motarsa
Hannunsa ya mika ya janyo abin goge baki da goran ruwa ya matsa gefe ya ringa goge du inda ya san zai samu abin

Sai da ya gama gogewa tas tas sannan ya mika hannunsa ya amshi kayansa da amintacensa ke miko masa ya koma gefe ya shiga kimtsawa

Yana gyara rawanin kansa ya kuma girgiza kansa a ransa yana ayanna" ita ga salihar mace mai tarbiya? Lale da bakone ni a rayuwarki da hakan ya birge ni, sai dai Zan iya rubuta labarinki a tafin hannunki harda wanda ke baki sani ba! NAJEEBA zaki zamo aya a garina, a kanki zan yi maganin kananun yan tsageran garina!

Ya kasance a wannan dare cikin nishadi da dan sanyi a zuciyarsa wanda ya jima bai ji ba a kala tun rasuwar yaronsa

Tabas wasa da Nusaiba da ya yi ya saka shi jin sanyi a zuciyarsa dan yarinyar sosai ta rukunkumeshi sai da ta saka shi yi mata murmushi mai sauti sannan ya bita da cakulkuli duda sakaryar yayarta ta rabata da shi dan iyayi nata

Adu'a ya yiwa kansa da sauran musulmai baki daya na Allah ya basu masu albarka baki daya

Sai a lokacin ya tuna da cikin jikin Zinaria, cikin na nan ko ta barar da shi? Duda da irin zubde zubden jinnin da ta ringa yi shi kuwa rabonsa da ita an jima, bai san me ke dauke hankalin yarinyar nan ba kamar itace sarkin ba shi ba,
Uzuririkanta sun yi mata yawa, uzururikanta kamar wace keda nauyin talakawa a kanta? Har ya zama uzururikanta sun fi shi mahainmanci
Shi kennan haka zai yi ta rayuwa ne? Sunna kusa da macen da suka fi nisa da junna
Sunna karkashin innuwa daya aman tafiarsu nada tsayi
Bai san me yasa ta dauki wasu lamura da zafi ba
Ya dace ya ringa samun kulawa ta miji da matarsa wace ta amsa sunnanta a cikon dakansa
Takan saka shi jin nauyinta idan tana masa kirarin nan
Wani sa'in har sai ya dubeta da sauri da mamakin shin mata ya aura ko baiwa?
Sam mace bata da lamari irin na tafiar da soyaya yanda ya dace?
Shi dai ba mai kallon film ko sauraron labarun soyaya bane
Yana anfani ne da ilimin da ya karanta na islamiya
Kwarai adininsa ya koyar da yanda zaka gudanar da rayuwar aurenka koda kiwa kai din shugaba ne
Annabi Muhammad Sallalahu alaihi wa salam , shugaba ne na duniya baki daya, aman irin yanda tsarin tsaftataciyar soyayarsa da matayensa ta kasance dole mutun ya yi sha'awar gudanar da irinta

Idannuwansa ya mayar ya lumshe yana jin wani takaici guda gefe guda dake yawan zo masa
Ko tunani take yanda na iya dane tarin rigingimun talakawana zan iya dane rigimar dake jikina? Ko ni din bana tare da sha'awa ne?

Gannin kamar tunanin ya sako shi gaba ya saka shi mikewa ya shiga nafila, zai fi kyau ya samu ladan nafilar tunda dayan ladan ba zai samu ba, ba zai fita ya je bangarenta ya lalabota ba, idan har ba'a nuna mata mahinmancinsa a islamiyarsu ko a gidansu ba ba damuwa, zai kuma kwatanta wani auren!

Dinkuna masu rai da lafia ke shigowa daga wajen telan Anmy na yaran baki daya
Sai dinkunnan da aka ware tela biyu aka kilace suke zuba aiki na gimbiya Zahrau

Aure har ya zama saura kwana daya tak wanda tun fitar nan ta su Najeeba Anmy bata kuma barinsu fita ba baki dayansu

Abincinsu su ke shiga kicin bisa jagorancinta su girka,
Hirarsu sunna dakanta daidai da masu yi mata hidima ta dakatar, su kuwa basu sako komai a ransu ba domin takan yi haka dama idan y'ayan nata suka zo yi mata yan kwanaki

Bakin da suka zo gidan a daren yau ne suka dan fara daukan hankulan mutane
Sai dai ba wanda ya kawo wannan lamari a ransa

Wayewar garin safiyar juma'a, tun da sasafe ana ta karatu da sadaka a baban masalacin juma'a na gidan sarki
Sosai ake kara gyare gyaren masalacin da zagayensa an saka turaren wuta mai wani irin dadin kamshi ya zagaye ko'ina har cikin anguwanin kusa da gidan sarki

Lokacin sallar juma'a na yi wajen ya gama daukan musulmai

Ko'ina ka duba sune cikin shiga mai tsafta tarin musulman garin damagaram ne sun fito ba yara ba manya ba tsofafi, kowa ya fito cikin tsafta da turare a jikinsa ya zo da karfin gwuiwarsa da tarin son kasancewarsa a wannan waje mai albarka wajen da zai gabatar da sallar juma'a

Dawakai biyu dake tafe da ado irin na sarakuna ya shaida cewa yau zunna da baki bayan sarkin garinsu harda wani sarkin

Sosai aka ringa bada hanya ana miko gaisuwa har suka idasa shiga ciki sannan fogaren dake kakare da dawakansu suka rike dawakan aka rurufe saukarsu

Sallah aka gabatar cike da nutsuwa, kafin a ja doguwar Adu'a sai kuma sanarwar a dakata za'a daura auren SARKIN GARIN AGADEZ

Da yake akan yi daure dauren aure wasu har sun fara tashi sai dai jin daurin auren ya saka su komawa suka zauna
Chapter 42 · 0% Book details