Sashe 119
Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya ta dan sauke a hankali ta dan yinkura ta fara mikewa
Sai dai bata rigaya ta idasa mikewar ba muryarsa ciki ciki ya ce" idan kika tashi a nan sai na baki mamaki BEEBAHHHH "
Bakinta ta kara turowa, wai me ya sa ya cika son takurawa rayuwarta ne? Ta ga dai ba maganar za'a yi ba, ai sai a barta ta kara gaba ko?
" Yaya kuka tsara kwanakinku " ya fada yana kara juya dan zoben dake yatsarsa yana mai tsatsare su da ido tamkar zai dauke su da shi, barema NAJEEBA wace du ta takura ta gaji da hararanta da yake
Nadia ta kasa yin magana, dan a tunaninta Najeeba ya dace ta yi magana, ita kuwa itama ta yi shirun dan kuwa bata tunanin wannan hukunci na matar karshe ne
Shaheed sai ya fara tunanin shin raini ne ko me ya sa basu yi gagawar amsa shi sunna dukar da kai kamar yanda Zinaria ke yi ba? Sun wani dake sunna basarwa? Bayan ya yi magana daya dari suke jira ya masu? Hannunsa ya kai wajen goshinsa a hankali yana dan murzawa, kasa kasa ya ce" ya zama wajibima na maido matata sannan na dauko wata dan ba zan dauki wulakanci ba "
Su duka suka dago sunna kallonsa, sai dai Nadia da sauri ta sada kanta, NAJEEBA kau dan kurawa fuskarsa da ta yi ja alamun gajiya na tatare da shi ta yi
Muryar Nadia na rawa rawa ta ce" ka , ka yo hakuri dan Allah mun tuba, Najeeba ce ta dace ta fada ko ko ka zaba mana koma yaya ne ya mana in sha Allahu "
A hankali Najeeba ta maida dubanta kan Nadia, zata iya rantsewa bata taba jin wani abu ya tsirga mata mai kama da wanda ya tsirga mata a yanzu a kan Nadia da furucinsa ba
Idan bata manta ba a
Jiyama ya yi maganar sai ya karo aure aman bata damu ba, sai a yanzu da ta lura da furucinsa kamar irin na serieus din nan ne sai ta ji wani irin lamari na kamar bata ji dadin jin hakan ba, sannan tana kallon Nadia sai ta ji wani iri, wai yanzu Nadia ce kishiyarta? Wace suka hada miji tare? Yanzu abinda ya yi mata a shekaran jiya Nadiama ya mata? Akoy wasu manyan kalamai da ya furta mata wa'inda har yanzun idan ta tuna sai ta ji wani irin yar yar yar, shin itama Nadia haka yake fada mata? A hankali ta fara watsi da kalaman, ta fara kushe su da rage masu karfi a zuciyarta bale har su lahantata
Kuma duban Nadia ta yi, ta san wacece Nadia, a da Nadia kan cewa ita burinta ta auri mai mace ta yanda zasu gwabza rayuwar kishi, kowa halinsa ya kwace shi, ita kuwa sai tace bata son mai mata domin bata taba tunanin wani ya tauna nama ya bata ta tauna itama
Idannuwanta ta lumshe, haka kawai sai ta ji wani irin abu na sukarta a cikin idannuwan nata, a hankali ta dago jin ya daga waya muryarsa kasa kasa yana magana da alama da Yaya Dayabu yake wanda ya shiga garin Niamey a jiya kafin ya ajiye ya dago subansa su yi ido hudu
Janye nata idannuwan ta yi cike da jin haushinsa, haka kawai ta ji wani irin haushinsa ya tsirga mata, wai yanzu zaunar da su ne ya yi yake fada masu zai kara aure? Me yake so su ce da shi? Da su suka saka shi hukunta matarsa ne,?
"Ohk, fine" abinda ya fada kennan kuma ya yi shiru na wani lokaci kafin ya dora da fadin" ki fada min yanda kike so Nadia "
Kanta ta dago ta kuma kallonsa a karo na ba adadi sannan itama ta sauke ajiyar zuciyar, ta maida dubanta wajen NAJEEBA ta ce" dai daya ya yi ko Najeebana? "
NAJEEBA ta lumshe idannuwanta ta komar da bayanta a hankali ta jingina jikin kujera, kanta ta iya dan dagawa a sanyaye sannan dake
Sai Nadia ta ce" Alfarma nake nema Allah ya taimake ka, kafata bani da lafia bana iya komai da ita dole sai nai jinya, idan har da hali ina so idan auntyna ta zo mu je gida tare, ba dan na raina kokarin AMMI ko gazawarku ba, MAMA yanzun ba zata kuma zama da mu ba, ni kuwa na tsorata sosai, ina neman alfarmar na je koda sati daya ne na kara warwarewa....."
Ta idasa maganar tana sada kanta kasa
Shaheed ya kwashe minti biyar yana nazarin maganarta, ta gama sarewa cewar ba zai bata amsa a kan hakan ba, sai ji ta yi ya ce" wani wajen maman ta ce da ke zata tafi ?"
Da sauri ta dago kanta tana girgizawa, sai kuma ta mayar ta sada cike da tsoro, ita a ganninta an maida auren mama me zai sa ta kuma zama a nan kuma?
Shaheed ya lumshe idannuwansa yana kallon NAJEEBA, haka kawai yannayinta sai ya ringa taba nutsuwarsa, wannan dakewar da ta yi sai yake so ta dago koda tsokana ne ta yi yana kallonta
Dan ya kara kular da ita, wanda ya tabata sai ta kale shi , haka kawai jikinsa ke bashi idan ya fadi haka zata kale shi
Sai ya ce" Ni kuwa na yi baci ta yaya bayan kina nesa da gidana ? "
Da wani irin madaukakin mamaki NADIA ta kai dubanta kansa, a lokacin kuwa ya yi iya yinsa ya cire dubansa daga cikin idannuwan Najeeba ya dora kanta ya sakar mata san murmushin da ya sakata jin wata irin nutsuwa a cikin zuciyarta
Tana sada kanta ya maida dubansa kan fuskar Najeeba, ya ci gaba da fadin" idan ta zo zaku tare a bangaren da ba'a bude ba, na kusan bangaren BEEBAHH, a cen za'a baki dukan kulawar da kike so, sannan zan saka jakadiya ta kai maki kati biyar kina iya rabawa wa'inda kike son su ringa shigowa gannin ki, aman fa daga satin nan zaki dawo nan ladanki "
Murmushi ta saki tana kara rage tsayi daga zaunen da take ta ringa gabatar da godiyarta
A hankali ta kai dubanta wajen NAJEEBA, sai dai gannin idannuwanta a lumshe sai ta shiga kokarin mikewa dan zuwa ta amshi maganinta, sanan ta tabata zai bukaci yin magana da matarsa
Tana tafia a hankali ya maida dubansa sosai kan NAJEEBA, kallonta yake da kallo irin na son dole ya karance ta
A hankali ya ciciba daga inda yake ya koma kujerar dake kusa da ita ya zauna
Hannunsa ya dora saman nata dake jimke kadan saman cinyarta hakan ya sa ta buda idannuwanta a karro na biyu sunna kallon junna
Muryarsa ciki ciki sosai ya ce " sai na ga kamar ranki ya bace dan na yabi matata "
Dan yawun da take tunanin ta bari a bakinta ta tatara ta hadiye da kyar sannan ta fuskance shi, itama a sanyayen ta ce" anya ba sai ka je asibitin idannuwa ba kuwa? Domin dai idannuwanka sun fara baka gannin da ba daidai ba "
Kallonta yake bai bata amsa ba
Sai da ta ja hancinta a hankali ta dora da fadin" yaya zaka yi tunanin zan bata rai a kan auren da biyaya nake kawai?, kamar yanda baka so inaga nama fi ka so, dan ka san yanke min nishadi aka yi rana tsaka "
Bata karasa maganar da take ba ta ji saukar lebensa a kan nata, idannuwansa kulle sosai ya kama lebenta ya shiga basu wani irin horo mai zafin gaske wanda ya sakata saka hannunta tana ta son ture shi, aman ko gezau saima da ya ga dama dan kansa ya sake ta
Bai yi nisa da fuskarsa a jikin tata ba ya tsatsareta da kakausar murya ya ce" dan ki gane idan mai wuri ya zo dole mai tanarma kan nadewa, beebah ko kina mutuwa kina farfadowa ne kin harmatarwa wani, koda kuwa zaki hadiyi zuciya ne sai kin dandani azabar da kika kwashe shekaru kina dandana min, beebah meye samari basa fada maki, wayarki a hannuna sakon tsohon cen ya shigo cewar ki bashi nutsuwa?, sannan baki dadara ba kike ci gaba da neman fitina a gare ni, ba zaki gane ba, ba zaki taba gane komai ba, aman ki sani ina daf da dauke numfashinki ki dawo na kuma dauke shi ta hanyar hade bakin ki da hancin ki na rufe ki suma harma ki leko kiyama idan ta kama, domin ni narka min dalma da kike a wajen da ba zaki taba hasashe ba a sannin kanki ya fi karfin sumarki, beebah ina maimaita maki ki bar balaki ya yi baci, idan ba haka ba zaki haka mana ramin da zamu rufta ya halaka mu !"
Ya karashe maganar da kakausan murya tare da dantse lebenta na kasa da dan karfin da ya sakata fashewa da kuka ta saka hannayenta bibiyu ta shiga dokawa a kirjinsa ido ryfe ta ce"
My kaina😓
[3/31, 11:30 PM] BAK'A CE: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*Na*
*SAJIDA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
60
Hannayenta bibiyu ta shiga dokawa a kirjinsa idannuwanta rintse tana jin wani irin tashin hankalin take sukar mata kahon zuciya, meye wannan? Me ke damunta haka? Me ke kara gudun zuciyarta ya dada mata zafin jiki ya hasasa mata fitar numfashi da sauri ya sababa mata bacin rai a kan furucin farin mutun mai mata SULTAN SHAHEED ne? So take ta buda idannuwanta ta samu karfin gabatarr da fushinta a kansa, aman a irin abinda take ji da zufar da take fitarwa sai ta fara tunanin idan har ta buda idannuwanta tabas idannuwansa masu dauke da zanen kwali zasu hadiye nata hadiya irin wace maciji kobra ke hadiye dan uwansa a lokacin da suka tsinci kansu a waje na rashin abinci, zai hadiye su ne murus ta yada zata rasa idon duba a gabannan