← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 138

Sashe 51

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Du yawancin yan matan wajen shi suke kallo, babar yarinyar Najeeba ta kawar da dubanta daga kansa ko jus din da aka ajiye masa bai taba ba, Najeeba kuwa tana jinsa ta yi kamar bata san me yake fada ba sai da ta tsaga gaban kadan ta saka wata yar na'ura mai saka gashi ya bi umarni ta ringa bi a hankali tana kara kwontar da shi ya yi lumbuk a gefe guda ya kwontar da hankalinsa waje daya sannan tsagar ta fito sosai
Dan gel ta bude ta ringa lakata da broch cike da kwarewa ta ringa dan kwonto da kananun da suke gaban goshin hakan ya sa nan da nan budurwar ta kara wani shegen kyau tamkar gashinta ya yi mugun hadewa da gashin nata domin kalar daya ne sannan yannayin santsinsama daya ne

Dan ribom sabo ta siya a nan aka daure mata shi a tsakiya sai murna take kamar me kafin a saka mata gashin ido a gyara mata girarta
Itama ta ci kusan jaka goma sha talwas da rabi sannan ta roki idan zata samu mak'up gobe domin auren yar uwarta ne ake

Sai da Najeeba ta duba time din da take so ta amshi numberta tana mai sheda mata zata duba ta gani zuwa safe zata bata amsa idan har zata samu i.a

Kudin da ta bata ya mike ya dauko ya zauna yana kallo, budurwar ya bi da kallo har ta fita kafin ua maido dubansa wajen NAJEEBA da ta dawo ta zauna tana dan matsa yatsutsanta

Nadia ya kalla ya ce" Nadia, yanzu duka wannan tsayuwar da matata ta yi tana faman aikin nan sun tashi a wadinnan yan kudaden? Duba fa ki ga yanda ta kayar da wancen budurwar kamar gashin kanta ji yanda ta zama wata mai kyan gaske wannan tana fita ta fara wankar maza aman kuma sai kudin aikin matata ya zama ko jika ashirin bai rufe ba?

Sansanyan ruwan da daya daga cikin masu gyaran wajen ta bude ta zuba a tsaftatacen kofin gilas ta miko mata ta amsa ta sha ba mai yawa ba ta mika mata ta dora kafarta daya kan daya kafin ta kai dubansa wajensu Nadia sai kwatanta masa take cewar ai haka aikin yake kuma ina laifi kana samun haka ko a wuni ne baki daya bale kafin a tashi za'a samu kudade na mamaki domin saloon dinta ya zama saloon din da sai manyan mata ko yan mata masu ajin gaske ke zuwa domin akoy kashe kudi sosai sai dai aikinta daban ne ko a waje

Dubansa ya maido kanta ya ga su take kallo
Kudin ya ajiye yana dubanta ya ce" me yasa ba za'a bani dama ba? Bana tunanin zan iya bari ki ci gaba da zuwa wajen nan, zan sama maki aikin ofice ki kasance a kilace Najeeba, idan wata ya mutu ki dafe manya manya dan na san takardunki, Nadia ta fada min irin takardun da kike dasu

Murmushi ta yi tana kallonsa ta ce" waye ya ce maka aikin office ke birge ni? Ka ga aikin nan, shi na tashi da shi a cikin abubuwan da nake son yi a rayuwana shi yasa ka ga na ware nan
Da kake maganar aikin office, kidaya min zan iya samun nawa a wata?

Huzaifa da gagawa ya ce" zaki iya samun jaka dari hudu, ke har akoy na dari biyar din da zan iya zuwa na samu abokin mahaifina ya sama maki gurbi a wajensu domin idan ya ji matata ce zai samo mana da guduma

Murmushi ta masa ta ce" a ranakun da ban yi kwaliya ba, nakan tashi da jaka dari da arba'in, ko dari da hamsin, idan ba'a samu isasun mutane ba nakan tashi da jaka saba'in ko tamanin

Idan na samu yan kwaliya, amare nakan yi masu kwaliya a jaka hamsin, kawayen amarya kiwa jaka ashirin masu zuwa wajen biki jaka goma
Akoy ranakun da nake tashi daga shago da zunzurufun kudade kusan jaka dari hudu ko sama domin idan aka ce maka juma'a ce, asabar da lahadi wajen nan cika yake da mata da yan mata, amaren ne da uwayen gida,

Wayarta ta janyo iPhone tana kallonsa ta ce" irga min, ka dauka a jaka dari dari kulun zan iya tashi da nawa a wata?

Nadia ta ce" million uku

Najeeba ta yi murmushi ta ce" ba ruwa nake biya ba, ba ni ke biyan wuta ba sai idan na yi ra'ayi, Abih ke biyan duka
Idan kayana sukai kasa Anmy ke min oder ta cika min shago

Idannuwanta ta kara kura masa ta ce" shine zan je office na yi me karkashin ikon wani?
Murmushi ya ringa yi , a ransa kuwa ya yarda cewar ashe dai kasamcewarta babar yarinyar ba iya iya kwaliya da kyaun tsari ta tsaya ba, aljihunta nauyi ne da shi, rikakiyar boyayiyar mai kudi ce , to aman yaya aka yi ta zama lashe money? Shi fa ko gara ce ita wace take iya karar da dukiyarsa ya ji ya gani yana sonta

Rage muryarsa ya yi ya ce" ina son ki NAJEEBA

Sai da ta ji wani dan ras, tabas zuwansa kai tsaye da kalamansa na sakata kallonsa da duba na daban

Cire dubanta ta yi daga fuskarsa hakan ya saka ya kara matsota sosai yana kallonta ya ce" ina son na aureki Najeeba, dan Allah ki yarje min mana?

Kuma duban fuskarsa ta yi, tabas Huzaifa namiji ne mai kyau bakar fata ne shi mai tsafta,
Yana da fara'a sosai gashi mai tsayi daidai misali, yana da kakauran jiki sannan yana da dan tumbi na jin dadin rayuwa

Murmushi ta yi tana cire idannuwanta daga kansa,
Wayarta ne ta dauki kuka da wakar su akon wace yake fadin For ever i love for ever........ da yake ta kuma ajiye wayar a saman kujera ya saka du suka kai dubansu

*LIKITAN ZUCIYATA* , shine ke haskowa a saman sunnan mai kiran

Bata damu ba ta mika hannu ta dauko sannan ta daga

Salama ya yi mata kafin ya furta" ina cike da begen ranar da zan ganki, shin kina Niger kuwa?

Sai da ta dan saci kallon Nadia ta ga kamar zata dauketa da mari sannan ta dan yi murmushi tana satar kallonsa sai ta ga fuskarsa ta dan cenza daga yannayin fara'a zuwa sad

A hankali ta ce da shi" zan taboka Likitana

Shima murmushi ya yi ya kashe yana fatan ta tabo shin

Idan kana da time, ranar Wednesday ka zo fada

Farin ciki ne kuma ya mamaye zuciyarsa harma ya kasa boyewa da yatsunsa ya irga cewar....nan da kwana uku ko?

Kanta ta daga hakan ya sa ya mike, chek din da ya rubuto makudan kudi ya ajiye kusa da wayarta sannan ya juya yana murmushi ya masu salama

Da sauri Nadia ta dauki Chek din tana dubawa sai da ta yi dan ihu kafin ta ce" ke, wai kin san nawa ne?

Najeebama tana ta daria tana kallon chek din ta ce" da alama dan uwanki banar harka ne

Nadia ta ce" Najeeba ina fada maki ko waye shi kennan baki yarda ba? Babar harka ne,

Najeeba ta ce" na san waye shi, abinda ya sa na bashi matsayin babar harka nawa suke da kudi aman basa iya cirewa su yi kyauta da su? Sai ki ga sun tatare budurwa ita ba ga wani ba sai su kadai aman dan iskanci kudin zuwa saloon sunna bakin cikin bata? Gaskiya irin mazan nan basu da Mutunci!

Nadia ta ninke ta soke mata ita cikin jakarta tana fadin" bana tunanin zai kasance irin mazan nan, domin ni kaina dominki kwana biyun nan hajia ce bale ke

Ita dai Najeeba litafin da ake rubuta wa'inda suka nemi mak'up ta dauka tana ta dubawa dan gannin wanda zasu samu

Sai d yama ta yi sosai wajen ya kuma fara saukan mutane masu fitar dare

Ita dai zuwa lokacin sai ta kilace kanta sunna hira da yar uwarta wace ke magana kasa kasa bata jin dadin jikinta domin a jiya dai sarki sai da ya karbi sadakinsa

NAJEEBA ta zaro ido tana ganni uwar sarkar da ya baiwa Zahrau da makulin mota da hoton motar da kyautar wasu kuyangin amana kafin ta ce" Zahra wai kyautar meye wannan?

Zahrau ta yi murmushi kawai ta ce" zaki san ko ta meye, ba yanzu ba

Itama murmushin ta yi tana kallon uban badon da ta markada ta zabga masa madara da karanfani fiye da adadin da aka bukata ta kafa kai ta shanye
Zahrau da suke vido call ta zaro ido ta ce" Najeeba, ba zaki daina shan kayayakin gayran jikin nan ba ko? Gashi wa'inda kike dura min sai da na raina kaina , Najeeba sai da na ringa maki Allah ya isa

Najeeba ta yi murmushi tana gyara kayan gefe guda sannan ta rufe frij dinta ta koma ta zauna ta ce" aunty, ko gobe na ji abu naturel wanda zai sharen fage ya gyaran jiki zan yi na sha abina dan a gaskiya ba zama zan yi sai an tashi yi min aure a shiryani ba

Zahrau ta girgiza kai ta ce" anya ba babar mai jaraba bace ke kuwa? To yanzu idan kika auri mijin da hakan bai dame shi ba?

Najeeba ta yi murmushi ta ce" aunty ai shikenan, kin manta ban saba ba bale hakan ya wahalar da ni? In sha Allahu ko wani kalar miji na samu shi zai horani ta yada yake so na zame masa

Zahrau ta yi murmushi ta ce" wa kika tsayar? Dayabu ya fada min komai, dazu mai martaba ya turon sakon na tura number Ummu yarima na tambaya zai kirata , ke da Ummulkhair ku na sako gaba yanzun

Najeeba ta koma ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce" ni kaina ban sani ba, abinda nake son yi zan tsaida kwara biyi, a cikinsu sai na kaiwa Allah kukana kan ya zaba min daidai da ni
Chapter 51 · 0% Book details