← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 138

Sashe 21

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kansa kawai ya dan girgiza ya maida ya ci gaba da jan carbinsa

A ranar NAJEEBA bata fita saloon ba, sai washe gari wajen karfe goma

Ta gama shiryawa cikin tsararan shirinta
A yau riga da sket ta saka na atampa
Bata daura dan kwalin atampar ba sai wani dan kwali ja irin takalmin kafarta da jakarta ta dan yafa a gefen kafadarta

Hannunta dauke da agogo dan siriri yatsotsunta kuwa basu da zobe ko daya

Kanshin turare take bazawa mai dadin gaske ga turaran wuta da ta turarawa kanta sosai take baza dadadan kamshi

Ta zo tsakiyar gidansu ta hadu da yar kanwarta wace ita daya ce ta rage a gidan sauran du sun tafi makaranta masu aiki sun tafi aiki, itama dan karama ce

Murmushi ta saki ta karasa wajen yarinyar ta duka ta dagota tanai mata wasa

Yarinyar kuwa sai daria take tana dora kanta saman kirjin Najeebar

Najeeba ta duba kitson kanta ta ce" heyi an mata kitson nan ya tsufa mu je saloon a tsefe shi a sake sabo

Daga nesa da su kadan ta ji muryar matar babansu na fadin" kar ki daukan min y'ata ta saka ta ringa ramewa dan datin dake jin ki! Ajiye min yarinyata malama

Dagowa ta yi tana kallonta
Ta ga tana fadi ne tana nufota wato zata zo ta amshe yar

Mikewa ta yi da sauri ta sungume yarinyar ta karasa wajen motarta wace ta sha wanki dan da sasafe dan saurayin mai gadin ya amshi kys dinta ya wanke mata ita tas domin Najeeba nada kyauta sosai hakan ya sa kowanensu ke son kyautata mata koda bata nema ba

Cikin motar gidan gaba ta saka yarinyar ta rufe ta koma ta zauna itama ta rufe motar

Sai da ta danne horn sannan ta tayar ta yi baya baya da matsiyacin gudu wanda take hango matar baban nasu na ihun ta bata y'arta aman ta tabe baki ta fita a gidan da baya baya

Gashin kanta ta take birki ta nade shi dan ya fara damunta sakinsan da ta yi sannan ta dauki hanyarta tana tukin tana yiwa yarinyar wasa

Cikin nutsuwa ta karasa kofar shagonta

Sai dai irin motocin da ta gani ya sakata dan yin tsam tana bin su da kallo

Tas ta gane motar dake gaba ba motar kowa bane face ta matar Ambasador domin motar tare ya siya masu ita tata ta siyar dan su yaya ba zasu barta hawa motar kato haka kawai ba

Dama sun taba message da junna inda take mata kashedin bin mijinta har tana kiranta cewa" an koro su daga kasarsu sun zo sun samu arziki sunna bibiyar mazan mutane, abin ai gado ne ga kanwar ubanta ta amshe sarki kiri kiri , ga mamanta ta tafi yawon neman kudi ko karuwanci ba!

Hannayenta ta hade ta dan murza su, ta dauko turaranta ta kara fesawa ta kara gyara girarta sannan ta dauko kanwarta tana kara yi mata wasa ta fito daga motar aman bata dauko jakarta ba dan kayan hannunta sun mata yawa

........cikin nutsuwa take takawa har ta karasa kofar shagon.................

Hannunta ta saka ta kwonkwasa dan a bude mata tana kara kallon kofar shagon ta ga tsaftarsa ta yi mata sosai

Sai da ta yi murmushin dama ke nake jira ta kalli kawayenta ta nuna masu da bakinta sannan ta mike bugudum bugudum bugudum ta karaso wajen kofar ta dora hannunta ta............
[1/20, 9:50 AM] Ummu Suhan😍: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

12

Bakinsa ya buda zai yi magana, sai dai ta rigaye shi ta hanyar juyawa ta waiwaya ta kuma juyowa wajensa

A rikice take, hankalinta a tashe yake hakan ya sa a hargitse ta nuna masa motar ta ce" zai zai taba min jikina

Idannuwansa ya kausasa yana dubanta,
Sai da ya yi iya yinsa ya kara matse damatsunnan hannayenta dake cikin dafin hannayensa ya ce" ba abinda ya kawo ku nan kennan ba?

Magana ne ya yi mata a kausashe, a kidayance ,
Iskar bakinsa dake kusa da ita sosai ne ta fito ta daki hancinta

A hankali ta lumshe idannuwanta tana jin zafin rikon da ya yiwa hannayenta

Kanta ta ringa girgizawa da sauri ta ce" aa, aa, ni ba yar iska bace

Idannuwansa da sukai ja ya kai dubansa wajen motar, gannin na cikin motar na kokarin fitowa ya saka shi yi mata wani ja tamkar ya ja dan karamin yaro sosai

Sai da ya kara yin cikin duhun da ita ya sasauta mata rikon karshe ya saki hannayen nata
Da yake ya jima cikin wajen, ya fita ganninta sosai duba da ita a rikice take sai abin ya mata yawa take ta neme nemen inda zata saka ranta

Bakinsa ya tabe ya juya da sauri zai tafi

Da wani irin karfi ya ja ya tsaya hakan ya sa ita da ta tarbi gabansa dukan kirjinsa da goshinta

Hannunta ta kai gaban goshin nata tana sosawa a hankali ta ce" aushhhhhh

Tsayawa ya yi kawai yana kallonta

Sai da ta sosai sannan tana dubansa ta ce" dan Allah ka taimaka ka fitar da ni daga wajen nan, walahi ban taba zuwa ba kar wancen mugun ya cin min

Ji yayi gaba daya ta gama raina masa wayo, itane take gudun kar namiji ya cin mata? To ko ta danfaro shi wasu kudade ne take gudun ya kamata ya amshe?

Sai dai irin kallon da yake mata zai iya gannin yar karamar wayarta a jikinta ta cikin rigarta sakamakon rigar a matse take sosai
Bayanta baya gannin kudi ko abin kudi idan dai ba a cikin sket dinta ta saka ba
Shi zata kalla ta rainawa hankali?

Kansa ya girgiza ya ce" ba saurayinki bane?

Najeeba bata taba zuwa wajen nan ba, sannan zata iya rantsewa bata taba samun kusanci da namiji irin yanda Ambasador ya yi mata a yau ba
Hakan ya sa baki daya jikinta ke rawa takaici ya gama rufe mata zuciyarta

Hannunsa ya kai ya damki hannunta ya juya ya shiga janta

Bin bayansa kawai take
Bata san shi, bata taba haduwa da shi, bata san mutun ne ko aljan ba, bata san shima zai cutar da ita ko akasin hakan ba abinda ta sani daya ne tana son ta yi nisa da motar Ambasador
Tana so ta yi nisa da shi baki daya dan tana da muradin kasancewa ita daya
Gani take ko ina ta bi idan ta zo wucewa yana iya ganninta, gani take zai kuma yin yinkurin aikata mumunan aikin nan da ya yi na hada jikinsa da ita

Sai da ya fito bakin titi da ita ya saki hannunta

Juyawa ya yi yana tafia cike da wata irin kasaitar da ta sakata zubawa bayansa ido

Tsalaka titin ya yi wanda har sai da ta rintse idannuwanta sakamakon wani mai mota da ya so kade shi cikin ikon Allah maimakun ya tsere da sauri ko ya yi gudu dan tseratar da rayuwarsa sai ya zama mai motar ne ya take birki har hakan ya yi kara sosai

Tana buda idannuwanta ta ga ya tsalaka, bai kade shi ba mai motar ya leko kansa yana fadin" ka ga malan rai zaka yiwa kwombo? Ka wani hau bakin hanya kana tafe da takama tamkar *mai DAMAGARAM?*

idannuwanta ta yiwa luuuu ta ga ya shige kwanar hakan ya sakata daga kafarta a hankali tana gyara rufar lafayarta

Ta sha cika dare a shago dan takan kai har sha daya idan aiki ya mata yawa
Aman yaya DAYABU ke zuwa ya tarbota su tafi gida

Yau sai ta ringa tafia tana hankalce da mutane cike da tsoron daren

Da haske ko'ina ba wani duhu ya game garin ba

Mai mashin ta tsayar ta hau ta fada masa ya kaita anguwar gidan sarki

Yana kaita ta bashi mai akun nan guda dake bayan wayarta

Ido ya zaro ya ce" haba dai Hajia yaya zan samu cenjin wannan?

Bata yi masa magana ba ta juya ta nufi ciki tana tafe cikin nutsuwa

Baki da hanci ya saki yana kallonta har ta shige babar kwanar gidan sarki

A hankali take tafe tana jin zuciyarta na dokawa dan bata san yanda za'a yi ta samu shiga ba

Motar da ta hasketa ne ta sakata rintse idannuwanta ta rabe waje daya

Kusa da ita aka tsaya tana jin jikinta ya dauki rawa dan sam bata son aikata laifi a wannan waje

Wanda ya fito daga motar ya sakata sauke ajiyar zuciya

Da gudu ta karasa ta fada jikinsa lokaci daya ta saki kuka tana kara dora kanta a jikinsa

Kiransa Anmy ta yi cewa bata ga NAJEEBA ba, maza ya samo mata ita

Gabansa ne ya fadi ya shiga kokarin cireta a jikinsa sai dai ta ki bada dama tana kara shiga jikinsa tana hawaye

Muryarsa a cakule ya ce" NAJEEBA, meye? Me ya faru? Me ya same ki? Ke da wa?

Kukan take tana jin ciwo a ranta , gannin ya bambareta daga jikinsa tana kallonsa ta ce" yaya, me me yasa kowani namiji yake son nuna min shi dan iska ne? Yaya me ya sa suke son nunawa mutun iskanci?

Gabansa ne ya kara faduwa hakan ya saka shi kurewa fuskarta kallo
Muryarsa na rawa rawa ya ce" Najeeba, kar ki fada min abinda zan tsani kaina , kar ki fada min abinda zai sakani yin gaba da ke
Mutuncinki kika zubar?

Da sauri ta rintse idannuwanta dan jin maganar da girma sosai a kunnayenta

Sai kuma ta bude tana girgiza kanta tana kokarin rungume hannayenta a kirjinta

Hannunta ya kamo ya sakata cikin motar ya tayar ya juya cikin gidan

A hankali yake tafe har ya karasa wajen ajiyar motoci

Yana dakatawa ya kashe motar a hankali yana sauke ajiyar zuciya
Chapter 21 · 0% Book details