← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 138

Sashe 88

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dubanta ta maida wajen su DAYYABU , a hankali ta furta "Ku tashi mu shiga ciki"
Duk mikewa suka aniyar yi suna kama hannun Najeeba ta mike kafin su nufi cikin

Wudiliya ta kalli MARDIYYA da ta yi mutuwar tsaye ta gyada kai cike da mamaki

Mardiyya ta karaso ta zauna tana kallon Ammi ta ce "Ammi baki ce komai ba, ko ya sake ni ne bani da labari ya auro wata?

Ammi ta kalleta, bata gane ta mata shiru ne dan ga bakuwar fuska? Sannan bata so maganar ta yi nisa irin haka a gaban yaran?
A hankali ta furta mata "Mardiyya, kar ki damu zan kiraye shi yau, idan ya so zai zo koda kuwa da ni ta kama zuwan zamu zo"

Yar dake kuka ta dire mata ta mike ta fara kama hanya
Da sauri Wudiliya ta mike ta bi bayanta

Sunna fita Mardiyya ta ja ta tsaya ta keta wani ashar tana fadin "ldan na yarda ya banzatar min da aure shegiya nake" (shi ya banzatar maki ko ke?)

Wudiliya ta ce "Yau na ga bariki gannin idona, kina zaune za'a yi maki sakiyar da ba ruwa? To ko danginsu ce ita wannan matar dake goye da Nusaiba? Ke anya baki yi sake ba za'a maki sakiyar da ba ruwa? Anya ba wasa kike da lamarin MUTALAB ba?"

Mardiyya ta kalleta, da kallo irin na son karin bayani
Wudiliya ta ce "dubi yanda y'ayansa suka nuna basu san da wata halitta wai ke a wajen ba, kuma suna kiran wancen da sunan Mama, dubi fa yanda babban dansa ke hira da ita kamar wace ta nakudo shi? Anya ba wasa kika tsaya yi ta fi ki iya bariki ba har ta fi ki fada a wajensa?"

"Ke kika san dalilin rabuwarsu? Kin ga kar ki wani raba min hankali, ina ce kin rakoni ne dan ki tayani sakawa ta masa magana? Nima ba zan yarda ba, wannan tsohuwar da na tabbata ta haife ni na rantse a yanda na san MUTALAB na tabbata ba zata dauke hankalinsa a kaina, inaga yar uwar tasu ce kuma kin ga bama zan bi ki ba zan koma na nuna hankalina ya ki kwonciya saboda jikin Nusaiba, zan jira shi ya zo ya fada min matsayina a wajensa a yanzun ehe, maganar y'ayansa basu gaisheni ba kuwa ban damu ba, dama me kike jira da fitsararri tambaɗaɗɗi yan iska?" Mardiyya ta ida sa zuciyarta cike da wani tsoro da jin wata fargabar gannin Ummu, kwarai irin yanda ta ga yaran sun sake da Ummu ya daketa, irin yanda Ummun ta wani nuna ita din isasshiya ce a gidan ya daketa, ta jigata, accnt dinta ya yi kasa sosai, motarta tana bata wahala, ta je gidansu ya ce zai waiwayeta ya manta da ita, ko auren Najeeba sai a redio ta ji da kuma yanar gizo, ana ta yi mata barka wai ita matar ubanta, kwarai a yanda ta san MUTALAB da kwakwar mace ya bata mamaki, aman zai zo ba inda zata motsa wallahi kafarsa kafarta da tsiya tsiya! (Ko? Tsiya tsiya fa? Namijin? Ko kannin kemenka ne ka bishi a laluma domin yana dauke da igiyar da idan ya tsula maki ita sai kin rasa gane hanyar gidanku ko wacece ke!)

Kasa ce mata komai ta yi tana binta da kallon wawuya, idan ba wawanci ba ko Mutalab mahaukaci ne ai ita bata ga ubanda zai cireta daga gidansa a haka ba, bale mutumen a tsaye? Da alama Mardiyya sai ta sha bulaliyar duniya zata yi hankali

Du irin yanda suke so ta fada masu abinda ke damunta kallonsu kawai take, sai da ta ja iska a hankali ta kalli UMMU
Idannuwanta cike da kwallah, muryarta a raunane ta ce" me ya sa kika tafiyarki a lokacin da muke cikin rayuwar bukatar ki? Me ya dawo da ke a yanzu?"

DAYAyBU ya furta "NAJEEBA, meye haka?"

Najeeba ta dube shi ta ce "Yaya? Kai baka ssn sanin dalilinta na tafiya ne ko ka san dalilin nata ka ki fada min? Tsananin son kudinta ne ya hanata zama tare da mu ko kuwa bata dauki aurenta da mahinmanci bane? A yanzu da take son tirsasani zama da auren da bana so a matsayinta na wacce ta tafi ta tsinke nata auren tana tunanin zan mata biyayya ne?"

Da mamaki ya zaro ido, muryarsa kausashe ya ce "kina hauka ne? Mahaifiyar taki kike yiwa irin maganar nan, titaiyeta zaki yi kan abinda ba dolene sai ta fada maki ba ko fada zaki yi mata kan rayuwarta a matsayinta na mahaifiyar ki?"

Dan murmushi ta yi tana janye hannunta daga cikin na Ummulkhair, da yar yatsarta ta nuna Ummukulsum a sanyaye ta ce "abu nawa rashin uwa a kusa da ke ya tauye maki?"

Juyawa ta yi wajen Ummulkhair ta ce "har gobe cikinmu wa ke kukan da ace mamansa na nan?"

Zahrau ta nuna ta ce "yaya kika ji dadin zuwanta kusa da ke a yanzu?"

Ta koma wajen DAYYABU ta ce "da ace da daya wace ta rungume mu da yanzu ka haifi y'aya biyu ko uku, amma kasancewar kaine uwarmu a kulun tunaninka idan ka yi aure kar ka kawo wace zata daga maka hankali a kanmu"

Daga idannuwanta ta yi zata kuma yin magama suka sauka a kan ABIH, tsaye yake yana kallonta, duk basu san da zuwansa ba wanda tun da Mardiyya ta shaida masa zata je a message ya azamar ajiye abinda yake dan ya tarda ita kar ta je a yi rigima domin ya san wacece Mardiyya haka kuma ya san wacece NANA MARIAMA idan aka kawo mata raini

DAYYABU ya budi bakinsa a sanyaye ya ce "kennan har yanzu baki daina jin haushin auren nan naki ba?"

UMMU ta buda idannuwanta da suka cicika da kwallah
Karasawa ta yi ta zauna kusa da su sosai
Idannuwanta a kan Najeeba wace ta sada kanta tun da ta ga ABIH a tsaye

A hankali ta lumshe idannuwanta ta kuma budewa a kanta
A sanyaye ta furta "Ban taba aikin da na yi nadama irin tafiyar da na yi na barku a lokacin dakuke da bukatata ba, bayan sanin da na yi cewar y'a mace na samun tarbiyya ne daga mace yar uwarta, na san wa nake aure a lokacin, na saka kafa na shure y'ayan dake kallona su kirayeni *MAMA*, ya kara doke yaron dake zama ya dora kansa saman cinyata ya ce da ni *UMMU*, na tafi dan kawai fushin zuciyata bayan na kawo rantsuwa na gifta mai girman gaske da zafin kishin da ya rufe min ido wanda ya saka ni dana sani, na juya na tafi bayan na kunce goyonki a bayana ke da na haifa da cikina, ban ko waiwayoki ba na tafiyata da passport dina da visata na yi jiran jirgin da ya zo ya dauki passinger ciki harda ni ina hura hanci rai bace da kudadena da katina na banki na tafi na bar kasar haihuwata"
Sasautawa ta yi sakamakon hawayen da ya fara zubo mata daga gurbin idannuwanta
A hankali ta ci gaba da fadin "sai dai kashh, da na sani, da na kawar da kaina, na hadiye wulakanci da neman fitina da tashin dukiya da irin yanda kudi ke dukan kansa ke saka shi aiwatarwa a gareni na rungumi yan dagwai dagwai dina na rayu da farin ciki, domin kuwa daga bakin lokacin da na sauka, na fara kokarin ciyar da kaina, tufatar da kaina, neman abinda zan yi dan inganta rayuwata duk da tarin takardunna, da dukiyar da na tafi da ita ta gadona da iyayena suka bara min, sai rayuwata ta zamo wata sabuwar rayuwa mai cike da duhu duk inda na ga yaro ko yarinya sai na saki murmushi sai kuma hawaye ya biyo baya
Idan na zo kwontar da hakarkarina wani sa'in idan nonona ya soke ni sai ki fado min a raina
Nakan zabura ni kadai a dakin hotel dina ina jin kamar muryarki kina fadin *"MAMA, ZAN YI FITSARI"*
Na rayu cike da burin zama wata abu, da son goge ku a rayuwata na manta da ku na sake wani auren na haifi wasun
Sai dai me? Ashe na yiwa kaina mugun illah ta hanyar shakuwa da ku,
Makwoncinmu daya
A tsakiyarku nake kwanciya inai maku tatsuniya kunna hayewa jikina kuna kokoyi,
Idan kukai fada nakan ji hankalina ya tashi, zan saka ku shirya ta hanyar nuna maku ilar abin
Na saka shakuwa mai tsanani a tsakanina da ku, da yayanku har ya kasance na zabi kulawa da yara a matsayin karatuna"
Sosai take hawaye hakan ya saka ta saka hannayenta ta toshe bakinta dan kuka take son yi sosai

Dayyabu kansa da yake mai saurin hawaye ne idannuwansa sun cika da kwalla, hakama sauran du hawayen suke zubarwa ciki kuwa Harda Najeeba dake hango duk abubuwan da take fada a zahiri kamar a lokacin komai ke faruwa da rayuwarsu

Mikewa ta yi da sauri ta juya da nufin tafiya, domin ita dai da bakinta ba zata iya furta masu dalilin fushinta ba

Karron da ta ci da shi ne ya sakata kokarin zubewa
Sai dai bai bata damar hakan ba ta hanyar tareta sosai da hannunsa kafin ya maidota dakin da kyau kusa da yaran ya aniya zaunar da ita yana kallonta a sanyaye ya ce...
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

46

A sanyaye ABIH ya ce" ina zaki je bayan ina jiran wannan ranar shekara da shekaru dan na baiwa Najeeba amsar tambayarta wace du sauran yan uwanta ina iya basu amsa kai tsaye na dalilin da iyayensu suka bar gidana aman ita na kasa bata amsar?"

A tsorace take kallonsa, bakinta na rawa ta ce" amsar? Wace amsar kake tunanin zaka iya fada masu?"
Chapter 88 · 0% Book details