← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 138

Sashe 9

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya surbi lipton din da aka hada masa mai dauke da lemun tsami da na.a na.a sai turiri da kanshi yake kafin ya kale shi

A hankali ya ce" kana nufin na manta, na yi kamar ba'a yi ba?

Da sauri DAYABU ya gyada kansa ya ce" mun mata fada sosai, ita da kanta ta yi nadama, tana kuma bada hakuri sosai

Bakinsa da ya dan leko dan shan lipton din ya dan tabe ya yi dan murmushi sai da ya jima sannan cikin magana kasa kasa sosai da ba dan yana sauraronsa sosai ba da ba zai ji ya ce" to ta zo ta duka ta baiwa Zinariya hakuri

Kallonsa DAYABU yake, lokaci daya kuma yana tunanin maganar , yana shirin yin wata maganar wayarsa ta shiga vibrating a aljihunsa

Da sauri ya saka hannunsa ya lalubo ya fitar yana duba wanda ya yi kiran

Gannin sunnan abokinsa ne ya saka shi dagawa

Abinda ya fada ne ya saka shi zabura ya tsaya, a tsorace ya ce" what? Yaushe? Ita da wa? Me ta masa? Ina take?

Dukan tambayoyin nan a tare ya jero su kuma hankalinsa tashe hakan ya saka SHAHEED kafeshi da idannuwansa masu kalar na zaki yana kallonsa

Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une ya fada hankalinsa tashe yana fadin" gani nan tafe

Da sauri ya kashe kiran ya juyo wajen SHAHEED dake dubansa da duba irin na tambayar meye

Hankalinsa tashe ya ce" NANANAJJEEBA ce , sukai fada da wani ya daketa a ciki a wajen sports, yanzu haka dai an tafi asibiti da ita a summe

Irin duban da ya yi masa , ba tare da ya nuna alamun zai tanka ko zai tayar da hankalinsa a kan lamarin NAJEEBAR ba ya saka DAYABU dubansa da duba irin na haba dan uwa

Dan zamewa ya yi ya zauna yana kallonsa ya ce" haba SHAHEED maimakun ka zabura ka tashi ka bada umarnin a fitar da motar sirri a ja mu je ka ga yar uwarka sai ka yi min duba irin na tamkar an daki makiyiyarka ko tankawa ba zaka yi ba?

Duban da yake masa dai ne bai daina ba, hakan ya sa DAYABU mikewa ya kara kallonsa ya girgiza kansa a hankali ya ce" da hakuri, da kawar da kai, da adalci aka san saraki, sannan basa bambanci a kan kowa, sukan talabi mai ji da marar ji, sukan yi yafiya a kan kowa
Sasautawa ya yi ya ce" ban san me yasa taurinka ya tsaurara a kan yar uwarka ba

Sada kansa ya yi ya ce" Allah ya huci zuciyar sarkina, a huta lafiya

Yana gama fada ya juya da mugun sauri har kamar ya kifa ya fice daga fallon wanda dogarai ke tsaitsaye a kofa sunna gannin fitowarsa suka shiga yi masa fatan alkhairi da adu'ar sauka lafiya

Sai da ya ga tafiarsa sannan ya lumshe idannuwansa, tun da ya lumshe bai kuma budewa ba sai ajiyar zuciya da yake saukewa a hankali ya afka duniyar tunani

A firgice ya karasa asibitin
Sai dai abinda ya bashi mamaki ya kuma dakatar da shi kafin ya shige shine gannin docter Jibril da kuma mala'ika wato baban sojan da NAJEEBA ta baiwa banzar number a hanyarta na dawowa sunna tsaye kowane na muzurai

Ganninsa ya saka su saurin tarbo shi sunna kokarin rige rigen gaishe shi

Fuska hade sojan ya ce" ai na hana kowa shiga sai na kusa da ita, ta farka kuma wanda ya daketan yana hannunmu ko uban waye ubansa sai ya amsa laifinsa na dukan matana!

Doctern ya kale shi da sauri da mamakin matarsa kuma?

Shima a matsayinsa na docter ya matso ya ce" barka da karasowa yaya, Alhamdulilah ana kawota na saka manyan docters abokannan aikinmu sun yi mata dukan kulawar da ya dace
Yanzu haka maganar da nake maka ta farfado cikin hankalinta, sakamakon dukan ya mata a cikinta wanda take nisawa kuwa mun saka a yi mata dukan gwaje gwaje, ka san dare ya yi du an tashi da aikin gwaje gwaje aman da yake asibitin tamu ce ita kuwa matar docter ce ya saka har gadonta aka ringa turo kayan aiki ana aunata yanzu haka dai ana iya tafia da ita gida dan ta fada min bata son kwana a asibiti bata san irin halin da yan uwanta zasu kasance ba ya sa na bada damar a tafi da ita gida ko mu bada sabuwar ambulance a kaita har kifar dakinta

Wata uwar harara sojan ya watsa masa
Shima ya yi masa wani kallo irin na shiga gabankan nan

Murmushi DAYABU ya yi yana kallonsu daya bayan dayan kafin a hankali ya ce" Allah ya saka da alkhairi

Ba'a hana shi shiga ba domin docter na tare da shi
Sunna shiga ya karasa da sauri wajen bed din da take kwonce idannuwanta lumshe gashin idon da ta saka sun yi mata luf luf sun kara girman idannuwan nata
Lebenta kuwa du azabar da ta sha yana dauke da kalarsa na pink color iya na kasan na saman kuwa da dan duhunsa

Karasawa ya yi da sauri yana yaye abin rufar da aka rufa mata har daidai kirjinta yana talabota

Nan danan tabararta ta tashi, shagwabarta ta motsa ta langwabe masa ta saki kukan shagwaba tana kara langwabe masa
Cikin zazakar muryarta take fadin" ya, cikina, a cikina ya dakeni bayan shine da laifi haka kawai ya taba min cikina da hannunsa dan na mare shi ya dakan kafarsa a cikina

A hankali ya kara riketa ya ce" NAJEEBA, sannu, sannu kin ji?

Kuma langwabewa ta yi tana wani irin far da idannuwanta ta ce" ba zan iya yafe masa ba

Kansa yake gyadawa kafin ya bata amsa muryar sojan nan ta daki kunnayensu yana fadin" ni kaina ba zan iya yafe masa ba tunda ya taba min kafiarki, ashema shine marar gaskiyan? Ya dauka jikin ki abin banza ne da kowani banza zai iya tabawa?

Likitan ya kale shi da sauri, sai ya girgiza kansa ya juyo yana kallonta
Har kasan zuciyarsa yake jin kishinta sannan baya so ko da wasa ace tana son wani fiye da shi
Shifa sonta yake kuma ba son a watse ba
Gannin hankalinta ba a kwonce ba ya saka shi yin hakuri ya shanye kishinsa ya kara dudubata ya rubuta magungunnan da zasu kara kwontar mata da ciwon cikin da take ji ya fita da sauri ya bada a amso masa a cikin asibitin kafin ya zo da kansa su kamata da likita daya su dorata kan gadon marar lafia na turawa a tura gadon har wajen ambulance aka daga aka sakata dan tsabar gata ba dan bata iya tafia ba

Sai da ta ga da gaske ciki aka sakata ya saka ta mike zaune tana yatsina fuskarta ta kalli yayanta dake ta aikin jera mata sannu hankalinsa a matukar tashe

A hankali ta ce" ya, da sauki fa ni kar a kaini a cikin ambulance din nan hankalin Abih ya tashi, duda yanzu ya tsane mu

Murmushi ya yi ya kamata ta sauko daga bayan a hankali yana rike da ita suka karasa wajen motarsa ya buda baya ya sakata sai kokarin riketa suke son yi shi kuwa yana tarewa ta kwonta a bayan sannan ya juya ya amshi magungunnan da aka kawo

Kudi ya ciro a aljihunsa masu yawa ya mikawa likitan

Da mamaki ya girgiza kansa ya ce sam shi ba zai karba ba

DAYABU ya dube shi da kallo irin na yana son ya fahimce shi ya ce" ka yi hakuri, ni ina matsayin tamkar uba ne a wajenta
Da sanina, ba zan yarda wani ya yi dawainiya da lafiar kanwata wace na raina bayan na san ba'ai maku baiko ba
Alhamdulilah in dai inada rufin asiri zan yi iya yina a kan rayuwar kanaina
Ba mayar da kyauta ko kyautatawarka na yi ba
Ba raina maka na yi ba
Hasalima na ji dadin irin kulawar da kuka bata baki daya
Sai dai ka sani hidimar tsakaninku na soyayarku daban wanda ko shi da zata ji maganana ba zata amshi kudin saurayinta ba har sai ya zama miji a gareta
Sai dai zamani ya zo mana da abubuwa daban daban, a yanzu dan saurayi na yiwa budurwarsa hidima ba wani abin bane, hasalima shi ke kara aminci tsakaninsu
Sai dai ba zai kai har fannin lafiarta ko cimar da zara ci ba
Ka yi hakuri ka amshi wannan a je a cike dukan abinda ya dace a cike

Murmushi sojan nan ya yi da jin dadin abin a ganninsa an wulakanta likitan da ya bi ya kanainaye masa waje run dazu ya ce" aa yayanmu, ai kawai ka mayar da kudadenka, shima ba shi zai biya ba, wanda ya daketa shi zai biya komai dan shine da laifi shi ya fara shiga huruminta har ta mare shi

Ita dai idannuwanta ta lumshe tana jin haushin ubanda ya fadawa malaikan nan cewa tana asibiti
Lale ta fara yarda cewa an saka mata ido a garin nan
Idannuwanta ta kuma budewa ta kalle shi
Bakinta ta tabe a ranta ta ayanna" anya kuwa yana sallah? Yo sam ba annuri a tatare da fuskarsa sai duhu da warin baki!

Jin haka ya sa shima likitan sauke ajiyar zuciya domin shi dai ba zai karbi kudin nan a gabanta ba, haba shi da yake so ya yi mata wanka da kudi ta yanda sai shi

Shima sojan murmushin da yake yi yana ayanna ina zan yarda ka yi bajinta ka biya bayan na zo ne na rufe baki daya bakin yan gidansu da shagun? Ai zan saki bakin aljihunna na wankesu da yayan banki ta yanda zasu miko min yar koda ba fatiya na je na kara buda rigar nan nata na kali na cikin rigar nan dake hararena da kyau

Salama DAYABU ya yi masu bayan ya yiwa sauran likitocin da kuma masu tsaron kofar urgence din alkhairi wanda suka ji dadi sosai harma suka shiga bayanin ko shi waye cewar yan uwan sarki ne fa, kowa kuma ya san waye sarkin wanda idan ka samu kadaicewa da shi ka warke da izinin Allah
Chapter 9 · 0% Book details