← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 138

Sashe 36

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dubansa ya kai wajen amintacensa
Ba zai iya tura shi ya kaita bangaren Anmy a irin wannan lokacin ba, idan kuwa shine zai kaita dole ya bi ta hanyar da zata sada shi da fallon Zinariya sannan ya bi ta fallonsa ya bi ta doguwar hanyar da zata kaishi bangaren Anmy din ba tare da ya bi ta hanyar da kowa kan iya ganninsa

Hannunsa daya ya mika ya daukota
Dauka irin na yara ya yi mata a hannayensa bai rufe motar ba bai masa magana ba ya juya ya nufi bangaren Zinariyar

A daidai lokacin tana zaune a fallo ita da yayarta sunna cin abincin da ta saka aka masu wato gasashen naman rago ya ji kayan hadi sai turiri yake sunna ci sunna hirarsu hankali kwonce

Kasancewar hanyar ta sirri ce, ba'ai masa iso ko ta saka ran zai iya zuwa a irin wannan lokacin

Jin karar bude wajen ya sakasu waigawa a tare

Da yake kofar mai dauke da dan haske ne sai suka ga yannayin tsayi da fadinsa hakan ya sa da sauri suka mike yayar nata ta warci hijab dinta ta saka haka itama

Kofar ya turo da kafarsa
Kasancewar tafiar nan tamkar ta giwa a jinninsa ne ko yanzu ba sauri yake ba a hankali yake tafia da uta a hannunsa

Gaba dayansu suka zube kansu a kasa har sunna hada baki wajen furta" barka da war haka mai martaba

Bai iya amsawa ba, da kansa kawai ya dan gyada kai,
Jin kamar zai wuce da kyakyawan takalminsa ne ya saka Zinariya dago kanta a hankali

Gabanta ne ya kwonci kwonci ya yi faduwar da ita kanta ta kusa zubewa daga duken da take

Ya shige ciki hakan ya sa ta kara zabura ta mike

Da sauri yayar tata ta riko hannunta ta ce" ina zaki je?

Warve hannun nata ta yi ta ce" baki ga waye a hannunsa ba? Yarinyar nan da nake fada maki nace da ita yar talakawa ta mari fuskana itace a hannun mijina mai daraja me ya kawota bangarenmu? Me ya hadata da shi? Me ya sa ya dauketa da hannayensa masu matukar daraja da kima a duniya baki daya?

Aman idan kika je me kike son yi bayan kin san sarkinki ne shi kuma kanwarsa ce? Ta fada tana son tareta

Hannayenta ta kuma warcewa tana kallonta ido cikin ido ta ce" shi ya sa kika kasa gagarar kishiya! Koda kare jinni biri jinni ni Zinariya sai na kafa tarihin zama daga ni sai mijina
Babu shegiyar da ta isa ta hau hannunsa haka ya bi ta falona na barta da hankalinta da ranta koda kuwa zan yi yawo tsirara ne!

Tana gama fada ta juya da sauri tana bin bayansa, yayar tata kuwa ta yi gagawar daykar waya dan kiran mamansu

Tun da ya shigo Anky dake zaune da su Zahrau suka zabura sunna kallonsa

Da sauri Anmy ta karasa dan itace kawai zata iya tarbansa

Har hade maganarta take wajen fadin" sususubahannalah, Shaheed me ke damunta kar dai ciwon zuciyar ya yi tsanani

Irin yanda ta rikice yake kallo, da ta san shagalinta ta je ba asibiti ba zata rikice haka?

Anmy ta ce" likitan ya yi kurana yake ce min da sauki aman zata koma ya kara bincikata, wai summa ta yi ne Shaheed?

Ta fada tana rungumota jikinta a lokacin da ya ajiyeta saman kujera

Tsayawa ya yi yana kallonta, yayaunta kuwa du suka duduka kansu sunna faman yi masa barka da warhaka

Bai baiwa Anmy amsa ba ya juya a hankali zai tafi

Har ya kusan fita ya juyo, muryarsa a hade ya ce" ZAHRAU, ki shirya aurenki karshen watan nan idan Allah ya aminta

Yana gama fada ya juya ya fice a dakin

Kicibis dukai da ZINARIYA wace ta labe dan jin abinda ya hada shi da ita har ya rungumota haka, sam bata ji takun fitowarsa ba

Bai kulata ba ya fice ya barta kai sade tana fadin" a huta lafia mai damagaram

Yana fita suka rikice, kan mai dankarawa da gudu ya daukowa Anmy ruwa, sai mai kara rungumarta

Da gudu Anmy ta yi ciki dan kiran likitansu ,
Tana shiga Najeeba ta ja dogon numfashi

Idannuwanta a rintse tana jikin Zagrau bata bude ba ta furta" *BAN TABA TSANAR HALITA IRIN YANDA NA TSANEKA BA! NA RANTSE SAI NA RAMA A KANKA KO A KAN ALADEN MATARKA!*

a tsorace suke kallonta, Zahrau ta dora hannunta gefen fuskarta a hankali ta buda bakinta zata yi magana sai ga Anmy ta fito da wayar a kunnenta tana fadin"

...............😓[1/30, 11:58 AM] Ummu Sadeeq: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

2 1

A sume ne take docter ki zo yanzun

Da sauri ummulkhair ta ce" Anmy ta farfado

Anmy ta ajiye wayar tana karasowa itama ta duka ta kamo Najeeba ta rungumeta a jikinta tana fadin" Najeena, meye? Jikin ne ya saka kika suma? Likitan ya nuna min da sauki kar na damu kuma yayanku ya shigo da ke a summe meye ne?

Najeeba kam irin yanda zuciyarta ke kunna bata da bukatar komai sai na kadaicewa

Ga jikinta du a jike yake gashi zuciyarta na yi mata zafi tamkar ta ciji babu

Anky, zan kwanta

Tsurawa fuskarta ido Anmy ta yi na dan lokaci kafin ta shiga taba jikar jikinta da cirar hannun rigarta sannan ba alkyaba a tare da ita ba hijab dinta

Tana kallonta ta ce" me ya fari da ke kika dawo min ba a yanda kika fita ba?

Najeeba ta ja numfashinta da kyar ta ce" Anmy, athsmana ne ya tashi,

Anmy ta kara jin tausayin yarinyar fiye da sauran yan uwanta
Kamata suka yi suka nufi dakinsu da ita

Saman bed din suka shinfideta Anmy na ta shafa kanta tana kallonta

A hankali ta ce" Allah ya baki lafia bara na je na fadawa yaya cewar da sauki

Mikewa ta yi ta juya ta fita

Tana fita da sauri Zahrau ta riko hannayenta ta ce" me ya faru da ke? Me ya maki? Waye kika tsana? Me aka yi?

Gaba dayansu hankalinsu a tashe yake su duka

Najeeba ta cije lebenta na kasa tana jin wani irin kunci a zuciyarta

Muryarta a kausashe ta ce" SHAHEED NE, Shaheed ne ya min wankan janaba

Da karfi suka kusan fadi a tare kan me cewa" quoi? (What?), sai me cewa Me?

Idannuwansu a zazare a waje cike da tsoron abinda ta fada din

A hankali ta ja hancinta ta tashi ta dan jingina tana kallonsu, sai da ta kuma lumshe idannuwanta ta bude , a hankali ta kabarta masu abinda ya faru

Kwarai sun ji tausayinta sai dai Zahrau na budar bakinta sai ta ce" Najeeba, rashin jin maganarki ke jaza maki fitina
Ke da ya sauke ki ya ce ki je ku hadu a lokaci me ya hana ki zuwa ki yi jiransa?

Ummulkhair ta ce" bama wannan ba, tsakani da Allah ciwon zuciyar nan dama karya ne Najeeba? Ke kam bakya jin magana ban san me ke kwakwaluwarki ba

Ummukulsum ta ce" NAJEEBA, kudin da ya baki kika watsar? Sannan kika yi fitsari a gabansa a gaban yaronsa? Me kike so ya dauke ki? Najeeba ko bai yi tunanin baki da kamun kai ba ai kema kin san baki da shi ko?

Najeeba ta lumshe idannuwanta a hankali ta ce" eyah, me zai hanna ku taru ku min dukan tsiya dan na taba dan gwal?
Dagowa ta yi ta firfito da idannuwanta ta dauki hannunta ta nuna kanta ta ce" na rantse da wanda raina ke hannunsa bashi da mutunci, kuma bai sani bane irin yanda ya yi ikirarin ya tsane ni na fi shi tsanarsa, zan nunna masa a aikace, ba dai ni Najeeba ba? Nice ya kwontar jikin maciji?

Kallon Ummukulsum ta yi ta ce" ji wani kililin kasau da ita kamar ta Allah ke nan kyankyaso ne ya shiga rigarki kika cire rigar da wasu kannanun nonuwanki kina ihu a gaban kannenki,

Ummukulsum ta ce" ai dai ni ban yi fitsari a gaban mazan da ba maharamaina ba

Ta buda baki zata rama Zahrau ta ce" kun ga ku saurara mu ji da abinda ya sha mana kai mana haba da Allah, ku kawai baku da aiki sai fitina? Maganar zaki rama bata taso ba! Ki rama me? Ta yaya? Ki bari ki mutu maza su kaiki ba mata ba dan walahi da zaki ji tarihin bawan Allahn nan sai jinninki ya hau, baki yi mamakin yanda aka yi yake damkar maciji da hannunsa katon maciji ba wani jariri ba? Ke ki kiyayi maza walahi bana son fitinar da zata saka ransa ya bace ya batar da ke Najeeba! Ke kin san albarkar anmy kike ci, kin san albarkar su Abih kike ci, aman kina da izgili a abinda ya shafe shi, ke idan ba rigima ba ina ke ina tsayawa kafada da kafada da shi? Ai ko ba sarautar dake yawo a jinnin jikinsa ba shi din yayanki ne, yaya aka yi kike girmama yaya DAYABU ne? Bale ko a cikin mutane akan yi wani halayensa daban!
Najeeba mutumen nan adali ne, aman kuma inaai tabatar maki ya fi macijin nan da ya sumar da ke balaki idan kika tankwalo hakan zaki samu domin mu yan uwanki ba abinfa zamu iya yi maki NAJEEBA!

NAJEEBA dake kallonta ta yi murmushi tana dan girgiza kanta, a hankali ta dan yi atishawa tana dafe daidai kirjinta ta ce" tabas shi din wani ne na yarda, shi din ya girme ni kuma na yarda
Dubansu ta yi ta yi murmushi ta ce" sai dai ni din kamar yanda ya ce ne *MAGE ce ni mai kwonciyar d'aukan rai* zan dauki ransa a lokacin da bai ji ba bai gani ba bai san da zuwan lamarin ba
Tunda ya yi saken na kasance mace......zan nuna masa irin girman karfina a kansa! Shi da takobi take suka, ni kuwa da kalamai nake suka idan na tashi harbi da tawa kibiyar nakan harbi wajen da baya jin magani!
Chapter 36 · 0% Book details