← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 138

Sashe 58

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta nufi bangaren ZINARIA domin ta san wacece a halin kishi dan irin haukan da ta zuba a auren bintu ko a gari fadi ake ita ta kasheta!, ta yi niyar zata fara fada mata maganar da sarakuwarta ke shirin aikata mata idan ya so sai ta zama makiyarsu ta gasken gaske

Anmy ta kara kallon Najeeba kafin ta kuma sada kanta, a sanyaye ta ce" yaya, ina so cikin su biyun nan da suka kawo, a hada auren SHAHEED da daya

Wata wawuyar ajiyar zuciya ce Najeeba ta saki wace ta saka Anmy sauke dubanta jiki a mace

Ajuyar zuciyar ta kuma saki tana kamo hannun Anmy, irin zata yi convincing dinta ta ce" Anmy, Alhamdulilah, dama Anmy Ummulkhair ce bata da saurayi, Anmy kin ga ni ai na maki maganar Huzaifa ga kuma likita, a cikinsu koma wa kika zabar min na yarda zan zauna da shi Anmyna

Jikin Ummulkhair har rawa yake a lokacin da ta ji abinda Najeeba ke fada
Hakan ya saka baki daya ta yi kamar zata fashe da kuka ta ce" Eyah Najeeba, Eyah Najeeba, wace irin magana kike haka bayan kin san cewa kaf cikinmu na fi ku rauni? Ni a gidan sarauta? Ko sujada na kai ina fadawa Allah ya hada ni da kunu huce in sha ka domin ina matukar tsoron ringingimun yau da kulun , Najeeba ke kuwa kin sha fada ke ai su kike so ko?

Najeeba ta yi gagawar fadin" ke, ki rufa min asiri, ki rufa min asiri da wata fitinar gwara na san salar gawata ake yi, bayan wannan ni Huzaifa nake so, yanzun nan tafiar da ya yi mun tsayar da maganar zan kawo maganar gida ne fa

DAYABU dake kallon su da matsancin mamak8n shin sun manta cewar sarki na zaune ya daka masu tsawar da ta saka du suka zube jikin Anmy

Ransa bace ya ce" lale baku da kunya da kawaici
Gardama kuke a kan maganar da aka yi ko me kuke nufi da maganarku?

Ku tashi ku bacewa mutane a wajen nan, kuma magana ta riga ta yita a yanzu yanzu zamu yanke wace ta dace idan ya so in an yi auren dan Allah ta kashe kanta!

Hankalinsu du a tashe suka shiga mikewa , du sai suka shiga gware da junna tsabar rikicewar hanyar da zasu bi

Sunna shiga daki Najeeba ta karasa da sauri ta rukunkume Ummulkhair ta saki kuka tana fadin" ashe ba zaki ringa daukan girma irin na aunty zahrau ba? Ashe kin manta irin tsanar da wannan bawan Allahn ya min har zaki nuna kina jin tsoron zaman aure da shi? Ummu, a titi ya min wanka da ruwan sanyi cewar na dauki niyar yin wankan jannaba shin karuwa ce ni? Kaf cikin mu ku kun fi kowa sannin ko rigima ta kawo mu fada ya kama hararana tamkar zai kashe ni da idannuwansa da mugun kallo
Ummu, kin fi kowa sannin a duniyata ina jiran damar da zan rama irin cin wulakancin da jifana da mugayen magangannun da ya yi nake nema ko? Kafin aunty zahra ta bar gariin nan sai da ta sakani rantsuwar fita a harkar matarsa
Ummu, me na mata? Du idan mun hadu ko ta zartar da yawu ko ta kirayeni banza talaka
Ummu wace irin rayuwa kike son saka yar kanwarki a ciki bayan kin san a duniya *SULTAN SHAHEED MAKIYINA NE?*

UMMULKHAIR ta yi gagawar rufe mata baki ta kara janta ciki ta dungurar da ita saman kujera
Tana kallonta ta ce" ohk laifi na yi da na zilewa auren mutumen da ya kasance ko hauka nake idan na ji sunnansa nake wartsakewa?
Kaf cikin namu waye yake dago kansa ya yi masa duban ido cikin ido a lokacin da kowa ke rawar jiki? Kaf cikinmu waye ya daga hannu ya wankawa matarsa mari ya kwana lafia bayan nan muka ringa nafilar Allah ya sa kar a sace ki a je a datse hannayen ki?
Najeeba, a gaban Anmy kika nuna mata ke kina da wanda kike so? NAJEEBA yaya kike tunanin zan iya zaman kishi da matar da nake tsoro kamar raina? Kin taba gannin na gaishe da matarsa a tsaye ba tare da na duka ba? Ke kin taba gaisheta tun da kike?
Najeeba ni, ni Ummulkhair auren Sultan SHAHEED? na tabata maki tsoronsa zai saka nima a tardo gawata a ajiye kafinma a sadani da dakinsa
NAJEEBA a kan mema Anmy zata so hadin nan? Me ya sa zata nemi wannan abin bayan mu tsakaninmu da shi ubane sarki ne a wajenmu?
NAJEEBA waye ke bibiyar matar da yake aure? Idanfa wani ne ke kashe masa mata?

Najeeba ta ringa binta da kallo kafin ta ce" idan fa ZINARIA ce ke kashe masa mata?

Da sauri Ummukulsum dake tsaye hannayenta rungume a kirjinta ta matso ta ce" kai, ku yiwa mutane shiru kar garin haukan ku ku yi kokarin kauce hanya! Zato? Zato irin wannan?
Wai da kuke ba ni ba , ba ni ba, an fada maku shi yana da ra'ayin aurenku ne?
Banda masifa, rigima, fitina, tara samari, iya shege me muka iya ne y'ayan mutalab? Ikon Allah ne ke giftowa yana hada mu da na kirki, idan ba wannan ba ku fada min a samarin tsayuwar titin waye ba dan airs ba?

Najeeba ta ringa gyada kanta ta ce" ka ji uwarmu ta yi magana, ke Ummukulsum na rantse kika kuma ce mana yan iska sai na fafala maki mari malama a nan, kuma ba dai sarki ba ? A kai kasuwa, ko ina numfashin karshe aka daura min shi zan mike na murje ido na ce bana so!

Gaba dayansu da mamakinta suka kura mata ido, lale ta cika mutun mai karfin hali,
Yanzu itane ke fadin haka a kan sarki?
Ummulkhair ta ce" aman an fadi ba nauyi, an ji kunya
Na tabata yau Anmy ba zata iya rintsawa ba idan ta ringa tunowa kin nuna kin fi son wani dan daudu a kan yaronta!

Najeeba ta yi shiru jikinta du a mace tana kallonsu idannuwanta suka ciciko da kwallah
A sanyaye ta ce" Ummu, Huzaifan ne dan daudu? Ummu Huzaifa ba dan daudu bane na rantse
Kuma kin ga, ban taba sannin yaro zai juri iya shegena sai da na zauna na ringa masa yana taro ni
Ummu, ina son Huzaifa har raina, ya jima yana fama da ni
Meye laifin Huzaifa?, saurayi tsayaye yaro mai jinni a jika
Ummu, Huzaifa ya iya sangarta ya iya hira ya iya yi min kallo irin na mutun mai daraja
Ummu me ya sa zaki zagar min shi bayan shi zan aura nake so na zama uban y'ayana?
Ummu, kin manta irin namijin da nake so?
Huzaifa du ya hada abubuwan nan Ummu, shine tsakani da Allah dan ki tayar min da hankali zaki zage shi ki ce da shi dan daudu kuma ummu dan kawai na nuna aa ba ni ba sai ki ce na tayarwa da Anmy hankali? Ni yaya kike so na iya yin bacin ne? Ummu aunty Zahrauna kan sadaukar da farin cikinta domina
Na tabata da itane ake magana a kanta, da ba zata taba kawo sunnana kusa ba dan ta san idan na tsani abu na tsane shi, zata amsa ne koda kuwa hakan na nufin karshen numfashinta
Ummu, a hannayenku ta barni ashe ta yi aikin banza shine kuke tayar min da hankali fisabililahi?
Ta karashe wasu irin hawaye na zubowa daga idannuwanta kafin ta juya da gudu ta yi cen ciki

Kafarta ta daga zata bita hankalinta tashe
Da sauri Ummukulsum ta riko hannayen nata
Maidota ta yi kusa da ita kafin ta bata kyakyawar rungumar da ta sakata itama fashewa da kukan tana girgiza kanta ta ce" walahi zan amshi auren nasa koda kuwa matarsa zara kashe ni, ta daina kuka ina sonta ban yo haka dan son kaina ba

Ummukulsum ta ringa sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" zata fito ne, ta yi mana haka dan ta saka mu, mu kwana muna kuka hankulanmu tashe
Barta zata fito ne ummu, aman in sha Allahu rigimar Sultan da mutanen dake tare da shi kaf cikinmu ba mai iyawa sai Najeeba

Shin baki ga tsarin tafiarta ba? Tamkar dawisu haka take tafia cike da takama tana baza albarkatun jikinta ba tare da tana yi da gangan ba

Shin baki ga irin yanda take iya saka idannuwanta cikin nasa ba? Waye yake da wannan kokarin bayan ita din?

Shin baki ga ranar da ta daga hannu ta wankawa Zinaria mari a gabansa ba? Hakan na nufin koda a gabansa ne ba zata taba bari a takata ba!
Tabas tsana, ko na ce wani baban lamari na faruwa tsakaninsu wanda mu kanmu mun kula da irin rashin daidaituwar yannayinsu dake faruwa a tsakaninsu
Aman wannan lamari kam, inaga na Allah ne!

Ummulkhair ta ce" idanfa suka yanke ni ce zan aure shi?

Ummukulsum ta ce" haka Allah ya tsara, koda ke ce zaki je ki rayu da su in sha Allah babu abinda zai same ki face wanda Allah ya kadaro maki!

Baki dayansu shi suka saka gaba a lokacin da suka roke shi shin ya amince su je su fadawa Allah kan zabi biyun nan Allah ya dora su a kan wada ta fi dacewa da shi
Chapter 58 · 0% Book details