← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 138

Sashe 25

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wajen bai cika mutane ba, idan ka ga mutane a wajen tabata irin manyan yan gayun nan ne

Salaya ta shinfida ta gabatar da sallarta a wajen da hijab dinta dake cikin mota
Haka ta yi ta isha ta shafa fatiya

Mikewa ta yi ta adana komai ta dauko shawarmar ta zauna saman daya daga cikin kujerun wajen a lokacin duhu ya shigo sosai ta shiga harba yan kafafuwanta tana bude takardar shawarmar

A hankali ta rike a hannunta tana fadin" Aikin banza! Aikin banza aikin wofi! Shirme shirme shirme kawai! Ta karashe tana murguda bakinta

A hankali ya furta" ke da wa?

Da sauri ta dago dubanta, sai dai bata idasa dagowa sosai ba gabanta ya fadi haka kawai ba tare da ta san dalili ba

Wannan mutumen ne na ranar, wanda ya taimaketa ya fitar da ita
Yauma wani irin turarensa ne ya fara yi mata salama kafin ta sauke dubanta saman jajayen lebunansa
Irin yanda tsarin haliyar jikinsa take kuwa shi ya fi komai bata tsoro
Haka kawai ta ji jikinta na yi mata wani yam yam yam dan irin yanda take gannin idannuwansa da girma ga kwali sai ta ji tsoron kar dai aje aljani ne?
Bata idasa tunanin da take ba ya karasa saman kujerar dake daf da tata ya zauna yana jan dan karamin tsaki a cikin zuciyarsa yana mai dannar kansa cewa ka yi hakuri, ta hanyar nan ne kawai zaka iya cinma burinka! Ka yi hakuri.
a fili kuwa sai ya furta" kema an kona maki zuciyar ne? Ya Allah ban san menya sa mata suke haka ba!

Gaba daya sai ta ji kanta a takure, abincine fa zata ci ya wani sakota gaba, to wai wayema shi? Ina ruwansa da ita ne? Ita dake boyon cin abinci idan ba da yan uwanta bane sai anmy sai abih
Haka kawai wani garjehen kato ya wani shiga yi mata bayanin da bata tambayeshi ba? Yanzu haka da budurwarsa ya yi fada, shirme! Shirme! Aikin banza kawai!

Da yannayin tsiwa ta dube shi ta ce"....
......

Commetn comment na sis

Ina jin dadin comment dinku, karo min zai karan karfin gwuiwa hajiyoyina😌😌
[1/23, 6:57 PM] Ummu Suhan😍: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

15

Da yannayin tsiwar nan ta ce" ka sanni ne?

Kwarai hakan ya bashi mamaki, ya matukar bashi mamaki, shi? Shine yau mace macenma wace ya fi rainawa take furta masa magana haka kai tsaye?

Saurin kawar da hakan ya yi yana kirmiro murmushin da bai yi ba baki daya wunin yau ya miko mata hannu irin su gaisa din nan yana fadin" je suis desoler ( i'm sorry), ban gabatar maki da kaina ba, FARID ELHAJ BASHIR by name, ni dan Abuja ne ina shigowa garin nan ne dan kawowa yayana ziyara Elhaj Muctar Garba mai gold, ni matukin jirgi ne sannan dan kasuwa ne

Du wannan jawaban da ya yi Najeeba ta yi sakalau da abincinta a hannunta tana kallonsa
Tambayar da take yiwa kanta shine, to ita ina ruwanta ko tambayarsa ta yi ne?

A hankali ta bi hannun nasa da ya miko mata yana nufin su gaisa ko me?
Wani sakaran murmushi ta dan sakar masa ta maida hankalinta kan ledarta ta dan duka ta dauke sannan ta mike tsam ta koma kujerar dake nesa da shi ta barshi nan sakaye da hannu baki da hanci bude cike da mamakinta

Wai bata ganninsa sa kyau ne?
Duba da irin shigar da ya yi tau ya yi shiga ne irin ta yaran atajiran nan, ya saka riga da wando na wani mahaukacin yadi wanda koda baka san yadi ba idan ka gansa a idannuwanka zaka gane ba fa na wasan yara bane
Ya dora yar hula a kansa wace ta kara kashe kyansa ta fitar da dogon hancinsa zuwar sannan ta kara masa kima
Rigar ba wata mai budadan hannu bace, dinkin ya kama hannayensa sosai har kana iya gane hannayen nan nasa bafa na wasa bane
Sai ya ringa dan kara kallon kansa a kaikaice kafin ya yi gagawar karyata abinda yake tunani ta hanyar fadawa kansa kalamai kamar haka" ranta ne a bace, shi yasa ta ki baka hannu, idan ba wannan ba yarinyar dake jira a tayata ta karba a guje?

Tuna hakan da ya yi ya saka shi kara baiwa kansa hakuri ya mike cimak ya koma kusa da ita, wannan karon face dinta ya zauna yana dubanta ya ce" i'm sorry plz
Na bata maki rai ne? Nima ina cikin damuwa ne shi yasa kika ga ina yi maki magana haka sannan kamar na taba ganninki

Sai kuma ya dan zaro ido ya ce" oh yes, ke ce, ranar nan na fitar daga stade kun je ke da saurayinki nah?

Tsatsareshi ta yi da ido ga abincinta ta cira ta fara taunawa hakan ya saka ta kasa ci gaba da taunawa sai kawai take kallonsa
Ko maye ne? Abinda ta tambayi kanta
Idan ba raini ba shi a nan bai gane ni ba sai yanzu?
Ta kuma tambayar kanta

Sai da ta juyar da kanta ta labe fuskarta ta karasa taune abin bakinta sannan ta juyo tana dubansa ta ce" aman bawan Allah fisabililahi me na yi maka ne? Ka dai san tunda na baro gidanmu na zo nan kadaicewa nake da bukata kuma shikenan sai ka shiga zayano mon magangannun da ya shafeka? To waima an rubuta a goshina cewa ga NAJEEBA maganin damuwarka ne? Plz ka girma ka je ka iya da matsalar budurwarka haka kawai ka wani matsa min , to ni ba ni ka ganni a inda kake tunanin ka ganni ba

Tana gama fada ta mike ta bara masa ledar a nan ta yi gaba da sauri ta karasa wajen motarta tana jan tsaki ta fada ta rufe ta tayar ta warceta da gudu gudu ra bar wajen

Zuwa wannan lokacin har sai da ya talabi habarsa dan mamaki
Wato ita bata tsoro ga tashen iskanci ko? Bata tsoron ko shi wani mugu ne ya fafalawa fuskar nan tata mari ta zo ta saka abin idannuwan nan dake mayar da ita tamkar wata aljannah ta tata masa rashin mutunci ta tafi

Kansa ya girgiza ya kai dubansa wajen ledar

Dauka ya yi ya buda ya ciro abinda ke ciki

Jujuya abin ya ringa yi kafin a fili ya furta" da na halal din ko da na haram din aka siye ku?

Mayarwa ya yi ya ajiye a nan ya mike yana tafe kamar mai jin tsoron taka kasar ya bi ta cikin duhun da ya ratso ya shigo wajen yana mai ayanna" sanu sanu dai bata hanna zuwa, zaki yi bayanni ne daga bakin lokacin da na kama ki da laifinki, na rantse maki sai na fitar da ke waje zan hukunta ki a wajen da ba wada zan iya kallo na daga maki kafa marar mutunci kawai!

.......................................

Hotunnan y'an matan da aka turo masa ne yake bi ta compte professional dinsa

A gajiye yake tilis, ga kallon hotunnan da yake yana son a yau a yau din nan sai ya fitar da yarinyar da za'a kawo masa a matsayin mace ta biyu gidansa
Yana son kara auren nan ba yau ba sai gashi da banzarsa ta buda masa hanyar yi

Ya yi hayaniya mai yawan gaske hakan ya hadasa masa da gajiya mai yawa sai kawai ya dawo juyawa a saman bed din yana sauke ajiyar zuciya

Shi kam a kan hitunnan wasu yan mata uku ya tsaya
Ba dan komai sai dan irin shigarsu ta kamala sannan iyayensu mutanen kirki ne
Biyu y'ayan hausawa ne sak, dayan ce bafilatana

Turawa wanda ya turo masa ya yi, kafin ya mayar da kansa har ya turo masa da message kamar haka" *Su duka ukun uban gidana?*

Tambayar ya kurawa ido, su duka ukun? Sai ya ji wani abu na ce masa me zai hana ka dauke su su ukun? Idan ka yi hakan ka gama cikewa sai ka koma gefe ka karbi salon kowace

Bai bashi amsa da gagawa ba, shi kuwa ya yi ta jiran amsar karshe shima ya bar wayar a kunne ya kasa kashewa dan gudun ya sauka a je ya turo amsar

bayan ya gama salar asubah ya dawo bangarensa ya kwonta yana duba agogon dakinsa ya lumshe idannuwansa

Irin yanda zinariya ke ta tsatsareshi da ido aman ta kasa tambayarsa abinda ta masa ke bashi mamaki
Me ke damun kwakwaluwar yarinyar?
Shin sarautar ce ko sakarci ne?
Yakan cika da mamakin wasu abubuwan nata
Tabas shi mutun ne mai son sauki a rayuwarsa bai san dalilin da ya saka mutane da yawa ke tunanin ya cika son zafi ciki kuwa harda abokiyar rayuwarsa wace ya dace ta fi kowa sanninsa da fadin halayansa

Yana so ace matarsa ta san cewa shi mutun ne mai son shakuwa da mace
Yana son ya gabatar da rayuwar aure irin yanda ma'aiki ya koyar
Yana so koda bai cika komai daidai hakan ba ya kwatanta
Ya so ace shi din mutun ne marar nauyi a kansa, da ya rantse abinda zai hana shi zuwa ga matarsa lalle baba abu ne
Sun yi auren biyaya ga iyayensu da zinariya, ya sameta a matsayin cikakiyar budurwa, sai dai a kulun abinda yake nema ido rufe ya rasa shine kasancewarta irin matar da yake so
Yana so idan ya fita ya bayar da umarni idan yana daka a umarceshi cikin kissar da shi kansa ba zai gane umartarsa aka yi ba
Yana so tsakaninsa da matarsa idan da ido ta yi bayani ya fasara abinda take nufi koda a cikin duban mutane ne
Yana so tsakaninsa da matarsa ace idan akoy wani abu mai sunna kirari to fa ta yi shi ne a lokacin da idan ta yi shi zai kara kaimin faranta mata ya farantawa kansa ya lula da su a cikin duniya mai dadin gaske
Sai kawai aka samu matsala tasa matar takan kwashi kirari ne kamar wata jakadiyarsa a duk lokacin da suka hadu
Shin sai ya koya mata ne ko sai ya karo auren ta ga yanda wata zata wakanar sannan itama ta dauki hannu?
Chapter 25 · 0% Book details