← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 138

Sashe 23

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su duka suka amsa mata da nutsuwa kafin du su tashi su tafi bayan sun gama yin salama da ita

.............................................

Kansa a sade yake gaban mahaifiyarsa
Kunyarta ne ya ji ta lulube masa zuciya sai wani irin takaicin zinaria da haushinta da mamakin ashe har yanzu bata da hankali? Yarinta ce ko raini ne ya shiga tsakaninsa da ita?

Cikin tausasawa Anmy ta kara tambayarsa kamar haka" *SHAHEED, SHIN ZAKA IYA FADA MIN KAMSHIN TURARAN WA MATARKA TA JI A JIKINKA KAFIN ZARGI YA SHIGA TSAKANINKA DA ITA DA NI KAINA MAHAIFIYARKA KO BA ZAKA IYA BANI AMSA BA?*

Me zai ce mata? Ce mata zai yi ga mai turaran ta tambaye shi me ya kai turaranta jikinsa? Ko fada mata zai yi ga abinda ya kawo turaran nata jikinsa ta titsiye shi kan a kan me?
Aman yana tunanin ya yi girman da zai iya tara mata hudu shine zinaria ta masa gangancin kawo irin maganar nan kunnen mahaifiyarsa? Ta kuwa san irin yanda yake kiyaye lamarin mamansa shine ita zata masa wannan shirmen?

Anmy ta shiga girgiza kanta a hankali sannan ta ce"
[1/20, 7:40 PM] Ummu Suhan😍: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

14

Bude matan da aka yi ya sakata saka kafarta da bismillah ta shiga shagon

Sai dai bata kai ga idasa shiga ba ta ji wata murya sama sama ana tafa hannu aka ce" oyah, gata fa ta shigo, karuwar yar dake zuwa nan ta amshe kudadenku kuma ta raba ku da mazajenku

Da sauri ta dube ta
Duba irin na tsanaki nan ta tabatarwa kanta cewa wannan itane matar Ambasador din

Ko karya na yi maki? Idan karya na yi maki ai sai ki musa ko kunya bakya ji yarinya karama da ke kin mayar da kanki karuwa kina bibiyar mazajenmu

Yarinyar dake hannunta ta kara rikewa dan kar ta fadi tana kallon matar

Zata iya rantsewa idan auren kauye ne matar nan tana iya nakudota ta haifota ba tare da an talafa mata ba
Gata ta wani zama wata kantamemiyar mace ba wani waje dake rabe ko'ina a hade yake
Gaske, shi ya sa mijinta ke haukacewa ko wani dan karamin tabara nata

Fuskarta ta dan yatsine ta juya a hankali ta nufi ciki

Mayafinta ta warto tana fadin" ke dan ubanki ki tsaya min a nan dan ko uban wa nake magana da shi bai isa shigewa ba sai na gama! Zuwa na yi ki fada min karuwancin naki a kan mijina zai tsaya ne ko me?

Da sauri Najeeba ta karasa saka kanwarta ciki ta zaunar da ita ta mika mata wayarta wace bata da wani code ta fito tana janyo kofar cikin

Mai aikinta babar ce ke ta raraba ido hannayenta saman kanta , fadi take" Hajia dama abinda ya kawo ki kennan? Ki yiwa girman Allah ki yi tafiarki kar ki rikita mana wajen aikinmu dan mu aiki muka fito

Wata bagwariya da ake dinkawa atash kuwa ta yi saurin fadin" jesus, wannan yalinya da gaske ne?

NAJEEBA ta dubeta, ta kuma kallon mutanen cikin shagon

Kafadunta ta daga ta karasa da karfi ta warce mayafinta dake hannun matar ta ce" eh haka ne, ni karuwarsa ne, nice nan mai haukata maki miji ya je gida yana ihun kiran sunnan NAJEEBA NAJEEBA NAJEEBA a tare da ke!

Dan ubanki karya kike, ke nan har mace ce? Ina wajen da zai rike har ya haukata shi? Ta fada a zabure

Najeeba ta yi far da idannuwanta ta ce" meye kuwa ba zai rike ya kasa zaburar da shi ba tunda har yake iya banbance sama da kasa, teba da mazaunai? Ke ko jiya a wajena ya raba dare mijinki!

Tabas a jiyan kuwa ya raba daren domin shi dama mutun ne mai yawan yawace yawace ga cika dare a waje, ga uwa uba a jiyan ya nemi Najeebar kamar me dan ya jima wajen shagonta bai sameta

Najeeba ta dora da fadin" kin ga kuwa idan har baka iya kiwo ba, baka iya daure akuyarka ba dole ta fita waje ta ci! Hakan na nufin ba'a karuwa daya shima mijin naki namijin karuwi ne

Abin da ake busar da gashi na kusa da ita ta kinkima wanda ke jikin abin jonawa a jone ta shanmaci NAJEEBA ta tafka mata shi daga gefenta wanda hakan ya sakata yin tangal tangal ta je ta daki garun dake kusa da ita

Ta saurin balaki ta sabule takalman kafarta ta rike guda a hannunta da yake mai dan tsini ne kadan

Da gudu ta karasa ta shigi matarnan da wani irin masifa tana doka mata du inda hannunta ya kai

Kawayenta da suka rakota basu shiga fadan ba sai rabawa da suke, wanda hakan ya fi yiwa Najeeba ciwo gannin mace kusan hudu ta ririketa

Su dukansu kallonsu take , sai a lokacin ta gama fahimtar tare suke mace kusan shida dan hudun sun riketa sunna bata hakuri biyun kuwa sun rike Hajiar sunna tausarta sunna fadin ya isa hakannan ta bari haka

NAJEEBA ta ringa kokowar kwacewa aman du sun saka mundula mundulan hannayensu sun ririketa hakan ya sakata sakin wani irin kukan takaici
A rayuwarta ta tsani tana fada a riketa, ta fi so a barta idan akai mata jina jina zara rabu dan kanta, ta fi so a barta ta ji jiki ko wanda suke yi ya ji jiki da haka raini zai rabu tsakaninsu

Tana ihun kukan take fadin" ku sake ni! Ku sake ni! Idan baku sake ni ba na rantse da wanda raina yake hannunsa kuma kun jazawa kanku fitinar da ba zaku iya dauka ba
Dan walahil azim ko mazajenku kushewa ne a tsufa, ko a masalaci suke kwana tsabar musulunci ya ratsa su, ko mata maza ne sai na birkita lisafinsu, sai na rikita maku gidajen aurenku, sai na fitine ku ba dare ba rana! Walahi sai na koyawa mazajenku cika dare, sai n koya masu bibiyar mata! Sai Na gwada maku bariki iyawa ce!

Dayarsu ta saketa da sauri cike da tsoron kalamanta
Wada ke kusanta ta ce" ke ki riketa mata idan muka saketa zata koma wajen hajia ne kin ga fa ta fasa mata goshinta sai jinni yake

Kanta ta girgiza da sauri ta ce" to ku saketa hakanan mana zaku kama riketa mu tafi, kunna fa jin abinda take fada kuma ni na san wacece ita dan haka ba ruwana

Wa'inda ke tare da hajiar ma sun tsorata da hakan, dan haka suka ringa turata waje sunna fadin kawai ta kai kara gidan sarki a mata tsakani da ita da mijinta kar ta rabata da mijinta haka kawai da y'ayansu

Da wannan shawarar suka samu suka tura hajiar waje

Sai da ta fita sauran suka saketa

Da wani irin masifa ta ringa wawurarsu tana jufansu hakan ya sa du suka fice a guje

Dukewa ta yi wajen tana kukan takaicin bata yiwa hajiar yanda ta so yi mata ba,

Da gudu yarinyarta ta duka tana fadin" aunty, dan Allah ki yi hakuri, walahi talahi ban san abinda ya kawosu wajen nan kennan ba, ki yafe mini ki daina kukan nan

Dago dubanta ta yi tana kallonta

Idannuwanta ta lumshe wasu hawayen suka zubo a hankali ta ce" kin ga wadincen? Baki dayansu sai na saka su a uku! Yanda suka tozartani bayan bani da laifi ko? Sai na tozartasu daidai da laifinsu!

Mikewa ta yi tana goge fuskarta da tissu tana gannin yanda ake ta bata hakuri

Murmushi ta yi tana kallon mutanen dake zazaune ana ta masu aiki aman an dakata sanadiyar fadan ta ce" saloon dina a bude yake daga safe har zuwa dare
Zakunna zuwa nan ne muna amshe kudadenku muna gyara maku abinda ya dace mu gyara! Inaga kun san cewa mace sai da gyara ko?

Ta kara lumshe idannuwanta ta ce" irin haka ke kara min gwuiwar fitowa daga gidanmu
Idan bana samun masu jirana dan su fada min cewa lale ni din wata kwaro ce mai bada wuta a duniya da ba inda zan je sai na boye a daka

Murmushi ta yi tana kara fadin" tawa sallon daukakar kennan kwacewa du wace ta yiwa mijinta rikon sakainar kashi da wace bata tashi tsakiyar dare tana adu'ar Allah kar ya hada mijinta d aalshe money idan dai ba matar aurensa bace

Wata yar daria ta yi tana dage gira ta furta" du Alhajin da ya saki bakin aljihu zan kwasa ne!

Ihu ihu saloon din ya kwasa ita kuwa ta juya ta shige ciki ranta du a bace tana jin haushin irin yanda bata wanwanke fuskar banzar matar nan ba

Zama ta yi kusa da kanwarta ta janyota ta shiga tsefe mata kanta da dabara dan kar yarinyar ta yi kuka, tana tsefe mata tana mata cakulkuli nan ta samu ta ji sanyi a ranta sakamakon wasan da ta ringa yi da kanwarta

Aiyukansu suka ci gaba da yi, duda a darare suke aman sun san da zata yi fushi da su nan take zata yi shi ne
Itama cikin nutsuwa ta gama gyara kan kanwarta ta yarfa mata kannanun kitso ta saka mata tsakiya sukai kyau sosai a kanta ta shinfideta sannan ta saka a kawo mata abinci

Kanta ta fita suka wanke mata tas ta shiga wajen busar da gashi
Bayan ta gama ta zauna babar yarinyarta ta shiga yi mata wani irin kitso manya manya kwara hudu kawai, wanda ake yinsa kamar zane ya tafi baki daya baya
Da yawan lokuta an fi yinsa da atash, Kasancewar tana da gashi sosai sai ake mata da gashinta hakan ya saka kitson ya yi tsayi ya yi tudu sannan ya yi wani irin kyau mai tsarin gaske tamkar ka kwace ka dora saman kanka

Tana gama yi mata ta je ta zauna ta shiga gyara kwontacen gashin dake gaban goshinta tana nanade shi tana gyara shi da gel, a haka har gefe da gefen fuskarta ta gyara shi sosai
Gashin ido ta fitar da wani sabon kala wanda ya fi zama natural, ga tsadar gaske da yake da shi

Zama ta yi cikin nutsuwa ta saka abinta tana kallon yanda yake a idannuwanta
Chapter 23 · 0% Book details