Sashe 17
Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wayoyin dake cikin aljihunsa kasan babar rigarsa ne suke ta vibrate
Wayar wajen Zahrau ne da ta Najeeba da ta su ummu, ya amshe su ne a wannan karon bama dan bincike ba sai dan ya daidai du wani shigi da ficin da zai hada zahrau da wani, dan tuwon girma miyarsa nama
Sai dai tun da ya amsa yar karamar fara kar din samsung din ciki ake ta kira
Hannunsa ya saka ya lalubi wayar ya cirota
Yana kallon screen din sai ya ga sunnan kamar haka" Ambasador zumana
Wayoyin du farare ne, bai dai tantance wace marque dinsu ba hakan ya sa ya kasa gane ta waye
Sunnan sam bai masa, sunnan ya saka shi dubansu daya bayan daya dan sunnan nan ba sunnan mutunci bane, koda soyaya ne me ya kawo zumma a ciki?
Haka kawai ya tsayar da dubansa tsakannin ummulkhair da NAJEEBA, sun fi masa kama da wa'inda basu san meye jin magana ba
Jin an maido kiran ya saka shi dagawa sannan ya kara a kunnayensa
*haba baby, haba hearty, me yasa zaki ringa bani wahala haka ne? Kin san mutun nawa ke iya saka dukiyarsu dan su ganni? Kin san mace nawa ke faman na zama abokin gaisawarta? NAJEEBA na yi missing din ki, shi ya sa na taso na zo har masarautarku da alama baki ne da ku dan da kyar na iya gannin su liman babama, ki fito ina bakin zagayen kwanar gidan sarki dan Allah, idan ban ganki ba yau ba zan iya rintsawa ba*
Dukan ratabi maganar nan ya yishi ne ba tare da ya ji muryar wanda ya amsa kiransa ba, shi dai dama faman da yake ta daga tunda ta gadaga kuwa zai fada mata gaskiya ne ta zo, ta zo fa idan bata zo ba ba zai bar wajen nan ba
A hankali ya shiga cire wayar daga wajen kunnensa
Zuwa lokacin kuwa irin jin abin ana kallon kan nan ya saka NAJEEBA dago dubanta dan tabatar wa ke kallonta ne?
Da sauri da kuma tsoro ta mayar da kanta kasa ta sada sakamakon irin duban nan dake sakata jin babu dadi da ya tsareta da shi
Ne ya sa ya tsane ni ne?
Ta tambayi kanta
Yana kokarin mayar da wayar message ya shigo kamar haka" kin kuwa san irin tsarabar da na kawo maki? Na zo maki da iPhone 12, na siyo maki wata gown, na siyo maki wata sarkar zinari a dubai
*Baby ko nawa kike da bukata a yau zan baki in dai zan samu biyan bukata*
Biyan bukatar ne ya kasa karasa cewa na son ganninta, sai ya tsaya a iya biyan bukata
A dole yau ya gama yarda cewa yarinyar nan ta gama wulakanta su,
Karshen wulakantawa a yanzu har nan cikin gidan nan mai daraja take baiwa samarin nata zuwa, sannan har a zo har nan a yi kokarin yada lalatar da aka saba?
Bayan su ke hukunta wanda ya aikata lalata?
Tabas a yau sai ya kamata turmi da tabarya da kansa ta yanda zai yi mata hukunci baki daya garinsa ya sani dan akan baiwa gawa kashi ne dan mai rai ya ji tsoro
Ya san bai isa ya hukuntasu ba tare da huja ba
Zai nuna mata yaro yaro ne, zai bi ta da kansa idan ta kama! Zai yi mata kamun da ba zata musa ba, zai yi mata bulalar nan a tsakiyar gari sannan shi kuwa katon banzan zai haka rami a cikin gari a jefe shi! Baya son zina! Baya son mazinaci
A hankali ya fara jin tashin zuciya yana jin wani masifafen haushinta
Tir da ke! Ke kuwa bayan rashin jin magana sai kika auri aikin da zai rarake ki ya tsufantar da ke a wulakance ya hada ki da cuta ko ya hada ki da tabo? Mace da zata ji, da ta kilace kanta a dakinta komai muninsa dan samun sakamako mai kyau zuwa gaba
Dubansa ya kai kan Ummulkhair
Da hannunsa ya yafitota
Tun da ta ga haka a hankali ta tako ta dan tsaya dan nesa da shi kanta a kasa
Wayoyin saura ya hada ya mika mata yana mai nuna mata ta koma
Da murnar samun wayoyinsu ta juya ta koma kusa da yan uwanta, Najeeba fa nan da nan tsayuwar ta isheta, tun da ta ga wayarta a hannun Ummulkhair sai kafafuwanta suka fara yi mata kaikayi harma ta ringa jin kamar wace take jin fitsari
Ta gaji da tsayuwar iskancin nan da irin duban da su Zagra ke aikawa junnansu da mai martaba da kuma irin kausasashen kallon da mai garinsu ke aika mata na kiyaya wanda ya kara fitar mata da tsayuwar kallon kallon a rai ya sakata a hanakali ta ringa dan matsowa kusa da Ummulkhair
Raf ta kai hannunta saman nata ta damki mai wayoyin wanda tsaf a kan idannuwansa harma ya yi murmushin samun nasara domin dama burinsa ta karbi wayar dan ya aiwatar da aikinsa a yau ba sai gobe ba!
..............more comment aminan arziki😄😄😄😄😄💞💞💞💞💞💞💓💓💓💓💓💓💓💓
[1/20, 9:50 AM] Ummu Suhan😍: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*Na*
*SAJIDA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
11
Sakar mata wayoyin ta yi baki daya ita kuwa ta koma wajenta tana mai ci gaba da tsayuwa irin na yan uwanta
Sai da suka kuma yin magana wace iya su ke jin abinda suke fada tsakaninsu sirikan kafin SHAHEED ya kai dubansa wajen su ZAHRAU
Muryarsa kasa kasan nan ya buda bakinsa a hankali ya ce" ku koma ciki, sarki na godiya
Kamar jira take a salamesu, ita ta fara daga kafarta tama manta da sai sun risina sun kara godiya ta yi gaba a hankali ta shige ciki
Suma bayanta suka biyo sai dogarin dake tafe da wata katuwar ambulope dauke da sako dan nesa da su
A nan tsakiyar gidan suka tsaya NAJEEBA na ta dadana wayarta tana duba sakwonnin da ta bari, irin kirate kirayen da ta samu wa'inda du ba'a daga ba aman an daga na yau na yanzu
Sai tarin messages din da suka cika wajen ajiyar message suma sun cicika wajen wanda ta ringa bi da gagawa tana karantawa
Tsaf ta ga na yanzu an bude shi, kuma ta ga sakonsa
Zahrau ne ta ce" mu je mana meye wai kuka tsaya a nan bayan kun ga da mutun a bayanmu?
NAJEEBA ta waiwaya ta ga Dogarin nan ne
Karasawa ta yi wajensa shi kuwa ya sada kansa yana gaisheta
Murmushi ta yi ta ce" baba dan Allah daga kanka, ku kam bakwa gajiya da wannan gaishe gaishen? Kawo sakon ka koma abinka ka ji?
Da mamaki ya dago yana dubanta jin ta kireshi da baba
Tabas shi din datijo ne, aman kasancewarsa a karkashin gidan sarakan bai taba ji ab kireshi da sunna baba ba
Ko baki akayi in dai sun samu shiga ciki shikenan suma sun samu hanyar wulakanta mutane a bayan idannuwan manyan
Sam sarkin bashi da hayaniya baya anfani da sarautarsa dan wulakanta mutane, aman na kasa da shi sunna anfani da damar nan
Kwarai ya ji mamakin gannin kanwarsa ce, aman ta kiraye shi da baba
Sai ya ji darajar yarinyar ta shiga idannuwansa nan take harma ya sakar mata murmushi yana kokarin risinawa dan godewa
Kanta ta girgiza tana dubansa ta ce" ba dai zaku daina dukawar ba baba sai an jima
Gaba ta yi ta karasa kusa da yan uwanta
Tafia suka shiga yi suka nufi bangaren Anmy
Hat sauran sun samu shiga ta tsaya
Hannun Ummulkhair ta kamo ta saka mata sakon a hankali ta ce" eyah auntyna zan je na dawo wollah bako gareni
Ummulkhair ta yi murmushi jin yanzu kuma ta zama aunty bayan dazu ta gama cewa zata wanka mata mari,
Itama a hankalin ta ce" aman ai kin san ba'a zance a gidannan ko?
Najeeba ta ce" ai nima ba a gidan zan yi zancen ba
Kanta ta gyada har zata juya ta damko hannunta
Tana juyowa ta sanyaya muryarta ta ce" kar ki manta abinda Ya ke fada mana, mutuncinmu darajarmu kin ji?
NAJEEBA ta yi murmushi ta shafi gefen fuskarta sannan ta juya tana kalle kalle kamar munafuka ta kama hanyar fita
Ta jina tana leke har sai da sahun mutane ya fara daukewa sannan ta samu dam dam ta bi ta daya daga cikin kananun kofofin gidan ta fice da sauri
Tana fita ta cire alkyabar nan ta haska da hasken karamar wayarta ta samu waje ta ajiyeta sannan ta gyara lulubin lafayarta ta shiga takawa a hankali tana tafia
Idannuwanta take tafe tana lumshewa dan jin wata sansanyar iska na busawa ta ko'ina
Irin yanda wajen gidan yake da fadi da shukoki abin gwannin sha'awa, nan ne ake gudun dawakai
Tun da ta tunkaro babar kofar fita gabanta ya fara dari dari ta fara tunanin yanda za'a yi su barta ta fita
Wasu irin dafka dafkan mutane ne tsaitsaye a kofar fuskarsu harhada kamar basu san yaren fara.a ko sakin fuska ba
Me zan ce masu dan su barni fita? Ta tambayi kanta tana mai dan ja ta tsaya tana hangensu
Idannuwanta ta kuma lumshewa gannin bafa dare ya cika sosai ba ita kuwa niyarta ta je har saloon dan ko kiransu batai ba ta ga shin idan bata nan zasu iya kulawa da wajen yanda ya dace?
Rufar jikinta ta kara gyarawa kafin ta hade ranta
Tana zuwa ta ratsa tsakanin na faro, ta ratsa na biyu, ta zo na uku ne wata gabjejiyar murya ta dakatar da ita ta hanyar tambayar inda zata je a irin wannan lokacin?
Sai da ta juyo ta kalli mutumen, sarai ta san ya santa ya kuma ganeta dan haka ta masa karyar ba yar cikin gidan bane bama bai taso ba
Dubansa ta yi da kyau ta ce" sako zan karbo wajen Abih da suka fita dan rakiyar sarki
Sannin cewa sarki ya tafi kuma ta tabata mahaifinta na cikin yan rakiya ta samu wannan amsar duda tana da shakun idan har zai yarda