Sashe 94
Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
........................
Cike da shagwaba Zahrau ta kara rike wayar hannunta tana hangen yanda du yan uwanta ke ta kai kawo dakin NAJEEBA tana dan murmushin gannin zasu ci galabar abinda suke so ta kara rage muryarta ta fan saki kukam rigima ta ce" ur excellency my happiness, idan har ka amince min ne, idan baka amince ba zan taso a yau yau na zo gareka, domin du duniya babu aikin da ya kai min naka daraja wanda ba zan iya takewa saboda kai ba"
Sai kuma ta dan ja shashekar kuka ta ce" Duda nice babba mace a cikinmu, kuma ina son na ga na bara masu du wani farin ciki kafin na yi nesa da su, bale Nusaibana yar jaririya da ita abin tausayi, ina so na je da kaina wajen mamanta mu sasanta huby"
Ido kawai tsoho ke lumshewa yana sauraron wani salo na son rokon alfarmar ta zauna a gidansu ta kara yan kwanaki, shi abin sabo ya zo masa
Tabas a matansa Gimbiya takan tsiri tafiar shakatawa a kadan ta yi wata haka kawai ta je wata dubai ko london ko hawai.....gari dai da zata more rayuwarta ta jima a cen ga kashe kashen kudi ga abubuwa dai sai hamdallah kafin ta dawo, ita kuwa dayar sai ta shekara bata fita ko kofar gida ba, aman itama idan ciwon gida ya kamata takan lula a kadan ta yi kwana hamsin wai tana hutawa domin tana samun balewa daga kusa da Gimbiya bata yiwa abun rikon wasa, tana morewarta daidai gwargwadon iyawarta
Sai gashi ita daga sati daya, duda ya damu ainun domin kuwa shi kadai ya san irin farin cikin da yar karamar cikinsu ke saka shi, aman sai gashi tana neman alfarmar kara sati daya tak a gidansu, ba irin abinda ke birge shi sai idan tana fadim kaf duniya a yanzu yana gaba da kowa da komai nata, sai kuma cikin hikima ta nuna masa yan uwantanma sunna da nasu darajar wada ba zata iya samun farin ciki idan har daya daga cikinsu ya ce washhhhhh
Murmushi ya yi yana dan shafa gemunsa da ya fara furfura farare kal a sanyaye ya ce" Sati daya tak, daga shi kin yarda ba zaki kara ba?"
Itama murmushin ta yi jin sautin muryarsa kafin a sanyaye ta ce" In sha Allah ogana"
Wani murmushin ya kuma yi a bayanne yana jin kansa sai kara fadi yake ,
Sunna yin salama ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta karasa kusa da Ammi dake danna wayarta tana rubuta message
Allert ne ya shigo wayarta, tana dubawa ta ga kudi ne zunzurutu daga mijinta
Wani murmushin ta yi ta shiga rubuta masa messafe din godiya, hade da kalaman soyaya ba wani dar ta tura masa sannan ta juyo tana sauraron Ammi
Ammi ta ce" yaya bai kyauta min ba, yayya zai tashi kai tsaye ya yiwa NAJEEBA maganar nan a yanzu bayan ba lafiar kirki gareta ba tsakani da Allah? Gashi du ta rikice min ban san ta inda zan fara ba anya ban shiga hakkin yarinyar nan ba kuwa?
Zahrau ta ji Tausayin Ammi a ranta sosai, sai dai bata da niyar ja da baya dan haka ta kama hannun AMMi ta ce" Ammi, ba wani abu fa, idan har ta samu kulawarmu baki daya zata mike ta warware ne, kin ga abubuwa masu girma har biyu ne suka sameta a yau kadai, dole sai an rarasheta an lalamata
Ajiyar zuciya Ammi ta sauke kafin ta saki murmushi a sanyaye ta ce" ta ji ciwo ko?"
Zahrau ta dan sada kanta dan kunya, a hankali ta ce" Ammi, kin san tana da saurin warkewa a kan ciwo ko wani iri, bata da kam jiki in sha Allah nan da kwana uku zaki ga ta ware"
Ajiyar zuciya Ammi ta kuma saukewa a sanyaye ta kuma fadin" na so a kira likita kun hanna, bana so ciwo ya hanna mata nutsuwa fa"
Zahrau dai bata gushe da murmushi da son kwontarwa da Ammi hankali ba, har sai da kiraye kirayen salar isha.i ya tashe su
Tabas abinda ta kudiri niya ta samu, domin kuwa ita kanta wace suke tsoron yau hankalinta ya kasu kashi da yawa sannan ita kanta so take ta ga fara'ar Najeebar, uwa uba Ammi dake nan nan da ita, ita kuwa ta karbi jawabi ta langwabe sai shagwaba take sosai, lale tana jin ciwo a jikinta sai dai tunda ta wuni shiga ruwa da anfani da ruwa abin da sauki sosai, sannan lamarin mahaifinta da mahaifiyarta ta yiwa kanta shawarar zata cire wata damuwa, ita dai abinda ba zata yi ba shine ta lalabata ta koma masa, idan ta yi ra'ayi dan kanta halasss
Nana suka hade a dakin sunna ta hira da wasa da daria harda DAYABU da ya fito daga zance, Mardiya kuwa tana dakin da aka kaita ta yada zango da waya sai karbar banzayen hudubobi take daga wajen kawayen duniya, ita a dole miji zai saurareta, kasancewarta a gidan sarki kusa da tsohuwar matar mijinta kuwa ta yishi ne dan ta nunawa shegiyar Najeebar nan cewa uwarta bata isa ta dawo gidan MUTALAB ba!
..........................................
Karfe goma ce ta gota a agogon bangon dakinsa
Kwonce yake saman lalausar shinfidarsa mai dauke da zanin gadon ruwan ashe color irin manyan zanin gadon nan ne da ake dorawa bayan an shinfida bargunnan nan na lybia manya manya masu nauyi da kyau
Jikinsa sanye da riga da wando farare kar na baci, wandon mai dogon kafa ne rigar ce mai yankaken hannu aman itama baba ce rigar domin budadiya ce sosai
A irin gajiyar da ya yi yau, ya hau gadon nan ne da burin rinyse idannuwansa dan ya samu ya shiga baci,
Sai dai tunda ya kwonta din sai ya kai idannuwansa kan kofar shigowa wajen bacin nasa ya kura ido kawai yake kallo
Lokaci zuwa lokaci sai ya maida duban nasa wajen agogo sai kuma ya kalli kofar
Juyawa ya yi ya baiwa kofar baya ya shiga adu'o'in tsari
Ya jima yana yi ya tofa ya shafe jikinsa, sai kuma ya kuma juyo dubansa ya kai kan kofar
Mikewa ya yi zaune a hankali ya sauka daga saman bed din ya kama hanyar fita
Yana fitowa ya shiga bin falon da kallo
Shiru ne falon ba kowa sai kamshin turaran wuta da sanyin AC
Fitilar dake kara haske ya kunna ya kuma bin dakin da kallo
Idannuwansa ya dan kikifta gannin har karfe goma sha biyu ce ta gota
A hankali ya karasa wajen doguwar kujerar falon ya hau sama ya kwonta hannayensa tokare da keyarsa kafafuwansa daya kan daya yana kallon bakin hanyar coridor din bangaren Ammi
Irin motsin da ya yi jin kamar kiran sallah ya saka shi idasa bude idannuwansa da kyau
Hannayensa sun yi tsami sosai ya kai dubansa da mamaki wajen agogo
Tabas lokacin salar asuba ne har ya yi
Da sauri ya kara kai dubansa falon sama ko kasa abinda yake son gannin bai ganni ba
Lebensa na kasa ya tsinci kansa da dan cijewa yana jin kamar damuwar son sannin dalilin hakan na son kutsowa cikin lamarinsa
Tabe bakinsa ya yi ya mike ya nufi bayi dan shiryawa ya gabatar da sallah
A wunin ranar ya yi ta tunanin lamarin duba da Ammi bata yi masa maganar ba, shi kuwa sam bai nemi jin ba'asi ba, sai ya ci gaba da harkokinsa da yau da kulun
Wasa wasa sai da ta kwana uku bata waiwaya turaka ba, domin tun tana na wasa har ta hadu da na gasken domin athsmanta ne ya ringa tashi gadan gadan sakamakon kurar da aka yi ta bude window din dakin da suke
Ammi kuwa ta shaka ne, a ganninta ya dace ya bi bayan Najeeba, ko dan a yanda aka rakota daga bangarensa dan haka itama ta ki kawo masa maganar ko irin gaisheta da yake na asuba bata taba kawo masa maganar
Yau ta kama kwana hudu, a yaune Zahrau ta yi niyar garin Allah na wayewa zata je anguwa wajen Hajia Hadiza Awilo , matar dake gyara kala daban daban
Kamar yanda ya saba zuwa da asusuba yauma hakan ce, AMMI ce da UMMU zaune a dakin AMMI din, a yau tataunawa suke na lamarin da ya shafi AMMI din da kanta
Cike da damuwa take gabatar mata da abubuwa irin na halayan da Zinaria da mahaifiyarta ke nunawa, irin na Nadia da ta shigo jiya tsal itama ko sau daya bata zo ta gaisheta ba, da yannayin damuwa ta furta" ki duba ki ga yaron nan tun da aka rako NAJEEBA bai waiwayota ba, me ke damunsa? Me ya sa matansa basu dauke ni da mahinmanci ba? Ko dai laifin daga shi ne baya saka su a hanyar da ya dace su bani girmana?
UMMU ta ce" eyah Ammi, inaga lamarin nan dole sai da adu'a, bana so ko daya ki ga laifinsu, shima haka ina so ki masa uzuri, kin ga fa abubuwan kansa da yawa, wani abin yana iya shige masa a duhu ne bai san da shi ba
Aman in sha Allah ni zan nemi kusanci da matansa dan na gane meye matsalar, sannan shima zan zauna da shi daga ya samu lokaci
A hankali ya yi salama muryarsa a ciki aman kuma kunnaye zasu iya jiyowa
Amsawa suka yi baki dayansu shi kuwa ya karasa har inda suke zaune wato bakin bed
Hannayensu dake rike da junna ya saka hannunsa ya raba sannan ya shiga tsakiya ya zauna
Da yannayin sakin fuska ya saka hannunsa ya dago, dubansu ya yi da yannayi mai tarin kaunarsu da jin wani irin girmansu a zuciyarsa , a hankali ya furta " barka da asuba ummani"
Murmushi ne ya wadata fuskokinsu, cike da girmamawa, fa kaunarsa suka amsa gaisuwarsa
A hankali UMMU ta ce" Yaya fama da al'umah?"
Sai da ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya furta" ALHAMDULILAH "
mukewa UMMU ta yi cikin dubara ta furta" zan leka kicin na ga idan an gama Ammi "
Har sai da ta kusan fita ta ji muryarsa cike da kamala yana fadin" shin zan samu dan kwano tare da kowa Umani? "