← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 138

Sashe 19

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana gama fada ta kashe kiran ta kara fefesa turare ta kara duban kanta a madubi sannan ta ci gaba da kimtsa abinda ba lalene su kimtsa shi yanda take so ba

Bai dauki wani lokaci ba sai gashi ya tsaya a kofar shagon

Mikewa ta yi ta fita

Bude motar ta yi ta shiga, sai dai tana shiga wata ta fito tana kallon numbobin bayan motar
Kanta ta gyada ta koma da sauri ta dauki wayarta tana neman number kawarta

Da gagawa ta ce" kin kade kawata, kin kade, kin san da ambasador ne ya fita daga shagon NAJEE?

Kawar nata ce ta zabura daga zaunen da take tana ciye ciyen naman da aka gasa mata rusheshiyar mata da ita bata da aiki sai ciye ciye, itane matar ambasador kuma uwar y'ayansa uku ta ce" wace najee din? Saloo?

Amsa ta bata cewa" kwarai yanda na gansu haka Allah datar da ni gannin annabi kiri kiri

Ji ta yi zuciyarta ta shiga bugawa da sauri ta shiga neman abinda zata yafawa kanta tana fadin" gani nan zuwa

Su kuwa tafia suka yi mai dan tsayi ya tsaya wajen masu gashin kaji

Siya ya yi ya shigo motar da su ya tayar ya karasa wajen stade, wajen da yawanci samari ke zuwa su kebe da yan matansu su yi hira cikin aminci

Sannan wajen akiy duhu hasken bashi da yawa sosai

Kashe motar ya yi ya dauki wayarsa ya haska yana duban fuskarta

A hankali ya ce" ina son ki Najeeba, ke kuwa kina wahalar da tsufana

Murmushi ta masa ta ce" ka daina kiran min kanka da tsoho, ka fi yaro karami a wajena kai din jarumina ne na yarda da hakan

Kansa ne ya ji na huruwa ya kawo hannunsa a hankali ya shafi gefen fuskarta wanda hakan ya saka ta dauki hannunta ta bige hannunsa har wayar nasa ta fadi

Ranta ne kuma ta bata ta ce" meye haka? Ka san dai ba kyau ko?

Kansa ya dafe yana kallonta ya ce" wai wani irin ba kyau? Yaya kike son ringa cutata ne a rayuwa? Ni bance zan je cen ba, na adana zuwa cen har mu yi aure aman kuma dan taba jikinki ba zaki barni ba sai ki ringa hanna min ko dan ba ni ake yiwa son auren ba?

Idannuwanta ta lumshe cike da rakaicin soyayar zamani,
Soyayar zamani na bada gudunmuwa sosai wajen kokarin tatsar mazan zamanin da take
Dan me maza suke kokarin nunawa mace iskanci koda kuwa da nikaf suka ganta? Yanzu har fadi ake masu nikaf din sun fi masu yawo ba hijab munafurci shin laifin matan ne ko mazan?

Hannunta ta saka zata bude motar da sauri ya ce" hala har kin yi fushi? Kin ga kar ki min fushi dan Allah dawo mu ci kazarmu ki amshi tsarabobinki kin ji?

Najeeba ta juyo tana kara hade rai ta ce" bude min na fita

Hannayensa ya saka gaba daya ya janyota jikinsa yana fadin" come on baby meye na fushi bayan ko dan shan mintin nan baki taba barina na yi ba

Sosai ya riketa a jikinsa ita kuwa ta saka dukan karfinta ta hankade shi ta mika hannunta da sauri ta danna mabudin dake gefensa ta bude motar ta fito da wani irin karfi

Wani kukan takaici ne ya zo mata lokaci daya lafayarta ta warware

Bayanta ne ta ji ya daki wani abu

Da sauri ta juyo jin an rike damtsen hannunta

Kamshin turaran da ta shaka ne ya so halaka tunaninta da sauri ta saka hannunta da lalube ta lalubo jin jikin baya dauke da babar riga hakama fuskar ba nadi

Wata mota ce ta hasko wajen

Idannuwanta ne suka sauka a fuskar wanda ya riko hannunta
Idan ana fadin an yi gamo takan dauka a wai ne sai yau da ta yi gamo da kanta
Wannan mutumen aljani ne , aljanninma mai aljanin kyau
Girarsa biyu a hade take kamar ransa a bace sai dai kyan fuskarsa ya batar da bacin ran

Wani dogon hanci ne da shi da lebunna jajaye uwa na macen da ta san kanta take gyaran kanta

Kamshi yake mai dadi da sanyi
Kirjinsa wasu rikakun pecto biyu daka daka ne suka gaje wajen
Damtsen hannunsa kuma tamjar zasu fasa rigar jikinsa baka wace ta dame shi
Tsayinsa sosai ya yi mata tsayi hakan ya saka gaba daya kanta ke kallonsa sama sama

Rigar jikinta ta kasan abayar fara ce mai dogon hannu aman ta dameta sosai

Ya take dayan hannun lafayar nata hakan ya sa take kara karkacewa

Bata taba jin mutun mai karfinsa ba, irin damkar da ya yiwa hannun nata ya sakata jinta ficik a hannunsa

Gaba daya jikinta ne ya kara daukan rawa tana dubansa shima ita din yake kallo yana son gane shin abinda ya fitar da shi ya ganni ko ba haka ba?

Takaici, haushi, tarin tsanarta ne yake ji a ransa hakan ya sa ya kara matse tatausan damtsen hannunta
Bakinsa ya buda a kausashe ya ce"

To fa, waye wannan?

Ina sarki?

Zai samu damar hukunta NAJEEBA kamar yanda yake fata?

Najeeba gamo fa kikai mun shiga uku😲😲😲😲😲[1/20, 9:50 AM] Ummu Suhan😍: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

13

Kansa ya kara sadawa sosai kafin a hankali ya ce" Allah ya huci zuciyar Anmy

Zamanta ta maida ta gyara tana mai girgiza kanta, kennan ta tabata wata yake ganni har kamshin turaranta ya zauna a jikinsa?

Cikin nutsuwa ta ce" kar ka manta kai ne mai hukunta laifin da ya kai hukunci, shin aikata abin hukuntawa ka yi?

Sai da ya kuma lumshe idannuwansa ya bude a hankali ya girgiza kansa

Ajiyar zuciya ta sauke jin aa, dan haka cikin nutsuwa ta ce" bana gane gabanka bare batanka SHAHEED, bana fahimtar me kake boyewa a cikin zuciyarka
Maganarka ta kasance kadan

Wata ajiyar zuciyar ta sauke sannan ta ce" koda kai sarki ne, ni mahaifiyarka ce
Ka yi kokarin yin shawara da ni idan bata girmi kwakwaluwana na mace ba ka ji?

Kansa ya ringa gyadawa a hankali sannan ya dan dago ya dubi fuskarta
Muryarsa dai cikin nutsuwa ya ce" ALLAH ya huci zuciyar mahaifiyata

Murmushi ta yi tana lumshe idannuwanta ta ce" idanma wacece ka aureta

Wannan karon da idannuwansa ya bata amsa yana kara sada kansa a gabanta

Murmushi ta yi ta furta" Allah ya yi maka albarka

A hankali ya amsa da amen

Bai tashi daga gabanta ba sai da ya cike lokacin da yake dauka a gabanta sannan ya mike ya yi mata salama ya koma bangarensa dan yau ba zai fita fada ba su waziri na cem sunna gabatar da shara'ar garinsa mai mutane masu rigima da saurin kawo kara

Kamar wace ta jima bata zo dakin nata ba irin ta shekaran nan
Da murna da komai ta shiga tana ta kara kallon dakin

Jingina ta yi da jikin garun dakin nata, kai a duniya fa tana ji da dakin nan nata domin rabin tanadinta a cikinsa ya kare
Bata tunanin ko dakin wata mai kudin mai auren zai nuna mata wani abu shi yasa take gannin idan ta tashi aure za'a kwashe komai a kai mata gidan mijinta ne

Kalmar miji ta sakata buda idannuwanta

*Mijina* ta furta a hankali

Ina ka buya? Ina kake ? Yaushe zaka zo?
Ko a ina kake na san baka da aure,
Idanma kana biya yan mata kana da budurwa ka yi gagawar salamarta
Zama ta yi saman kujerar dakin nata wace take da yannayin takalmi mai tsini ta dan talafe kuncinta

A hankali ta ce" bana so ka zama farin mutun, dan rike NAJEEBA sai tsayayen namiji Farin mutun kuwa ya cika son jiki da sanyi sanyi
Murmushi ta kuma saki ta dora kafa daya kan daya ta daga kanta kadan tana dan wasa da habarta ta ce" sannan ina so ka kasance mai lebe pink iya na kasan na saman ya zama baki....bai dameni ba idan an ce dan shaye shaye mai baki ja aman fa bana so ka zama dan shaye shaye ka ji?
Hannunta ta dora wajen kirjinta tana kara dora kafa daya kan daya ta ce" kirji fafada, askin yan tasha........murya irin ta zaki, damtse mai taurin gaske
Idannuwanta ta rufe da hannayenta irin ta ji kunyar nan ta ce" fafadan kirjin da zan iya kwonci na yi isashen baci da juyi
Wani murmushi ta saki tana fadin" na san sai ka so mata, ....na san sai an so ramawa a so min kai abinda na fi sani shine ba zan yarda a karya min kara a ido ba!

Ke NAJEEBA!
Muryar zahrau ta sakata zabura tana kallonta , a rikice ta ce" meye?

Zahrau ta ce" kin haukace ne kina zaune kina magana kasa kasa kina ta murmushi kina wani irin abu a saman kujera lafiarki kalau kuwa? Yanzu da nace kowace maza ta gyara dakinta ke ko kakaba baki fara ba bale shara bale guga kina zaune kina uban meye?

Da sauri ta mike tana hararan Zahraun ta shiga yaye zannin saman gadonta ta ce" yaya ake so mutun ya yi kiba idan akoy irinku a waje? Shikenan ba zan zauna na hasaso yanda nake son gannin mafarkina ba sai an samu mai dirowa ciki ya katse ta hanyar sako nasa maganar?
Yaya ake so mutun ya iya labewa ya samu lokacin kansa idan ba wada bashi da kys din dakin wani?
Ni gaskiya ana takura min

Zahrau ta tabe baki ta ajiye wayarta ta shiga tayata gyaran dakin tana fadin" yaya ake so a yiwa gandamemiyar budurwa aure a kaita dakin miji ta aikata abin kirki idan gyaran dakinta kawai na daukan mata awa biyu?
Chapter 19 · 0% Book details