← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 138

Sashe 124

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fitowa ta tsinkayo maganarsa yana fadim" haka kawai yarinya ki wani saka mu kokowa a bayi bayan ba kyau magana a bayi, kuma ki wani saka na rasa jam'i kai yarinyar nan bakya jin magana"

Baki ta bude da mamaki tana karasawa inda yake miko mata doguwar rigarta ta sallah da har ya fice ya dauko mata

Da sauri ta warwareta ta shiga sakawa sannan ta saki tawul din kasa
Ita kanta ta manta da komai bale shi dake kallonta hakan ya sa a rashin tunawa ta duka ta zare jikaken wandon dake jikinta ta ciro shi baki daya

Ido ya zaro gannin katon wandon da ya mata daidai, itama sai a lokacin ta ga abinda ta aikatan, ai da sauri ta matse shi a hannunta tana tura baki ta juya zata koma bayin

Hannunsa ya mika ya kamota yana mai kara bin jikinta da kallon kasa kasa, hankali ya ce" Let's pray "

Kai ta dan gyada masa, suka nufo kilatacen wajen sallah

Lalle ta yabawa limancinsa, ta yabawa irin tsarin sallarsa harma ta ji a ranta zata kara dukawa ya kara koyar da ita adininta domin kuwa ita ko a ina ta hadu da wanda ta san ya fi ta ilimi a kan wani abin bata jin kunya ko girman kan duka masa ya koya mata bare adinin musulunci mai dauke da abubuwa masu girman gaske wa'inda wasun har ka koma ga Allah ba zaka taba saninsu ba

Mikar da ita ya yi a hankali ya sakata gabansa shi kuwa a bayanta , bayanta mane da kirjinsa ya shiga takawa da ita suka nufi falon gidan

Ita dai inda ya yi da ita take bi, sai ganninsu ta yi sun yi dakin cin abinci

Kayatacen tankamemen table din diner ya nufa da ita mai dauke da wasu irin kuloli masu ado da zeba
Kana gannin kulolin nan ka san na manya ne, ga fruit wanke tass a cikin wani bowel mai shara shara domin ana iya gane ko meye a ciki kuma a rufe da wani marfi
Sai zug zug din da ta yi imanin jus ne a ciki

Idannuwanta ta lumshe sakamakon jin hucinsa wajen wuyanta wanda ya zame hular doguwar rigar tuni , sai take jin jikinsa da dan gumi, aman ta kasa tambaya

A hankali ya ce" ni yinwa nake ji "

Dan murmushi ta yi wanda bata shirya ba domin irin yanda ya yi maganar sai da ta ji kunya walahi

Kanta ta dan dago ta dube shi, sai kuma ta cire dan ita a yanzun irin duban nan nasa da sam baya barinta da shi ke rikitata, gashi dai maganar sanyi ke fitowa daga bakinsa zuwa gareta, ama kuma idannuwansa na jifanta da kallon tsanar dake ladaftar da ita!

Wajen cin abincin suka karasa

Kafin ta zauna ta dauki plat daidai cin sa
Aman sai ta ga ya cenza mata da wani baba

Yana kallon yanda take zuba abincin yana koya, domin dai sultan ko dafa ruwan zafi bai iya ba, inama ya samu damar dafe dafe shi da ya tashi cikin horon koyon abubuwa da dama ciki harda kasuwanci wanda bai fara harkokin mahaifinsa ba sai da ya kama masters a marketing dinsa sannan ya karbi komai yake tafiar da shi daidai da gwargwadon iyawarsa domin kuwa harta da takardar business communication sai da ya hada saboda tsaro

Tana gama zuzuba komai ya mike ya dauki farantin ya yi gaba

Bayansa ta bi da kallo, gane cewar ba a nan yake so su ci abincin ba ya sakata dan bubuda jus jus din
Na aya ta dauka da abin zubawa ta bi bayansa

Cikin nutsuwa ta karasa wajen da yake zaune yana jiranta ta ajiye sannan ta zauna itama
Bismillah ya yi mata ya fara saka hannunsa ya fara ci , kafin ta fara ci itama

Ta yi dagowa ya kai biyar tana kama shi da irin kalon nan, hakan ya sa ta yatsina fuskarta bayan ta hadiye abincin ta kura masa ido
A sanyaye ta ce" Me ya sa kake jifana da kallon tsana tun shekarun baya? "

Da mamaki yake kallonta, kallon tsana kuma? Wani irin kallon tsana ne yake jifanta da shi?

Gannin tana son cire hannunta ta tashi sai ya riko hannun nata
Idonta ta dora saman hannunsa dake rike da hannunta
A hankali ya fitar da hannun nata sannan ya matsota sosai
Hannun nan nata dake rike a nasa ya shiga sidewa daya bayan daya yatsotsin wanda hakan ya sakata shagala da kallonsa
Sai da ya gama sannan ya maida nasa hannun, wanda dama ga vokali ta dauko aman sai ya saka hannu ya diba a hankali ya nufi bakinta da shi
Dan langwabewa ta yi tana sauke ajiyar zuciya ta ki ta bude bakin nata

Yana mai dubanta a sanyaye ya ce" Ki ci kin ji, ki yi hakuri ki ci ko zan iya ci "

.............sai da na gama ya goge😭😭😭😭😭😭
[3/31, 11:36 PM] BAK'A CE: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

63

Wannan karron sai d akirjinta ya doka, harma ta ringa jin tamkar zata fashe da kuka da tashin hankali, a hankali ta kuma kurawa fuskarsa ido tana kallonsa ta kasa karbar abincin, shima dai kallon nata yake harma yana jin bashi da wani abu mai dadin kallo irinta a duniya sai dariar mahaidiyarsa

"Kin san kin ada kyau kuwa JEEBA?" Ya fada kasan makoshinsa yana mai shafa gefen fuskarta, bai bari ta dawo daga sumar da ta yi ba ya dora da fadin "Ina so idan Allah ya sa inafa rabon haihuwa a duniya y'ayana su ringa yin kamaninki da fatar jikin ki, da shahwabarki, ama banda fadan ki"

A hankali ta furta" Na shiga uku, meye hakan kuma?"
A kasan zuciyarta ta yi maganar, ama a fili ta bayana cikin sanyi da rarabewa,
Bakin nata da ya yi furucin ya kurawa ido, da ba dan baya son matse mata waje ta hanyar nuna mata zanlar zalamarsa a kanta ba, da ya kara kusanci a tsakaninsu a wannan zaman ta hanyar mayar da su abu guda a irin wannan lokacin

Buga kofar da ake a karro na ba adadi ne ya saka shi kai dubansa, haka itama

Hannunsa ya mika ya dauki remote tare da tablet dinsa ya kunna ya shiga kallon mutanen dake tsaye a cen wajen dogarai

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ajiye wayar ya dauki jus din nan ya zubawa kansa ya sha sosai

Kallonta yake kasa kasa kafin ya furta "zan je na dawo, ki ci abinci kin ji?"

Kanta kawai ta iya gyada masa tana mai binsa da kallo har ya shige cikin baban dakinsa

Ya dauki lokaci kamar minti ashirin sannan ya fito
Gaba daya sai ta ji wani irin yam yam yam a jikinta a lokacin da kamilin sarkin, mai wukar yankan ya bayanar mata a Sultan SHAHEED
Ajiyar zuciya ce ta kwace mata tana kallonsa sai ta ga wajenta ya nufo hakan ya sa ta ji zuciyarta na rawa

Yana karasowa da gaya sai ya ja ya tsaya kamar yanda yake yiwa Zinaria ta kwashi kirari ko ta dukar da dubanta har sai ya fice

Da farko kan nata ta dukar kasa kamar yanda idan aka kawora shara'a ko ta yi rakiya
Sai dai kamar yanda ya yi tunani ko minti daya bata yi a hankan ba ta shiga dago dubanta a hankali har ta sauke saman fuskarsa

Murmushi ya saki ya rage tsayinsa ya mikar da ita tsaye

Hannunsa ya saka ya janye abin wajen bakinsa sannan ya kusanto fuskarsa da tata
A hankali ya shiga kissing din lebunnanta har sai da ta bashi amsa son ransa sannan ya cikata ya sakata a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya
Muryarsa ciki ciki ya ce" Yaya aka yi bakya jin tsoron hada ido da ni? "

Itama sai ta ki bashi amsarsa, domin ai ita ta fara tambayarsa ya mata banza ko, sai da ya gaji dan kansa sannan ya cikata

Har ya fara tafia ya ji ta ce" baka koshi ba kuma zaka fita? "

Dakatawa ya yi ya juyo gareta, sai da ya mata kallon tsaf ya ce" ki tanadar min wani abincin, domin zan fita da matsananciyar yinwar ki, fatana kar na ringa magana ina ambatar sunnanki a lafuzana......." ya karashe yana mai kashe mata ido daya sannan ya juya yana mayar da rawanin wajen bakinsa ya fice

Ta kai minti biyar a tsayen nan tana kallon kofar da mamaki
A bayane ta ce" kan Uba," sai kuma ta juyo tana sakin murmushi

Sai da ta dan jujuya ta kwaso shokiiiii ta juya wajen kofar nan ta sauke masa ita a fili ta furta" gayen zai halaka ni ".........

Sunna fita daga nan waje suka samu mahaifin Nadia ya gabatar masa da dukan sakamakon binciken da aka yi, hakama lauyan da ya dauka da kuma police din da ya shiga cikin mutanen gidan sarautar ya yi basaja
Sosai ya gamsu da bayanansu, sannan aka tafi da dukan wa'inda suke da hannu a ciki tun daga kan wanda ya ga lokacin da ake kama macijin ya ji labarin macijin ne ya yi kisan an bai fada ba, da wanda macijinsa ne, da sauransu

Sai da aka gama hargitsa gidan sannan aka saka kowa kuble dan za'a fitar da Zinaria

Da kansa ya saka aka fitar da ita aka kawota gabansa

Gaba dayanta ta zube kasa har jikinta na rawa ta fashe masa da kuka tana neman afuwarsa, cewar ba zata kuma yarda ta hada kai da wani dan a cuce shi ba
Ta dora da fadin" Haba ya mijina, ka gafarta min laifukana a gare ka, na san da ban kyauta ba, ama ba zan taba hada kai da shi dan na ci amanar aurenka dake kaina ba, ban taba cin amanar aurenka dake kaina ba "

Ransa bace matuka , ya kalleta, muryarsa kausashe ya ce" Da kin san darajar kanki, da kin kilace min kanki, sai dai kashhhh........, shiru ya yi na dan lokacin kafin ya furta" idah ta hau kanki, na tura takatdarki wajen sarki"
Chapter 124 · 0% Book details