← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 138

Sashe 101

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ummu ta ci gaba da fadin" Tabas aure ya ginu ne da rayuwar Sex, sai dai baban abinda nake so ku gane kyakyawar mu'amala tsakaninka da mijinka shi ke sakawa a fi jin dadin komai, ina so ku yi kokarin jajircewa dan gannin kun wanzar da kyakyawar mu'amala irin ta shakuwa da fahimtar junna tsakaninku da mazajenku, ba wai dan kuj auri masu mata ba wanda ke kanki Ummukulsum zaki tare da mai matar ne halayansu ya saka ku hau kuma ku bi, ko kuwa ku ce da karfi da yaji zaku cenza su......aa, ita rayuwar baki dayanta yar dabara ce, yar siyasa ce, hakuri, da kuma fadawa Allah. Ba ina nufin kowani namiji ya saba da gim gim gim da matarsa ba aa, wani namijin matar tasa da ka zo ka tarda mace ce da ta san kanta, ta gane cewar idan har ya ci gaba da irin halayan nan na komai ba ruwansa ba ita kadai zai shafa ba harta da y'ayan da zasu haifa yana iya shafar su sai ta jajirce har Allah ya sa suka kasance aminan junnama ba tsorata zaki yi ba, zaki shige ne kema, zaki damki damar nan sannan ki dan kara naki salon da zuciya daya ba dan ki cutar da ita ko y'ayan mijinki ba. Idan kuwa namijin nan kin tarar da shi da halaya tamkar fan dambe kamar yanda na fada maku dole sai kin bi a hankali sannan kin bi da zafi zafi, kuma sai kin jure kin saka hakuri a zuciyarki a hankali har ki samu sasauci.....sannu sannu har ki fi karfin wulakanci a wajensa, irinsa ne sai ki ji ana cewa wane ai ya dauko ruwan dafa kansa, zafin nan du babu, mutumen nan idan yana gidan amarya hum zaka ga ya shige ne da wuri fitiwa ta gagara, zai je ya lafe abinsa ko me suke yi a gidan? Lolz abubuwa dai ire iren haka............."

Dan nisawa ta yi tana kallonsu ta ce" komai tsufan namiji, komai yarintarsa idan har ya hadu da mace zata iya daidaita abinta irin yanda take son rayuwarsu ta kasance, aman fa ban ce da ku wai zai zama mijin kan tace ba, kai ni kaina bana son namijin da lokaci zuwa lokaci ba zai botsarewa maganana ba domin hakan na bambanta min ni ba mamansa bace sannan a karkashin ikonsa nake, tunda muka samu kyakyawar fahimtar junna koda kuwa mun samu sabani shiryawarmu abu ne mai matukar sauki, mai yiwuwa daga idannuwanmu sun sarke da junna komai zai wuce, ko idan na zo wucewa yana iya riken tafin hannuna shikenan na huce, ko ya yi anfani da wani sunnan dake sakani nishadi, idanma nice na bata masan da nawa salon da ina yi zai sauko komai hawan da ya yi, abinda dai nake so shi ne *KAR KU KASANCE KU KOMAI FUSHI, KAR YA ZAMANTA IDAN HALIN NUNA FUSHIN NAKU YA KAMA A RINGA ROKAR KU ANA LALASHIN KU KU KI SAUKA HAR KU GUNDURE SHI YA YI BANZA DA KU, SANNAN KAR KU KASANCE KU BAKWA FUSHI EHE*"

Wasa wasa a nan UMMU ta tare da y'ayanta, tun sunna jin kunyar wasu magangannun har ya zamanto sun fara yi mata tambayar ta yaya hakan zai kasance? Har ya dawo sai su yi murmushi su kalli junna, a haka har Ummukulsum ta samu kwarin gwuiwar duba wayarta, irin tarin sakwanin da Yarima ke turo mata ta ringa karantawa Ummu da yan uwanta a hankali cike da nutsuwa har ta kai karshe wanda sakwannin tun sunna nuna tsagwaron ban hakuri da neman yafiyarta, har suka dawo kamar da wasa yakan dan sirka kalmomi kamar haka" kin tsaya min a zuciyata, na kasa cire wannan rana " , har ya dawo dora harafi a cicire kamar haka "i lv u", karshe dai baro baro ya doro shi a hade cewar "walahi i love you", har da irin yan yayan wayan nan dake nuna idan mutun na cikin halin sad da dai sauransu

Abinda ya fi birge Ummu bai taba tsalaken rana ba, hakan ya sa ita kanta a yau ta ji tana iya yafe masa harma ta dubi Ummukulsum ta umarceta da tana iya rubuta masa amsa dan gannin idan har ta fara daukan darusan da take masu a yau
Cike da nutsuwa ta dora kalamai kamar haka" *Asalam Alaikum, fatan an wuni lafia? Dan na kawo gaisuwata ne da fatan a yi baci lafia*

Bayan ta gama ta karantawa Ummu , ta yi murmushi domin kuwa kwarai hakan shine daidai, sam bata so ta nuna zumudinta ta hanyar bashi amsa ta farko ko ta nuna masa kamar shi take jira, sannan rashin ambaton sunnansama nada nasa wajen, tana turawa ta sakata kashe wayar dan ta tabata idan ya gani yana iya beman kiranta ita kuwa ta hane su amsa wayar saurayinsu mai mata a irin lokacin nan, dan kuwa ba dadi idan ka yiwa wata kaima za'ai maka!

Murmushi kawai NAJEEBA take har tana dan rage girman idannuwanta irin tana dan kausasa kallonta tana hangen abubuwa da dama, ta tsinci kanta da jin zata kwatanta abubuwan nan, tabas zata kwatanta abubuwan nan.

........................................
Baki daya a falo ya yada zangon aikinsa a yau, ba komai ne yake hadawa a computernsa ba sai binciken da ya saka wani kwararan police abokinsa ya yi masa a kan rayuwar mutanen nan uku komai da komai da ya shafe su
A hankali ya ringa nazartar irin abubuwan da aka kawo masa har ya tsaya kan Amintacensa
Ya maimaita wani waje ya kai sau uku, wanda abinda ya samo da gaskiyar lamarin ba haka bane
Kan soyayarsa ne da ita, an nuna ya so ya yi soyaya da ita sai dai mahaifinta ya dakatar da kamarin bayan ba haka abin ya kasance ba, soyaya sak suka yi mai zurfin gaske daga baya suka rabu a lokacin da mahaifiyarta ta fito karara ta nuna masa shi din ba dan wani bane, ba jinnin sarauta bane kwarai zai yi rashin kunya idan ya nuna yana son yar sarki, dan haka ya kiyaye takunsa ya bar matar manya wa manya
Hakan ya hanna masa zaman garinsa ya dawo DANAGARAM, karshe ya ajiye aikinsa harma ya samu kusanci da sarki ya samu karbuwa, wannan shi ne gaskiyar lamarin abinda ya kawo shi garin DAMAGARAM har ya zama gagara badau a cikin masarautar ta hanyar samun kusanci mai karfi da SULTAN
A hankali ya ji ya kasa cire ayar tambaya a kansa, *WACECE* a cikin y'ayan sarkin?
Sai a kan Liman baba, wanda shima ya samu wasu karin bayanai kan wa'inda yake da su a kansa
Sai kuma mai bulala, wato baban dogarin zabga, wanda shi ke tsaye da babar bulala a fada......labarin *Dandatsa* da akai masa tun a shekarun mahaifinsa, ya kasance ya afkawa mata har shida hakan ya sa akai masa hukuncin dandatsa aka jefa shi a gidan yari na dan lokaci
A lokacin da ya fito sai ya samu matansa biyu sun barshi, y'ayansa kuwa ba maganar su yi masa biyaya, dan haja sai ya koma wajen sarki Allah ya jikan rai da koke koke da komai da alkawarurukan ya shiryu,
Sarki sai ya amince, ya janyo shi jikinsa dan ya kara shiryuwar, ya nuna masa kyakyawar hanya da komai karshe har ya samu mukamin nan, sai dai har yanzu shi da mace sai dai kallo, shi a yanzu matan nema sam basa bashi sha'awa sai dai ya kalla ya cire kansa.

Kansa ya dago ya kuma kallon hanyar da ta nan ya dace a ce ta shigo tun dazun, sai dai yanzunma ba alamunta
Dan murmushi ya yi a bayane yana dan girgiza kansa, wato dai AMMI ta shirya? Bakinsa ya tabe irn bai dame shi ba, sannan ya mike da computern nan ya yi ciki

Sai da ya daura alwallah kafin yake hawa Bed sinsa bayan ya yi wanka
Idannuwansa ya lumshe a hankali ya cije lebansa na kasa
Baki daya jikinsa ne ya amsa masa a lokacin da ya hango kogin nan, tabas wannan shine kogin zuma
A hankali ya buda idannuwansa da har suka fara amsar sakon nan ya sauke dubansa kan AC din dake kusurwar dakin, a fili saman lebensa ya furta "Bacin zaki hana min yauma?"
Sai kuma ya lumshe idannuwansa yana hasashen irin haduwarsu ta gaba, zata amshi tukwuicin tsagerancinta ne a hannayenta! Wato dai yar fitsarariyar AMMI ba zata shiryu da neman magana ba?
Jikinsa ya ringa hadewa ko zai samu dan sasauci cike da wani takaici dake taso masa, wai yana da mace uku aman yau kwanansa hudu rabonsa da Mace dan kawai yana tare da amarya? Hum! Ai kwanakin amarcin saura gobe kawai zasu zo ne a yita ta kare walahi shi ba waliyi bane!
Chapter 101 · 0% Book details