← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 138

Sashe 112

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ammi kai kawai take girgizawa hawaye masu zafi suna zuba daga gurbin idannuwanta sunna sauka saman fuskarta, NAJEEBA kanta a zaune take ta zubawa mutanen nan uku ido, tun daga kan SULTAN, NADIA, uwa uba Zinaria
Haka kawai take jin abin sosai a ranta, harma irin tsayuwar da ya yi na yan mintunna ya kura mata ido ya bata tausayi

A hankali ya juya ya nufi dakansa wanda hakan ya saka du wani mutun dake wajen rakashi da ido, UMMU kanta hawayen take cike da mamakin wata amanar ta mutanen yanzu da sam basu da amana, shekara nawa kana tare da mutumen, du yawancin sirinsa da yardarsa ya yarda ya baka shikenan rana tsaka a kama irin wadinnan magangannun a kansa

Bai jima sosai ba ya bayana, cikin shigarsa ta sarakai sosai ya fito a yanda yake fitowa da

A yanzu sai ya zauna saman kujera ya dake
Ya dan jima a haka sannan ya dago da dubansa ya sauke kan NAJEEBA dake zaune jikinta doguwar rigar nan ce kawai ba wani lulubin da ya dace , dan haka a sanyaye ya furta " AMMI da UMMU, a lulube GIMBIYA NAJEEBA da NADIA "

AMMI na kallon yannayinsa cike da wani irin tausayinsa a zuciyarta ta janyo hannun NAJEEBA ta sakata a jikinta sannan ta lulubeta da alkyabar dake jikinta hakan ya sa sosai ta baza Alkyabar kasancewarta mai fadi da tsayi ga kauri sai ta wadace su ta baje da kyau ta rufe su su duka
Hakama UMMU ta aiwatar ta hanyar mayarwa da Nadia tata jikinta bayan ta kara lulubeta

Sandar dake hannunsa ta sarautarsa wace a yanzu a komawarsa ya daukota ce ya doka da karfi wanda hakan ya saka lokaci daya daga Zinaria, UMMU, AMMI, suka yi kasa da kawunnansu, Nadia da mahaifanta ne basu gama gane wasu sirinan maganar sarki ba hakan ya sa sai da suka kalli yanda su AMMI suka yi sannan suma suka sada nasu

Budewar da aka yi aka shigo da salama ne ya saka gaban AMMI yankewa ya fadi, muryar Amintace ne ta bayana rikeken Namiji maji karfi, tsayaye mai yannayin tsayayen namiji,

Sai da ya dan saci kallon mutanen wajen sannan ya yi irin gurfanar da yake dan kawo gaisuwa ga SULTAN SHAHEED

SHAHEED kallonsa kawai yake, sai da ya jima a haka sannan ya ce " Ka kula da bata mutu ba, gatanan ta mike da ranta AMINTACENA? "

irin yanda ya furta kalmar AMINTACENA din yana mai cije lebensa da karfi ya saka Ammi rintse idannuwanta cike da bacin rai da fargaba

Kara sada kansa ya yi, du da irin yanda gabansa ya kwonci kwonci ya fadi, sai ya yi kokarin anfani da kwarewarsa ta wajen yaudarar mutanen dake tare da shi da zuciya daya wa'inda basu gama fahimtar shi din ko wanene ba ya kara tausasa kalamansa domin sam bai taba tunanin Zinaria wawuyar da zata iya sakarwa lokaci daya bane harma ta fadi abinda ke faruwa dan haka ya dauki aniyar karyatar da Gimbiya a gaban sarki duda hakan baban laifin da ake iya gurfanar da shi ne, sai dai zai yi anfani da tarin yardar da Sarkin ya yi masa shima ya kwatanta kwatar yancinsa, dan haka ya ce " wace bata mutu ba ya uban gidana "

Shaheed ya kara lumshe idannuwansa cike da dacin zuciya ya dan saki murmushi yana kawar da kansa, ta yaya zai zauna su ci gaba da wulakanta junna? Dan haka dubansa ya kai wajen mahaifin Nadia ya ce" honorable, gashi a tafi da shi PeJi, ka sani wannan yaro horona ne, domin tun yana da yan dabarunsa na kasancewa police a da, na kara nitsar da shi na bashi horo kala daban daban na yau da kulun, sai kun yi taka tsantsan da shi, sai kun dora idannuwanku a kansa sosai, kar ku saka shi a daki mai kasa ko mai ruwa, ku kiyaye saka shi a daki mai duhu , ya kasance a kejin da hasken wata da rana ke iya haske shi, ya kasance koda mutun daya ne na ganninsa hakan zai hanna masa du wani yinkuri na gannin ya kubutar da kansa"

Dan sasautawa ya yi gannin irin yanda ya dago a gigice yana kallon SULTAN

SHAHEED ya maido dubansa cikin idannuwansa, ya kasance sun yi ido cikin ido da wani irin kakausan kallo da idannuwansa da suka dauki ja yake kallon na Amintacensa, da sauri ya sada nasa duban dan kuwa baba da babansa fa, sai dai baki daya jira yake ya karasa ya bashi damar yin magana aman sai ya ji ya dora da fadin " A bincika maganar Gimbiya NADIA, sannan a yi anfani da shaidar abokiyar aikatawar tasa, na baku damar ku shigo fada ku yi binciken da ya dace da su baki daya, du wanda ya taka doka ta taka shi koda kuwa *Gimbiya Zulaihat* ce ! Ya karashe yana mai doka sandar nan a kasa a kausashe ya furta " *Idan har ka yi gigin tashin da kake kokarin yi a wajen nan zan tashi mu gwada karfi da kai wulakantace mai wasa da Amanar Allah! Domin ina mai tabatar maka ba zan barka ka huta ba har sai ka samu naka hukunci daidai da laifinka, sai ka girbi abinda son zuciyarka ya kaika aikatawa!*

Sakwat ya yi ya mayar da kafar tasa, ba zai yarda du haukansa Sultan shaheed ya ajiye alkyabarsa dominsa ba, shi kam ba yau ba ya ringa tunanin karfin Sultan Shaheed kamar mai iskokan dake doka mutun da kasa, irin mutanen dake kawo masa tsagerancin da wani sa'in dole sai shi zai iya tankwasa su bake wa'inda suka shigo da takamar asirinsu dake tatare da su hakan ke sakawa su gagari dogarai, daga ya fuskanci hakan yake gagawar yiwa tufkar hanci tun kafin a gane gazawar dogaransa da ba gazawa ce sukai ba, lale lale shi din ne ya san abinda ya taka shi yasa du wani kwaro mai jin kansa na hayaki yake yin lakwas a gaban Maza, dan kuwa makashin maza maza ka kashe shi ba shaka!

Sojoji ne su hudu suka shigo, babansu ne da yara uku,

Suma dukawar suka yi suka kawo gaisuwar sannan mahaifin Nadia ya kora masu bayani, da irin tsaron da ya kamace su da komai, sannan suka sakawa Amintace ankwa wanda ke ta fitar da huci yana son kallon Zinaria dake kuka ya kasa har suka fita da shi

Sai da ya kuma rintse idannuwansa ya bude a sanyaye yana kallin iya mutanen da suka rage domin mahaifin Nadia an tafi da shi, sai mahaifiyarta , ya kai dubansa wajen AMMI ya furta" A kilaceta bangaren bayi "
.yana gama fada ya mike inda baki daya Zinari ta idasa kara zubewa tana son kama kafafuwansa dan ta bashi hakuri, aman ina ya ki bata damar hakan domin na farko da ta rike irin yanda ya wancakalar da ita ne ya sakata idasa fashewa da kuka tana fadin ita bata yi kisa ba, bata yi zina ba za'a kilaceta a bangaren Bayi? Ita ba baiwa ba jinnnin sarkin Agadez, matar Suktan shaheed wace ta bashi d'a, itane yau za'a kai bangaren bayi? Dan ta yi kishi shikenan sai a wulakantata?
Chapter 112 · 0% Book details