← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 138

Sashe 72

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wajen kusan kowa hankalinsa na kanta banda Zinaria da mahaifiyarta da suka gama mutuwar tsaye a lokacin da suka gama fahimtar a yau wata bak'ar fatar, daya daga cikin cousins din Mai Damagaram, y'ayan Mutalab , wace suka fi takun sak'a da ita ta zama mata a wajen mai Damagaram, ZINARIA ta juya wajen mamanta, a fili cike da kidima ta ce" ashe wannan ce ya aura? Ya rasa wace zai had'ani kishi sai wannan marar kunyar yarinyar yar wulakanci? Ya rasa wa zai d'auko min sai wannan bak'ar yar mai idanuwa kamar na mujiya?" Kuka ta fashe da shi a fili wanda da sauri yayarta ta kamata ta aniya mayar da ita saman kujerar

A rikice mahaifiyarta ma ta kamata kasa kasa take fadin" ki min shiru, ki bari mu fita walahi ba zai yiwu ba!"

Kamar wa'inda suka samu TV dubansu ya dawo wajen NADIA da ta karaso kusa da Najeeba.

Hannunta na rawa ta kamo hannun Najeeba, auntynta kuwa kamar zata k'urma ihu dan takaici.

A birkice ta ce" ke kin san na san cewar bakya son kishiya, ke kin san nima haka ne, kuma ke kin san ke kika min alk'awarin rabani da kishiya ko da na auri miji mai ita, Najeeba, kin san ba zan taba auren mijinki kaina sane ba, koda maye nake da sani ba zai taba faruwa ba, ni ba maciya amana bace."

Najeeba ta lumshe idanuwanta tana jin yanda suka yi mata wani irin nauyi.

A hankali ta ringa satar kallon mutane
Kyam idannuwansa a kansu. Du abinda ke faruwa da ido kawai yake bi tamkar baya wajen.

Haka su Anmy har baki Anmy take saki tana bin ikon Allah
Zinaria kuwa sai danarta ake kamar zata hau bori.

Idannuwanta ta maida wajen Nadia
Sai da ta lumshe su sukai wani luuu sannan ta bud'e su.

A hankali ta ce" ke, daina irin haka mana, meye a ciki dan kin auri miji? Na ce maki na damu ne? Bayan kema ya d'auko Barira, ina taya ki murnar malakar abinda kika jima kina marari, ke kin san ba nawa ra'ayin kennan ba dan haka kar ki bani kunya kin saka ana kalona!"

Maganarta a fili ta yi ta, cikin kwonciyar hankalin da ya zama jikinta, duda daga kasa wani irin jimkar hannun Nadia ne ta yi wanda ya saka Nadiar shiga wani rud'un
Ta ce babu komai, irin magangannunta sun bayana karara ita auren kansa baya gabanta, aman kuma irin rikon ta mata ta tabata akoy wata a kasa.

Hannun nata ta saki ta koma ta zauna tana mai gyara alkyabarta da kyau kafin ta kuma dago dubanta ta sauke kan Nadia dake tsaye kanta

*Zaki ci ubanki!* shine abinda zuciyar Najeeba ke ayannawa

Na tsaye shi, baya gabana, aurensa baya gabana, aman ko kashin da na yar ya haramta gareki domin aminci ba karya bane! Ta kuma furtawa zuciyarta

Ji take baki daya ta gama muzanta a idannuwan mutanen dake wajen, du wanda ya santa, to fa ya san Nadia

Anmy da baki daya jikinta ya yi sanyi ta kai dubanta wajen Sultan

Irin kallon da yake ramkar kallon jin dadi, irin yanda ya maida hankali a kallon dramar da ta wakana, ko take kan wakana kamar wanda abin ya masa dadi

A hankali ta sada kanta

Ba'a taba hayaniya mai yawa haka a gabansa ba, baka isa ka yita haka a gabansa ba tare da ya maka abinda zai firgitaka ba, aman sai gashi ya yi shiru ya kyale har Najeeba ta fadi maganar da bata so ta fadeta a gaban kishiyoyinta ba, kwarai karara ta nuna bata yi auren da zata yiwa kishi ba!
Me ya sa Shaheed? Me ya sa ka auro aminiyarta? Shin amsa min ka yi dan baka da yanda zaka yi da ni ne ko me? Ni kiwa zan nuna maka ba sarauta ba,, ko me ke kanka ni na haife ka!

Ummu kam da kallo take bin kowa, har lokacin da auntyn Nadia ta karasa ta kama hannunta ta ja ta ta mayar da uta wajenta tana jin inama idan ta wanke fuskar Nadia da mari ba abinda zai faru? To da yau sai ta fafale fuskarta da mari sannan ta yi tirr da ita, bata taba bata kunya ta sakata jin ashe Nadia sakarai ce bata taba sani ba irin na yau, lalle Nadia sakarai irinta babu
Ashe yarinyar da take haukan tsoron ita batama damu da mijin ba? Ga alamu karar sun nuna kamar auren dole ne akai mata?

Zaunar da ita akai

Sai a lokacin ya dauke idannuwansa daga kanta

Kwarai da farko, wani murmushi ne ya subuce masa a lokacin da ya hangi dukan da gannin Nadia ya yi mata, irin yanda su duka biyun suka rikice da ganninta a gabansu kuwa ya bashi mamaki duda ya san Zinaria basa shiri aman bai taba tsamanin kawar tata tsoronta take ba, aman a kan me take tsoronta? A hankalo kallonsa ya koma na son karantar ainahin abinda take ciki maimakun wanda yake fitowa daga bakinta

Murmushi ya kuma saki irin na yake din nan a lokacin da sak kunnayensa suka jiyo masa irin yanda ta yi magana da nuna bata damu da gannin kawarta aminiyarta a matsayin kishiyarta ba, wace suke raba mafarkin kasancewa su kwalin kwal a gidan miji

Dubansa ya maida kan Zinaria, kanta sade yake, sosai an janyo alkyabarta an rufa mata dan kar a ga fuskarta

Tausayinta ne ya ji har cikin ransa, irin magangannun da ta yi kwarai sun bashi mamaki, meye ilar bak'ar fata ne? Bai san me ya sa idan hankalinta ya tashi take barin bakinta ya ringa fadin du abinda ya zo zuciyarta ba
Ya tabata da ba dan mamanta ta rufe mata baki ba, da zata dora wata kalmar mai zafi ne a kan kalamanta, menene a kishiya ne da mata ke tashin hankali dan za'a yi masu? (Han, baka yi rayuwar neman aure da wani bane, a wajen da kake soyaya ranka shi dade)

Kuma kai dubansa ya yi wajen da aka zaunar da Nadia, tsuru Najeeba take kallo hakan har ya so ya bashi mamaki, ta yaya mace zaki yi sake har a ga rauninki haka? Kansa ya girgiza sai kawai idannuwansu suka sarke da na Anmy

Irin kallon da ta masa ya saka shi sada nasa idannuwan wanda hakan ke nufin yana tausarta ne

Matar sarkin agadez ta tsakiya ce ta duka sosai ta kama hular alkyabar nan ta dora saman kan Najeeba,

Kanta kasa ta zagayo ta kama hannayenta, hannunta dayan suka kama ya kasance tana tsakiya

Anmy na kallonsu, sarai ta san abinda zasu yi, ita dai Najeeba bata musa masu ba , binsu ta yi a hankali suka nufi wajen da yake zaune

Sunna zuwa da hannayensu suka kaita kasa ya kasance ta duka a gaban kujerarsa

A sanyaye Zahrau ta ce" Allah ya huci zuciyar Sultan, Allah ya huci zuciyar mai damagaram, Gimbiya Najeeba na neman afuwar daga murya a gaban uban gidanta

A hankali da mamaki fal ramta ta dago ta hangi fuskar Zahrau, iyeah, yaushe ta koyi irin abubuwan nan?
Kishiyarta ce ta budi baki itama cikin kara sada kai kamar yanda suka tsugunar da Najeebar ta ce" Allah ya huci zuciyar mai wukar yanka, Allah ya saka sasauci a hukunci takawa, sannu da karin hakurin halayan mata , Allah ya kara maka lafia Gimbiya Najeeba na neman afuwar mikewa a lokacin da baka bada izini ba

Idannuwansa kawai ya lumshe masu bai ce komai ba suka mike a hankali suka koma

Sunna zama su Zinariama suka mike da ita suka nufi wajensa

Baki dayansu suka zube suma, cike da kwarewa a lamarin bada hakuri da kirari mahaifiyarta ta taushi zuciyar sarki da neman afuwa
Idannuwansa a kan Zinaria

A hankali ya budi bakinsa kasa kasa ya furta" Allah ya sanyaya zuciyar uwar gidan SHAHEED

Idannuwanta ta lumshe jin dadadar muryarsa a kanta, mahaifiyarta kuwa har sai da ta kara jinjina ta kara daga murya tana fadin" Zuciya ta sanyaya Gurnanin zaki, Allah ya kara girma, uwar gidanka ta amsa ta gode rarashi

Da biyu ta yi hakan, wa'inda take so su jin kuwa sun ji, a haka suka koma

Sai da Aunty ta kamata ta mikar da ita, ita kanta kafafuwanta rawa suke, sai wata datijuwar daje gefenta suka saka Nadia a tsakiya suka nufi wajen baki dayansu a tsorace domin basu taba kusanci irin haka da sarki ba, sannan basu san al'adun gidan sarautar ba

Sai da suka karasa suma suka tsuguna

Hannayensu du suka hade kamar sunna adu'a kafin su shiga hadin baki wajen maimaita abinda suka ji ana fada masa

Murmushi ya yi kafin ya gyada masu kansa

Auntyn Nadia ta ringa sauke ajiyar zuciya, a ranta kuwa fadi take" Allah ka sa mu tashi da wuri lafia daga wajen nan,

Gannin basu mike ba ya saka ua rage muryarsa sosai ya furta" ku koma mazaunin ku

Sunna komawa suka zazauna tadar gaba wace a cikinta ne ake fadawa junna magana ta hanyar firgitatun kyaututukan da matayen zasu yiwa junnansu

Wannan tada, zinaria ta san da ita, kuma ta shiryawa hakan, sai dai a yanzu a wajen mahaifiyarta ta kara ninka kyautar dan tana son ta fara kai mari da firgitatun kyaututukan da zata gabatar ba dan komai ba sai dan ta nunawa y'ayayn talakawan nan kudin kansa hawa hawa ne, sannan sarauta fa gado ce!

Yayar ZINARIA ce ta fito cikin shirin wata mahaukaciyar shada ruwan pink, an cancada mata mak'up tana baza kamshi sosai
Da alkyabarta baka mai shara shara wace ta fitar da tsarin gashinta karara

Cike da yanga dauke da jaka ta karasa Tsakiya

Jakar nan ta buda ta duka kadan ta ciro wata katuwar sarka ta zinaria kafin ta hada da chek mai dauke da kimanin kudi cefa millipn biyar biyar ya zama sarka biyu da million goma
Sai da ta dadaga ta nununa sannan ta buda bakinta da hausar buzayen da bata zauna ba ta ce" *Alhamdulilah, ZINARIA na yiwa Amare barka da sauka da fatan sun shigo lafia, Zinaria ta sauki Amare da ruwa sansanya da wajen zama harma da kyauta a ja jari*
Chapter 72 · 0% Book details