← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 138

Sashe 67

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai a yau da ta kalli madubi ta firgita da irin cenjin da ta ganni a jikinta tun daga fatar jikinta, gashin kanta, mamanta, duwawunta, kamshin jikinta kai harta da laushi santsin jikinta sai da suka bata mamaki mai tsananin gaske
Ta tabata a yanzu suturunta ba zasu shigeta ba ta wajen duwawunta da kuma mamanta domin sun kara cika ne sosai mamanta har ya yi girman da zai kai girman mangwaro mai dan girma kasanta kuwa tabas ta fi Niki minaj

Shigar da akai mata doguwar riga ce ta lesh wace aka yi wani irin dinki mai jan kasa daga baya sannan aka dora mata wata irin alkyaba mai ruwan ashh kala mai haske ta fi lesh din haske domin shi lesh din duhu ne da shi

Wani irin dadadan sanyi ne ya ratsa fatar jikinta da wani irin nutsatsen kamshi
Idannuwanta ta lumshe dan rabonta da ta ji sanyi haka na ratsa jikinta tun satotan da suka yi

Ji ta yi sun kamata sun gurfanar da ita zaune kasa sannan datijuwar nan ta karaso gabanta ta kama hannunta na dama ta kara durkusar da ita ta fitar da hannun mai dauke da wani irin kunshi mai shegen kyau a sanyaye ta furta" *ALLAH YA JA DA RANKA, MUN ZO NE NEMAN ALBARKAR AURE, ALLAH YA TAIMAKE KA*

wani irin tsintsinkewa gabanta ya yi ya dagargaje ya fadi hakan ya sa ta fago kanta da sauri dan tabatarwa kanta wani ranka ya dade din ne?

Lokaci daya ta mayar da kanta ta sada sakamakon ido hudu da suka yi da shi, idannuwan nan nasa sam ba alamun hutu domin har yanzu a rikide suke da fitintinnun da Zinaria ke gabatarwa na tayar da hankalinta da ta yi, ga abubuwan dake kansa, ga tunanin auren nan kamar da wasa

Idannuwansa ya lumshe yana jin kamshin da suka zo da shi, wacece mai kamshin nan a cikin su?

Kuma buda idannuwansa ya yi yana kallonsu du kawunnansu a kasa a gabansa, su dukansu jinnin sarauta ne yaushe suka zo? Me suka zo yi?

Sai da ya furzar da huci sannan a sanyaye ya buda bakinsa yana kallon Fadimatu
A hankali ya daga yatsunsa biyu ya yi nuni da wata ambulop yar karama fara karrr sannan ya lumshe idannuwansa ya dan jimke hannun nasa ya dan jinjina mata

Mikewa ta yi ta dauko ta duka ta ringa godiya da abin arziki duda basu buda sun ga meye a ciki ba, wannan shine kyautar da zai mata kafin aure bayan akwatunnanta da sauransu

Sai da ta kara tabata sannan Najeeba ta buda bakinta da take ji ya mata nauyi a sanyaye ta furta" *AN GODE*

da sauri suka kalleta jin AN Gode din da ta ce tamkar wace take magana da wani sa'anta bayan a hardace suka koya mata irin gidiyar da ta dace ta ringa yi masa a gaban mutane

Ta buda bakinta zata yi magana ya daga mata hannu hakan ya saka ta sada kanta ta ringa neman afuwa
Da yan yatsunsa ya nuna su tafi

Du mikewa suka yi basu kamata ba, domin kuwa iya su ya yi nuni da su fita

Tana jin alamun sun tafi ya saka ta dago da sauri dan gannin abinda ke faruwa

A yanzun kam ba iya zuciyarta kadai bace ta fadi harta da ita kanta sai da ta ji zata zube a wajen kafin ta yi gagawar mikewa tsaye nufinta ta juya ta tafi, sai dai ta tsinkayo muryarsa kamar ba shi ba a hankali ya furta" zo

Jikinta ne ya kara daukan bari
Ta juyo tana kallonsa
A zaunen da yake bai motsa ba sai dai irin kallon da yake mata ya isa ya halakata da tashin hankali
Kafafuwanta ta ringa jin sunna kaita wajen da ta tabata zai summar da ita idan ta idasa

Tana zuwa ta zube kasa hakan ya saka dubansa sadawa wajen da take tsugune

Kallo ya kare mata, shi kadai ya san irin hukunce hukuncen da zai mata a rayuwa

Bai ce komai ba sai da ya gama yi mata kakausan kallon da ya sakata jin zata fashe da kuka kafin a hankali ya furta " *TAFI*

ai kamar jira take ta mike da sauri ta fita , tana fita ashe sunna jiranta suka kuma daukan hanya suka koma

Ambulope din suka mikawa Anmy da Ummu dake zaune kafin ta shiga tube mata shigar nan tana mai yi mata maganar shin yaya aka yi ta furta iya kalmar nan a gabansa?

Anmy ta saki murmushi a lokacin da ta gaakudan kudaden da aka rubuta a kan chek, da kyautar gida da kuma kyautar zinarin da aka fadi irin kirar kafin ta mikawa Ummu

Murmushi itama ummu ta yi kafin ta mayarwa Anmy domin sam bata rike komai Na Najeebar dan ba zai yiwu ta diro kai tsaye a yanzu ta nuna itace uwar Najeeba ba

Ita dai Najeeba shigewa ta yi ko tsayawa bata yi ta ga abinda suke mamaki da murnarsa ba, alwallah ta kara daurowa ta zo ta shiga sallah, kuka take har kanta da jikinta suka dume da wani irin zafi da ciwo, fadawa Allah take aa ita bata so kar a daura ........... (HOUM)

*BABAR RANA*

Ranar da zata haukata zukata da dama, ranar da yan jarida zasu samu abin yadawa, ranar da zukatan maza da dama zasu ji wani iri da madaukakin tashin hankalin jin inda ta fada
Lale da yawa zasu ji inama, da yawa zasu ce dama ai yannayinta sai manyan ciki kuwa harda ambasador da soja da likitocinta uwa uba HUZAIFA,
Ranar da labari zai hadu a waje uku, tun daga bangaren ZINARIA, NADIA, DA KUMA NAJEEBA,
Jin labarin daga sama zai gigita da yawa,

.........ku biyoni yar mutan niger

Idan comment ya cikan gida zan yi na gobe, idan bai cikan ba sai nace Allah ya sada mu da alkhairi i.a

*Masha Allah*🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

36

A yau ta kasance ranar asabar ce,
Garin damagaram bai taba daukan harama irin na yau ba
Samari da yan mata, datijai da tsofafi, kar harta yara kanana idan suka samu hanyar fita sun fece zuwa baban filin da ake babar tadar wasan kaho

An shirya wasan kaho da sukuwa takanas saboda auren nan
An yada maganar daurin auren nan ne a gidan redio da TV cewar Sarki zai kara auren yan matala tsala tsala kwaya biyu duda yan matan ba'a fadi ko su waye ba, sai dai maman NADIA da Nadia du sun baza cewar itace dayar, su kansu sun kasa kunne su ji wacece dayar

Gaya kuwa ba sai an gayata ba, domin wajen ya samu halartar manyan baki na mamaki gidan sarki kara cika yake tun a jiya har zuwa yau cikin bakin kuwa harda su *MAI MARTABA SARKIN AGADEZ, DA MATANSA BAKI DAYA, DA YARONSA YARIMA*

Tun da suka zo, GIMBIYA mahaifiyar ZINARIA ta tare a bangarenta suka kile tare da sauran y'ayanta mata suka shiga hada hadar sa ji sa ganni sai dannar Zinaria suke wace take neman ficewa a hayacinta maimaitawa take ba zata iya raba mijinta da sarautar nan da wata halita ba

Yayarta guda kuwa ta fita cikin mutane dan ta samo rahoton dayar kuwa yar gidan waye? Domin tuni Nadia ta tona kanta ita da uwarta wa'inda basu san tana cikin amaren da za'a kawo gidan sarauta ba daidaiku ne domin ta karbi abin da hannu bibiyu, bata taba tunanin ita Nadia zata tare a matsayin amaryar mai martaba, ita zata ga fuskar mai martaba, takan yi daria ta furta" Najee, ina kika shige, yau daukaka ta tardoni a gida ni zan zama matar abokin gabarki, kar ki damu kawata zan shirya ku!

Bangaren Anmy hankalinta ya so rabuwa biyu, sai dai mahaifiyar Najeeba ta kaleta ido cikin ido ta ce" idan har kika yarda shiriritar yarki ta saka maki damuwa to fa ta samu nasara a kanki, ki gane tana kara langwabewa du idan kin shigo ne, ki zo ki kula da baki ki barta ta gama shan karin ruwan, idan lokacin fitar da ita ya yi za'a fitar da ita koda a sume ne a jinginar da ita, ban taba gannin bataciyar ya irin yarku ba! Kun wani rikice dan tana abu nan Abihnta har ni yake fadawa magana wai ina ruwana da ita, han

Murmushi kawai Anmy ta yi, domin a lokacin da aka basu damar su shiga su duka su kara ganninta a jiya ne suka yi kicibis da Ummu, du daburcewa Abih ya yi sai neme nemen kys din mota yake a aljihun rigarsa har sai da Dayabu ya yi murmushi ya kama hannunsa ya ja shi, har ya gifta ta ya juyo ya ja tsaki kamar wani yaro ya ce" an ji kunya, me kuma ya maido ki nan? Ki koma mana wajen neman kudinki, ki barmin y'ata babu ruwanki da ita

*FADA* ta rikice, ta hautsine wajen ya dinke da jama'a, dogarai ne sun sha rawani daidai misali du sun bazu sunna bada wani irin tsaro sai sojojin da suka barbazu suma sunna bayar da tsaron

Tsaye yake a cen sama ta wajen window dinsa mai duhu wanda shi yana iya gannin na waje aman daga waje ba zaka iya hango shi ba

Bashi da riga a jikinsa, ya gama moysa jikinsa ne da wani dan tawul karami yana goge zufar jikinsa yana kallon du wasu shagulgulan dake kai kawo a cikin fadar

Hannayensa masu taurin gaske ya daga ya dan dora a jikin garun ya kara kurawa wajen ido

Tabas ya jima rabonsa da ya ga taro haka, ya tabata Anmy ta bada babar gudunmuwa dan tana aurar da y'a

Murmushi ya yi yana girgiza kansa ya juya cike da kadaita ya nufi bayi da kansa

Ya jima ciki yana wanka da dukan uzurinsa kafin ya fito

Agogo ya kaiwa duba, nan da awa daya da rabi za'a gabatar da daurin auren dan haka sai ya zarce wajen tarin kayansa ya buda ya tsaya yana kallo
Chapter 67 · 0% Book details