← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 138

Sashe 37

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummulkhair da ta bude victago ta lakuto ta nufi wajen kirjinta tana shafa mata a hankali ta ce" ki dai bi a hankali, kar kibiyar ta kasance mai zuwa ta dawo ce

Ummukulsum wace itane ta fi su tsoro ta ce" ni dai dan Allah ki yi hakuri, a bar maganar wata ramuwa dan ba wajen bane, ko dan Anmy ai ya isa ya taka ki ki sada kanki, kinafa ji NAJEEBA yanzu yace auren aunty Zahrau karshen watan nan, ke kin ga Anmy kanta sai da ta zabura ta kale shi hakan na nufin ita kanta bata san da maganar ba bale Abih kuma ya zama wajibi su masa biyaya, ke kina kasa zaki wani ce ke aa?

Da yake ta fi rainata dama yan watani ne ta bata ba shekara ba sai ta ce" Ummukulsum ni abin ya fi maki ciwo dan nace zan rama ko? To na fada dan Allah ki dakeni ki huta mana tunda na ta a abokin tagwaitakarki!

Dawowar Anmy da waya a hannunta ya saka su yin shiru

Wayar ta mikawa Najeeba tana mai tsareta da mugun kallon idan bata amsa ba komai na iya faruwa

Wayar ta amsa da hannunta na hagu tana kallon saman screen din

Wauh na ce a lokacin da na ga wace ke zaune itama tana kallonta
Kallon kallo suke yiwa junnansu, har sai da matar ta dan saki murmushi ta lumshe idannuwanta ta bude cike da isa ta ce" ke yar Mutalab sai uwarki ta gaisheki ne?

Ta kasan idannuwanta ta kalli matar aman bata furta ko A ba

Murmushi ta yi tana yi mata kallo mai hade da madaukakiyar soyaya irin ta d'a da mahaifi
Ita kam ta ina zata bi y'ar tata ta dawo mata yanda take so?
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" yaya jikin ki?

Najeeba dai bata ce komai ba, Anky kuwa bata takurata ba ko amsar da ta yi ai ta yi kokari, hakama yan uwanta

Zahrau ce ta leko tana daria ta daga hannunta ta ce" Mama i miss u

Warcewa Ummulkhair ta yi tana ihun cewa" Mama, ni ke missing din ki

Ummukulsum ta amshe ta ce" mama ba ji ce tagwayenki ba?

Daria itama take a hankali ta dan juya idannuwanta wa'inda sukai wani farr da su gasu da girma masha Allah ga gyaran da suke dauke da shi ta ce" an matana, baku san irin yanda nake missing dinku ba, ina kewarku fiye da tunaninku, ina so na zo na ganku, na rungumeku, na ji me kuke ciki, ina son halartar auren Zahra, ina nan ina yi maku tanadin abubuwan da idan kuka saka baki daya damagaram sai ta girgiza

Bakinta ta tabe ta mike kwonciyarta tana lumshe ido, a kasan zuciyarta kuwa tana fadin" abinda kika fi kauri a kai kennan, abinda ya fi maki ni kennan wato abin duniya!

Anmy ta karasa kusa da ita ta ja bargo ta rufa mata, dan zaunawa ta yi gefenta a sanyaye ta ce" NAJEEBA

Kallonta ta yi da kallo irin na wanda take iya yiwa mahaifiyarta

Dukawa Anmy ta yi wajen goshinta ta yi mata kiss a goshin nata a sanyaye ta ce" ki huta kin ji? Dan ina so mu fita da ku duka gobe in sha Allah

Kanta ta dan gyadawa Anmy kafin ta maida idannuwanta ta lumshe

Su kuwa hira suka sha da mahaifiyar Najeeba wace du wasu abubuwa irin su wani lumshe ido, su shan iska, su shagwabe yannayi baki daya nata ne Najeeba ta kwasa, ba wai tana yi dan ta birge namiji bane, abinda dai ta kara a kai shine ta fahimci yana tsuma mazan sai take kara sakar masu shi

Kayan nasa ya tsurawa ido kafin ya watsar da su cikin kwondon kayan wanki

Kasan shower ya tsaya ya dora hannayensa jikin garun wajen yana jin saukar ruwa a jikinsa

Sai da ya gama ya darje jikin nasa da sabulu da soson wankansa kafij ya fito daure da tawul mai tsayi

A hankali ya karasa wajen miror ya tsaya

Turarensa ya dauko ya yiwa jikinsa bari da shi kafin ya jefar da kwalbar dan ya kare sai wani

Idannuwansa ya dan kurawa ido, yar yatsarsa ya kai wajen da bakin abin ya yi yar kwana tamkar wanda yake saka kwali
An haife shi ne da kwali a idannuwansa, shi kansa baya yiwa kansa kallon tsaf domin kwalin nan na tayar masa da tsigar jikinsa shi yasa baya matsewa mutun duba ko yace zai buda girman idannuwansa a kanka domin bai san yaya zaka ga idannuwan nasa ba

Juyawa ya yi ya ciro wata farar jalabiya marar nauyi sosai ya saka a jikinsa sannan ya saka dan gajeran wando

Wajen bed dinsa ya karasa ya kwonta yana mai adu'ar tsari dukan motsinsa

Rmt din Ac ya laluba ya dauka daga kwoncen ya kara masa karfi ya sada shi daidai kansa sannan ya lumshe idannuwansa

Tunanika ne birjik a cikin kwakwaluwarsa shi har ya yi watsi da abinda ya faru tsakaninsa da Najeeba domin ya ajiye hakan a fagen bata da kunya ne zai koya mata hankali a nitse

Baci ne ya sandeshi ya dauke shi , irin bacin nan wanda ke dan fizgarka sama sama
Irin abin nan dake zaburar da mutun a yayin da irin bacin nan ya zo masa ne ya zowa SARKI

Abin sai ya hade da a lokacin da ta kai masa damkar nan ta saka gwuiwar kafarta ta daki wajen da bai dace kafar tata ta kai ba, hakan ya saka shi kara jin wannan balakin da ya ji wanda da ba dan ya rintse idannuwansa ba a lokacin zai iya kurma ihu ne
A zabure ya farka yana mai kai hannunsa wajen ya damka yana mai rints ido domin sak mafarkin kamar a da gaske ne abin zai sake faruwa da shi

Da sauri ya kai dubansa wajen, idannuwansa ya mayar ya lumshe a cikin zuciyarsa ya furta" azaluma, na jikata da ruwa shine ta dakar min wajen da idan ta kasarani na gama wata takama a duniya ko? Ta Allah ba taki ba macuciya da lamarin maza ya gama bude maki ido!

Kuma lumshe idannuwansa ya yi yana tausar kansa
Bai taba nunawa Zinariya ta zo gareshi ba, ta yi kadan ba zinariya ba bai ga macen da zai je ya lalaba ko ya tura mata yar muryar cewa ta dube shi ba! Idan ta kawo kanta ne sannunta idan bata zo ba ko me zai ji yakan taushi kansa ya tirsasa kansa ne ya dane kamar yanda ya iya danne abubuwa da yawa a rayuwa
..........................................

Wajen karfe goma tuni sunna makeken fallonsa,
Fallon da ya saka yan matan daga kawunnansu sunna bi da kallo, falon da ya gama haduwa ya hade ya harhade

Sunna zaune ne saman maka makan kujerun falon na alfarma, kujerun kansu nishi suke sunna murmusmus a ido domin ba kananun kujeru bane baki dayansu irin na gidan sarakai manyan sarakai

Maka makan Ac din ne ke kara huro sanyi a falon wanda sakamakon zaman minti goman da suka yi har jikinsu ya gama daukan sanyin

Fitar da Anmy ne hakan ya sa dole kowace ta bi tsari na saka Alkyaba

NAJEEBA ta saka wata watsetsiyar atampa ja, an yi mata dinkin sket da riga ne , sket din daga baya an yi masa tsaga mai dan tsayi domin ta haye sama kadan sannan sket din ya kamata daga wajen duwawunta tsam sai ya tafi zuwat bai bude din nan ba
Rigar kuwa an yi mata dinkin zamani, an mata baban wuyan nan ne wanda ke saukowa kafada sannan daga gaban an dan yi yar tsaga an fitar da V
Hannayen kuwa an saka masu roba daga sama sun bude sosai daga cen kasa kuwa sun tsuke sakamakon robar da aka saka

Kanta kuwa dauri ne ta kashe na Zahra buhari

Ta rigaya ta saba da rashin zama fuskarta ba a gyare ba hakama ko fita zata yi sai ta tsuke ta gyara fuskarta tas
Hakama yanzun fuskarta a gyare take da simple mak up, idannuwanta kuwa ta yi masu sabo da dora natural gashin ido masu tsayi sukan karawa idon wani sirrin kyau da fuzga ne

A hankali ta sada kanta ta ce"Anmy, me zai hana mu bari gobe mu yi fitar nan? Duba da bai fito da wuri yau ba

Anmy ta buda baki zata yi magana jakadiya ta yi salama

Dukawa ta yi a hankali ta ce" Allah ya kara lafia, Elhaj Mutalab ya karaso

Kanta ta gyada mata dan haka ta mike da sauri ta fita

Tana fita bata jima sosai ba Abih ya shigo da salama

Murmushi ne kwonce saman fuskar Anmy tana amsawa kafin ta mike tsaye ta ce" yaya shigo zauna mana muma jiran fitowarsa ne muke

Karasowa ya yi ya zauna, yaren baki daya suka hadu sunna gaishe shi da yannayin murnar ganninsa

Hannunsa ya dora a gefen fuskar NAJEEBA ya ce" yaya jiki?

Murmushi ta yi ta dan dora gefen fuskar nata a hannun nasa

Ci gaba ya yi da shafa jelar gashinta dake yawo, dayan hannunsa kuwa Ummulkhair na rike da shi tana dan masaging daga kasa kuwa Zahra ta rike kafa daya tana masaging Ummukulsum kuwa tana daidaita masa ruwa daifai misalin shansa

Zamansa ya gyara ya ce" kin san me nake gani kuwa Anmynsu?

Anmy ta girgiza kai bayan ta ajiye masa abinci a plat domin komai a jere yake

Abih ya ce" sarka DAYABU ya saka aka yiwa yaren nan har shi aman banda NUSAIBA

Anmy ta dan yi turus tana kallonsa ta ce" kamar yaya banda Nusaiba? Me ta yi uta Nusaibar da ya wareta?

Abih ya dan yi murmushi ya ce" na tambayi kannen du sun ki fada min abinda aka yi, koma meye na san mai girma ne, aman kuma sun ki fada min abinda ya faru

Dubansu Anmy ta yi daya bayan daya a hankali ta ce" eyah, eyah, ashe zan ga haka da raina tun kasa bata rufe idannuwana ba?

Shigiwarsa da kamshin turarensa da ya shigo du kuwa da irin yanda dakin ke dauke da kamshin turaren wuta ya saka Anmy waigawa wajensa

Fuskarta ta sada, hankalinta ya tashi jin haka,
Chapter 37 · 0% Book details