← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 138

Sashe 87

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ANMY ta kuma kallon UMMU sai ta ga ta koma wajen Zahrau ta karb'e wayar hannunta ta nunata da yatsa a kausashe ta ce" ZARA MUTALAB , ko ki mik'e ki cire hijab d'inki a maki kitson nan ko na jibgeki na rantse a wajen nan!"

Da sauri Zahrau ta mik'e tana cire hijab d'in, muryarta a raunane ta ce" Ai da wuri yake kira a d'auko wace ta fara kwana b'angarensa, ai da wuri yake kira tun da duhu duhu, *ina NAJEEBANA? LAFIA HAR YANZU BA'A NEMI A ZO A RAKOTA BA KAR DAI A JE ABIN YA MASA YAWA NE UMMU?"*

Ummu ta saki baki gannin zata tona masu asiri dan kawai ta firgice.

Anmy ta kalli jakadiya ta shiga tunanin me zata ce mata? Baki daya y'ayan na nan, Dayabu na hanya uwa uba UMMU, NAJEEBA na iya shigowa yanzu ko idan an jima,
Shin zata yarda ta shigo bayan ta santa da neman fitina ta tada mata rigima a irin wannan lokacin ko zata hannata shigowa ne?

A sanyaye Anmy ta kuma kallon jakadiya dake jiran amsa kafin ta bud'i bakinta ta ce"...🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

45

A sanyaye Ammi ta ce "Ki shigo da ita"

Har ta mike za ta fita Ammi ta kuma faɗin "Ki kai gaisuwata ɓangaren Sultan"

Kuma ɗukawa ta yi cike da ladabi da biyayya ta amsa kafin ta tafi.

Ba'a ɗauki lokaci ba suka shigo.
Wata irin kwalliya ce jikin Mardiyya, ta sha wani rantsatsen lesh an yarfa mata mak'up

Tunda suka shigo hankalinta ya tafi wajen yaran,
Bayan wacve ke goye da Nusaiba kawai take iya hangowa, Ummu kuwa na tsaye ne tana nuna irin kitson da za'a yi wa Zahrau.

Zama suka yi saman kujera sannan suka shiga gaishe da Ammi

Ammi ta amsa masu cike da kulawa tana ɗan satar kallon yaran , sam ba wadda ta yi yunƙurin gaishe da Mardiyya, ko damuwa basu yi da ita ba
Kwarai bata ji daɗin hakan ba duk da mutum shi ke janyowa kansa mutumci ko akasin hakan, amman ai tarbiyyarsu fa?

Sai da ta sadda kanta a hankali ta ce "Allah ya taimake ki, dama kan maganar Abban Nusaiba ne na zo, kwata kwata ya zubar da ni, ya yi block din numbobina ba gabaɗaya da nake samunsa, hatta Mama sai da ta saka a neme shi amma ya ki zuwa, gashi ni ba sakina ya yi ba"

Dan saurarawa ta yi ta dan dago dan gannin shin tana sauraronta?
Gannin Ammi na kallonta da kyau ya saka ta ci gaba da faɗin "Idan laifi na masa tsakanina da shi ai ya ci ace ya yafe, idan kuwa fadana da yara ne ba ruwansa ya fita a ciki domin tsakanina da su ne"

Da mamaki Ammi ke kallonta a kasan zuciyarta kuwa faɗi take
'Ikon Allah, wai ita a gidansu ba'a fada mata ka so mutun ka so d'ansa ba?'

Dubanta ta kuma kai wa wajen Ummu dake dan jijjiga Nusaiba, ko nauyinta bata ji haka take jibgata a baya ta yi ta jijjigawa, a yan kwanakin da ta yi da yarinyar ta matukar sabawa da ita domin yanzun Mama sak take kiran Ummu da shi kamar yanda sauran yaran ke faɗa.

Mikewa ta yi ta nufi wajen
Muryarta a dan dake ta ce "Sannu fa?"
Dakatawa Ummu ta yi ta juyo daga wajen yaran dake ta mata surutu

Ido cikin ido suka kalli juna, ita dai bata santa ba, sam bata taɓa haɗuwa da ita ba, ko hotonta bata sani balle ta shaida ta.

Ba wata shigar firgita mutum ce a jikin Ummu ba, domin riga doguwa ce sakakkiya baka a jikinta
Sai dai yannayin tarin kamalar da fuskarta mai cike da yalwataccen gashi da ɗan murmushi ya saka Mardiyya jin shakkun yi mata magana a gatsai gatsai
Dan haka sai ta dan kakari murmushi ta ce "bani ita na rarrasheta ko zata yi shiru?

Kallon da Ummu ke mata dan ta fahimci ko wacece ita, sarai ta san matar ta hoto amma ko ita bata taba haɗuwa da ita gata gata ba

A hankali ta ringa kunce goyon kafin ta juyo da Nusaiba ta mika mata ita

Da farko idon yar a rufe yake, hakan ya sa ta yo lufff a jikin Mardiyya, sai da Mardiyya ta ce "A'a, bata da lafiya ne? Jikinta zafi haka me yake damunta?"

Jin muryar ya sakata buda idannuwanta
Kallonta take kafin ta fara rigimar sai ta koma wajen Ummu (idan baku manta na Nusaiba yarinya ce karama, ko a haka Mardiyya ta kasance mai yawan zaginta hantararta da yawan faɗa, a rayuwar yanzu ko ɗan naka ya mallaki hankalin kansa sai da addu'a da kawar da kai, bare yar yarinyar da ta samu mai rarrashinta da nuna mata soyayya hakan na iya haifar da son nisantar mahaifiyarta da ta haifeta, karamin abu ne hakan)

Da mamaki ta kalli Ummu, da yanayin shashanci ta ce "ke ko har kin canza uwa ne haka zaki ringa kuka a hannuna?"

Ummu kam wajen ta bari ta koma saman kujera ta zauna tana mai bin Wudiliya da kallo wace ke zaune tana bin kowa da kallo itama

Wani murmushin ta yi ta kuma maida dubanta wajen yaran
Da idannuwanta take gallawa duk wanda sukai ido hudu harara, sai dai a yanayin yanda ta lura sun rigaya sun hade kan nasu na iya shege wato kar wanda ya gaishe da Mardiyya?

Sallamar Dayyabu ne ta saka su duban wajen

Shine ya fara shigowa cike da yalwatacciyar fara'a a fuskarsa
Bayansa wata yar budurwa ce kyakyawa fara tas , ta saka abaya baka har kasa ta yane kanta da mayafinta

Du sai yaran suka shiga murnar zuwansu
Zahrau ta mike tana yafa dan kwalinta cike da nuna kulawa suke yiwa budurwar yayan nasu barka da zuwa

Kasa ta zauna kanta kasa tana murmushi tana dan murza yan yatsunta, shi kuwa yana zaune kusa da Ummu yana mata magana kasa-kasa, haka kuma kannansa duk sun zagaye shi ban da Zahrau da ta shiga hidimtawa bakuwar cike da fara'a

Hannun Bilkisu ya dan doke ya ce" Mairama ki barni da tsegumi wai ba yayarku bace ku je mana ku tambayeta"

Jin abinda ya fada ya sakata dan dago dubanta tun bayan gaishe su da ta yi
Dan murmushi ne a fuskarta kafin ta mika hannu a hankali ta furta "Ku zo"

Sai da suka kara kallon iyayen nasu kafin duk su yi wajenta
Ai kuwa ta ringa cafe hannayensu suna gaisawa duk da ba sakin jiki suka yiwa juna ba amma fuskarsu da mawadacin farin ciki

Baki ta tabe kasa-kasa ta ja tsaki sai kokowa take da Nusaiba dake son zuwa wajen Ummu

Ammi ta kai dubanta wajenta ta ce "Mardiyya, barta ta je wajenta mana, mamanta ce fa, mahaifiyar Najeeba ce"

Da sauri ta dago ta kai dubanta wajen Ummu,
Sam Ummu bata kallonta, hasalima dariya take yiwa maganar DAYYABU na irin rigimar da suka sha kafin budurwar tasa ta yarda ta zo gaishe da su

A hankali ta furta "Na ji dadin jin haka, hakan na tabbatar min da tarbiyyarta, har ma na ji ina zumudin kasancewarta matar yarona"
Tana maganar tana kai hannunta gefen fuskarsa ta dan shafa a hankali sunna dariya a tare

Wani irin abu ne ya tokare kirjinta kokowa take da abinda zuciyarta ke tambayarta, dannewa take dan kar ya fito fili tana kara kallon su UMMU da DAYYABU ga kuma AMMI dake ta sakin murmushi da alama ta manta abinda ya kawo su gidan ko meye. Zuciyarta ce ta ci gaba da fadin 'What? Meye wannan? Wani irin abu ne wannan? Ko dai yar uwarsu ce? Meye tsakaninsu mai karfin da take zaune rashe rashe a gidan Ammi haka? Goye da Nusaiba ga kuma yaran sai wani hira suke uwa wace ta haife su da cikinta?'
Daga dogon corridor din dake hadawa da bangaren SULTAN iso ya ringa shigowa cikin maganar mutun kamar biyu

Da sauri Ammi ta kai dubanta, hakama Zahrau da du wani wandake wajen

Ita ce ta sanyo kai, cikin shigar da ta tafi da ita wato alkyabarta ce sai dai kamshin turaran ba wanda ta je da shi bane, kamshin turaran SHAHEED ne ya fara dukan hancin duk wani wanda ke wajen

Da sauri yayunta suka yo kanta, domin ja ta yi ta tsaya tana mai jin kunyar kallon su ido cikin ido
Wani irin farin ciki ne ya lulube zuciyar Ammi a lokacin da ta fahimci komai
Ummu ta sadfa kanta tana murmushin cin nasara

DAYYABU ne ya mike shima cike da farin ciki ya yi wajensu

A hankali suka kamota suka nufo ciki da ita
Budurwarsa da kallo take bin su, tabbas yau ta kara yarda da irin soyayar dake tsakaninsu, cike da mangari take dubansu, a ranta kuwa ji take inama ace sune haka? Ita bama yan uba bane aman ba wani kulawa da junna da suke da yan uwanta
A ranta take jin zata dauri niyyar kusantar yan uwanta koda kuwa ba zasu kulata ba har su samu fahimtar juna

Kanta a sade yake baki daya yau kunyarsu take ji, ji take duk sun gane abinda ya sameta hakan ya sa ta kasa hada ido da su sai kara sada kanta take

DAYYABU ya ce "Ke wai menene?"

Jakadiya da babar baiwar bangaren SULTAN ne kawunnansu sade JAKADIYA ta furta" Allah ya ja da rai , Allah ya taimake ki , Sarki na gaishe ki, yana mika sakon gaisuwa da godiya, yana neman afuwar jinkirin zuwan GIMBIYA"

Ammi ta kara yin murmushi kafin ta gyada masu kai suka mike suka fice

Mikewa UMMU ta yi ta karasa ta kama hannun Budurwar DAYYABU

Cike da kulawa ta mikar da ita tsaye ta kara matsota kusa da Ammi sannan ta dan dago habarta a hankali ta ce "Allah ya albarkaci rayuwarki yarinyata"

Kanta kasa tana kara sadawa domin ya sanar mata mamansa ce, cike da jin kunya da kaunar Ummu take kara sada kanta
Chapter 87 · 0% Book details