← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 138

Sashe 111

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gannin numfashinta ya dawo, hasalima baci take yi mai nauyin gaske wanda daga shi ne komai zai saketa ta farka ya maido dubansa wajen AMMI da ta aiko masa da tambayar da ya zama wajibi ya amsata

Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" EH ba'a rufe wajen, haka ake barinsa ya bushe dan kansa ko ruwa ba zai taba wajen ba.
Dan shiru ya yi na dan lokaci kafin ya dora da fadin " Ba'a taba raba gidan sarauta da abubuwan tashin hankali, zagon kasa, munafurci, hade hade, fitintinnu, rigingimu, da dai saransu, ciki kuwa harda kisa,
Wanin kan tsinci kansa ne a wajen da bai dace da shi ba, wanin kuwa yakan kawo kansa wajen ne dan a ganninsa ai nashi da wani waje da ya fi nan din, dama dan irin rayuwar aka haife shi.

Dubansa ya kai wajen UMMU dake rungume da NADIA, zuwa yanzun sun rage mata nauyin suturar dake jikinta sosai dan ta sha iska, hakama ya kai kan AMMI dake rungume da NAJEEBA wace du ta makalkaleta idannuwanta lumshe tana kwonce a samanta sosai sai ajiyar zuciya kawai take saki,
Sannan ya kai kan Zinaria, sai ya ga sam ba wani yannayi na damuwa ko alhinin gannin yar uwarta kwonce sheme sheme a halin rai ko mutuwa, hasalima dan girgiza kai take irin idan mace na cikin neman balakin nan

Ya kuma saukewa a kan iyayen Nadiar, mahaifiyarta na kusa da bayanta, tana rike da hannunta cike da yannayi na tashin hankali, mahaifinta kuwa kansa a kasa ya dan dafe kai malunmalun din jikinsa a dan tatare, hularsa ta yi gaban goshinsa kadan.

A hankali ya ce" AMMI, kwanaki an kashe Bintu ta hanyar saran maciji, shine a yau ya sari kafar Nadia,
Dan sasautawa ya yi ya sada kansa a hankali ya furta" Ina cikin zargin mutun biyu ne, duda na san cewa zato zunubi ne sai dai na fada a wannan zaton ne bisa hujojina, mutanen nan kuwa sune *Amintacena da kuma sarkin Bulala*, kara sada kansa ya yi kafin ya dago ya sauke idannuwansa a kan Zinaria ya ci gaba da fadin" faduwar gaban kar a je da iyalina a ciki ya hanna min gannin amsoshina a fili, sai nake ta zagayewa ido rufe sai na samo hujojin dake hada matata da shi, koda kuwa ya kasance tsoron saurayinta, koda kuwa ya kasance bawa a gareta a yanzun, aman kiri da muzu na kasa samun kakarfan dalilin da zai iya hadata da shi a talatainin dare a wajaje uku, harda mahaifiyarta,, me suke fada? Me suke amsa? Me suke aiwatarwa? Meye tsakaninsu da shi? Shin kishi ne ya rufewa iyalina ido har ta kaita haka ko son zuciya, ko kuwa ramuwar na shiga tsakanin soyaya da soyaya ne? "
Ya karashe yana mai kara son dole ta dago idannuwanta da ta shiga wuwurgawa a tsorace dukan alamun rashin gaskiya ya gama bayana a tare da ita , wanda hakan ya sakata inda inda harma ta dauki magana a firgice cewar " Ni dai ba abinda na aikata "

Idannuwansa ya rintse sannan ya bude ya kalleta, hakama dukan mutanen wajen,, a takure a birkice , a wahalce ya ce" Shin na kama sunna a furucina ne a nan? "

Gannin ta sada kai baki daya jikinta ya kwashi rawa sai kawai ya mike tsaye, ransa bace ya shiga kai kawo

Juyowa ya yi murya a kausashe ya ce"

😁
[3/31, 11:30 PM] BAK'A CE: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

56

Juyowa ya yi murya a kausashe ya ce" shin kin aikata abinda zai sakani a cikin halin tashin hankali, kunya, matsanancin bacin rai? "

Kuma dago dubanta ta yi, baki daya jikinta bari yake ta rasa ina zata kalla, gani take ko'ina na dakin ya zama idannuwa ne, baki daya ta ringa gannin tamkar an tsatsarata a gaban alkali ne, duda kasancewarsa miju a gareta wanda ta yi rayuwar shekara da shekaru da shi aman sai ta tsinci kanta da kasa kallonsa sai tsabar tsoronsa da ya rufeta ta shiga barin jiki baki daya

Kai ya dan juya a hankali ya juyo dubansa kanta a lokacin da ya rage tsayinsa

Da dan karfi, zuwa lokacin muryarsa ta fara amayar da tsarin dake cikin zuciyarsa, tamkar zai hadiyeta danya dan bacin rai ya ce" Zaki budi baki ki bani amsa ko sai na aiwatar da abinda zai tayar da hankalin kowa a nan? "

Da sauri AMMI ta dora hannunta na dama ta saman kan NAJEEBA da ta cusa kanta cikin jikinta sakamakon irin yanda amon muryarsa ya yi mata rashin dadi a cikin kunnayenta

AMMI na shirin yin magana suka ringa jin maganar Nadia a firgice sannan muryarta a shake, sai ta shiga dan harbe harbe irin zata tare wani abin sannan ta kwala razananen ihun da ya saka baki daya akayi kanta

Ido rufe take fadin" kar ya sare ni, ka dauke min shi zai sare ni, walahi ba wanda zan fadawa, tsoron maciji nake ka kama shi yana lauye min kafata innalilahi wa'ina ilaihi raj'une wayo Allahna, wayo zai kashe ni "

A rikice mamanta ke ta girgiza hannunta dake cikin nata tana kama sunnanta sai dai kamar bata san ana yi ba

Da sauri ya duko da wani abu a cikin kofin glass da ya jika ya dan yi gyaran murya hakan ya sa UMMU bashi damar kama kanta

Bakinta ya gumtse da hannunsa sannan ya dura mata abin nan ta hancinta hakan ya saka baki dayanta ta yi wani irin tasowa a gigice sannan ta koma ta zube ta shiga amai ta hanci ta baki
Lokaci daya kuma idannuwanta suka bude jajajir da su tana ta zubar da hawayen wahala baki daya jikinta rawa yake tana bin dakin da mutanen dake wajen da kallo

Wani irin kuka ne Zinaria ta fashe da shi gannin Nadia ta tashi,
Ba wanda ya kula domin Nadiar du aka fi baiwa hankali wace gaba daya jikinta na rawa sannan ba karfi ta shiga fadin" Ban fada ba ko? Bai bari ya sare ni ba ko? Ba zan tona asirin ba kar ya kashe ni dan Allah "

Najeeba dake kallonta tana jin hawaye na ziraro mata daga gurbin idannuwanta zuciyarta cike da tausayinta, ta san za'a rina ne irin tsoron NADIA bare wannan abin ita kanta ta tsorata, ba zata manta ranar da ta ganshi yana ta damukar maciji ba, sai kawai ta shiga tsoron ko dai shima macijin ne?

Sai da ya yi iya yinsa sannan ya dan sasauta muryarsa ya shiga kiran sunnanta

Kanta take girgizawa tana maimaita ba zata fada masa ba

Mahaifiyarta ce ta kama hannunta ta rike a cikin nata da kyau ta ce" Nadia, kale ni, na zo, na zo fa, ba na fada maki zan zo ba? Kin ganni ni ce, fada min meye? Me kika gani, me ake fada? Idan har kika ci gaba da boyewa kin san da sannin ba barinki zai yi ba, domin kuwa ba zai taba yarda cewar kin rufe masa asirinsa ne, zai dauka cewar kina son tona masa a kowani irin lokaci, ki sani da ba dan Allah ya yi kina da sauran numfashi ba da yanzun an jima da goge babinki a duniya, ki sani kafin ke an kashe wata, idan kuma kikai shiru kema zaki bita, Nadia koda kuwa Allah ya yi wannan shi nr hanyar da zaki mutu kin fi so ki mutu ba tare da kin fadi abinnan ba? Bale da izinin Allah an kare, ba wanda zai kuma taba ki, ki buda idannuwanki ga mijinki, ga mahaifiyarsa, ga mahaifinki, ga yan uwansa da iyayensa , ki fadi koma menene"

Nadia ta dora kanta saman cinyar mahaifiyarta ta rintse idannuwanta, ta ce" Amintace ne, da kuma wannan mai rike katuwar bulala kusa da Sultan idan an zo shara'a, su ne suke zance, shi wancen ya ce shi dai baya cikin maganar kisa, abinda yake so kamar yanda aka hana masa jin dadin aure shima ya wayi gari Sultan baya iya jin dadin aure..........

Sai ta fashe da matsanancin kuka ta dora da fadin", shine Amintace ya ce" kamar yanda ya katse masa dukan farin ciki, ya dawo ya dauke shi a matsayin dogari ya ajiye komai nasa na farin ciki, to lalle shima sai ya kai ga ransa, kafin nan sai ya cikawa Gimbiya burinta na son raba shi da kowace mace ko ta halin kaka sannan ya kashe ya kashe Sultan"

Wata irin faduwar gaba NAJEEBA ta ji, har ta yi gagawar kallon SHAHEED dake tsugune kusa da Nadiar yana kallonta tamkar TV

Da sauri Zinaria ta sauko kasa hannayenta saman kanta ta ce" Na san a duniya idan akoy abinda na fi tsana shine mijina ya rabi wata macen, burina koma wacece ta bar min mijina koda kuwa mutuwa zata yi, aman ban taba gigin kashe kowa ba, ba ni nake kashe masa mata ba, ban taba zuwa dan kashewar ba, na san bakina na furta kalamai aman ban taba gigin kashewa ba, kuma haduwar da nake yi da shi ba wani abu bane sai taimakon da yake kawo min ba dare ba rana cewar na aikata ko na zubawa Sultan a abinci hakan zai saka ya tsani matan da ya aura, ni ban san maganar maciji ba, banma san cewar wai har ta kai shi ga haka, tabas ina da matsanancin kishi, ba zan iya raba mijina da kowace mace ba, aman ban taba aikata kisa ba....." ta karashe tana mai fashewa da matsanancin kuka

Kamar wace aka kunna ta kuma zabura ta dora da fadin " kuma a jiya a jiya kirana ya yi, bamu hadu ba yake ce min zai saka ni farin ciki yau, zai fara rabani da daya kafin dayar, ni ban san nufinsa zai kasheta ba "
Chapter 111 · 0% Book details