← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 138

Sashe 102

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani tsakin ya kuma yi a hankali sannan ya mike ya shiga cire rigar bacin da ya saka ya koma bayi
Sosai ya ringa zubawa kansa ruwa sannan ya fito ya zauna saman kujera da karamar wayarsa a hannunsa, shi kadai ya ringa tunani shin kiran AMMI din ne zai yi ko me? Mtsssssss han hm,
A hankali ya ringa jin ransa ya fara bacewa sakamakon wani tunani da kalamanta da suka fado masa a ransa
Na tsane ka! Bana son ka! Ka sake ni na auri masoyina! Ni bana son farin mutun Huzaifana nake so!
Idannuwansa ya rintse da dan karfi a lokacin da ya ji wani abu mai karfi ya soke shi a kahon zuciyarsa, kamar da wasa ya ringa jin abin ba dadi a ransa harma ya tsinci kansa da fadin" *Yanzu fisabililahi me ya yi zafi a maganar nan da har zan ringa tunota ina jin tamkar wani mai ciwon athsma zuciyata na tafarfasa bayan na san gaskiya ne tana da saurayinta aka raba su ai kau?, kuma shine hankalina zai ringa tuno min shirmen nan? Idanma bata so na ai inada masu so na! Nima kuma ai ba son nata nake ba!*
Lebensa na kasa ya kuma dan cijewa, da gaske zafin maganar yake ji kamar a yanzu ta fada masa
Sunnan Huzaifa ya yi masa katutu a zuka yana jin wani irin daci a kan sunnan da wani tunani daban
Gannin zai cutu ta hanyar tinane tinanen nan sai kawai ya nemi kusanta kansa da Allah ta hanyar dora nafila, domin kuwa ba zai yarda yana ji yana gani kamar wani yaro karami ya tinga tino maganar yarinyar nan da bata jin magana mai fadan tsiya gabansa na faduwa haka kawai!

Morning people😁, ga breakfast😌🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

52

Tun karfe bakwai su Najeeba suka gama kitson nan, kitson da akai masa wani irin kannanun tsinta har sai da Zahrau ta ce yanzu Najeeba haka kikai min kannanun kitson nan wa zai tsefe min?
Sai kawai Najeebar ta yi murmushi abinta ta janyo sabuwar wayarta IPhone da yaya DAYABU ya kawo mata a jiya ta kunna
Whatsup din da ta riga ta yi installed ta shiga, tarin numbobin mutanenta da take yiwa gyara wa'inda Habu dan daudu ya tuturo mata ta shiga saving kafin ta yi message daya mai dauke da gayatarsu gidan Mai Damagaram cewar saloon dinta ya koma nan, za'a ci gaba da aiki kamar yanda ake budewa a da, da sasafe sannan a cika dare kafin a rufe, daga kasa ta saka sunnanta da kowa zai iya ganewa kafin ta fita a whatsup din

Instagram ta shiga ta yi posting din hotunnan talar kalolin mak'up din da take yi masu ita da yan uwanta sannan ta dora da albishir din dawowarta
Hakama ta shiga Facebook da tsohon cmpte dinta shima ta yi posting din bayani wa mutanen da suke hira a ciki
A kwoncen nan hankali kwonce ta ringa aikinta ta hanyar posting din tarin hotunanta masu matukar kyau da tsari,
A haka take samun tarin tambayoyin mutane masu son sannin wai da gaske tana gidan sarki? Wai da gaske Mai damagaram ne ya aureta?,
Sai tarin masu turo mata invitation din son ta zamo kawarsu a Facebook
Cikin sabon posting dinta harda numberta na whatsup wanda ta jadada ga mai son kwaliya da gyaran jiki yana iya tuntubarta a number ta tura
A haka ne wasu daga cikin tsofafin samarinta suka ringa bata nishadi ta hanyar turo mata habaici, zata karanta ne ta yi daria kafin ta yi block din mutun ta je ta maka numbersa a black liste
Number Aida ta dannawa kira

Kamar wace ke jira ta daga tana salama

NAJEEBA ta ce" Aida, goben in sha Allah ku fito da wuri fa, yanzu su aunty Zahra sun je su ga yanda aka yi wajen, ni ban je ba in sja Allahu sai goben, ina so ku fito da wuri ku yi dukan gyare gyaren da ya dace kafin na fito domin na tabata wajen nan namu sai ya cika ko dan masu son gannin kwakwaf"

Da sauri Aida ta amsa cike da ladabi kafin su kashe, itama ta shiga kiran ma'aikatansu tana shaida masu sakon mai gidansu inda suka cika da farin cikin tashin aikinsu kai da fata ga mai gidansu a gefe gasu a fada, sukan hasaso yanda abin zai kasance ne, sun tabata ci gaba ne

Isashen Baci ta samu a lokacin da yan uwanta suka yada zango a saloon dinta
Sosai wajen ya mugun tsaruwa ya birge su, haka suke yiwa wajen vidio cike da mamakin irin tsarin ginnin da akai a dan kankannin lokaci aka shake shi da kaya cikin tsari

Kaya dai gasunnan, an zuba sai fatan samun ribarsu

Da farin ciki suka yada zango dan yiwa Ummukulsum gyara tsakaninsu har sai da kusan yama sannan suka firfito sukaiwa masu tsaron kofar salama domin kuwa wannan karron bama dogarai AMMI ta saka a kifar shagon NAJEEBA ba, haka kawai tsoron dora dogaran take dan haka ta tura takarda wajen commissioner yan sanda aka turo mata mutun biyu ginanu ta ware masu mota daya da dukan abibda zasu bukata hakan ya sa su kansu farin cikin wannan aiki domin kuwa ci gaba ne suka samu mai girma

Vidion kawai take ta kallo tana karawa, sai wani zumudin zuwa ta gani ya shiga zuciyarta, wata irin kaunar iyayenta ta kara shiga cikin zuciyarta hakan ya sa cike da farin ciki ta duka har kasa ta shiga koro masu adu'o'in gamawa da duniya lafia da dukiya mai albarka

Da farin ciki Ammi ta mikar da ita ta ce" Najeeba, bafa mu mukai abin nan ba, wannan din da kike ganni daga mijinki ne domin da na kai masa maganar ne ya samu mai zane ya zana yannayin ginnin ya zuba ma'aikata sannan ya zuba kudin kayan da za'a zuba a cikin"

Sai ta ji abin wani bako a wajenta, aman kuma farin cikin da take ciki ya hanna mata jin abin sosai din nan sai kawai suka ci gaba da farin cikinsu, ita kanta UMMU ta sha mamakin wajen, lalle an dankara dukiya ba laifi sai adu'a da fatan a mora

Zama sukai sunna hirarsu domin yama ne

Hanyayoyin dake jere su uku ne aka shiga kokarin bude daya da kys hakan ya sa suka dan dakata dan gannin ko waye sai dai ba dukansu ba,

A hankali ta fara leko kanta kafin ta sanyo kafarta muryarta kasa kasa ta yi salama tana karema mutanen fallon kallo
Dukan Alamau sun nunna a tsorace take da shugiwa wajen hakan ya sa take ta rabe rabe har idannuwanta suka sauka kan NAJEEBA da ta dago dubanta daga kan wayarta tana amsawa mutane maganarsu ta sauke a kanta

Da sauri Nadia ta sada kanta haka kuma da dan sauri ta karasa wajen su UMMU ta duka har kasa harta da muryarta na dan rawa ta shiga gaishe su ta hanyar fadin" barka da safia mama"

Ummu ce ta saki murmushi ta mika hannunta ta kama na Nadia , da kulawa ta ce" ki karaso daga nan Gimbiya, barka da yamaci"

Baki daya ta kasa samyn nutsuwa ko sakewa, du tsoro ne bayane karara a fuskarta, yau tun da safe take shan gumurzu da kanta kan shin zata zo ne ko kar ta zo? Gashi dai ba yan rakiya , ita daya zata zo, a yanzun da maman Najeeba ta kama hannunta sai ta jara jin tsoro, itafa tsoronsu take gaskiya

Dosanuwa ta yi kanta kasa ta shiga gaisar da su daya bayan daya

Ga mamakinta sai suka ringa amsata da kulawa, har tambayarta UMMU ke yi yaya bakunta fatan komai lafia bata da wata matsala

Ajiyar zuciya ta sauke ta jin sanyi sanyi a ranta, dan kuwa sai da auntynta ta rakota har kofar ta turota kafin ta iya shigowa domin zuwanta uku har sai da ta sha stop diarhee tsabar rikicewar da ta yi dan kawai ta saka tsoro da tunanin idan ta yarda ta zo zasu hadu su yi mata jina

Baki dayansu sun amsata, hakan ya sa a hankali ta dago dubanta dan satar kallon NAJEEBA

Sai da gabanta ya kuma tsinkewa ya fadi, da sauri ta sada kanta kasa ta rike hannunta da dayan hannun nata tana fatan Allah ya fitar da ita lafia,
Gata dai zaune itace farar mace kaf a wajen nan aman baki daya da ta sauke dubanta kan Najeeba sai ta ji ta muzanta, munnin kanta ta ringa ganni a bayane, irin yanda NAJEEBA ta kara zama ne ya bata mamaki, a gaskiya ta kara zama wata irin babar yarinya, gashi dai ba kwaliya ko dis a fuskarta, sannan suturar jikinta doguwar sakakiyar riga ce irin ta shan iska, kanta kuwa a kunce yake ba kitso sai tasubala da ta soka a ciki da alama tana shirin gyara kan ne, tarin gashin nan nata sai ya yi uwa tukunya a saman kan nata hakan ya sa gaban goshin ya kuma yin luflufluf
Abinda ya kara kayar mata da gaba ido hudun da suka yi, irin kallon da Najeeba ke binta da shi ba zata iya fasara ko me ke cikin zuciyarta gane da ita ba, kamar mai yi mata kallon ta bata mamaki, ko macuciya, ko zata hadu da ita, hakan ya sa ta ringa jin fitsari na mintsinar mata mara

A hankali ta kara rage tsayinta bayan ta dan mike ta yi masu salama

Da mukawa Ammi ta yiwa su Ummu magana cewar su yi mata rakiya

Ai kuwa da ido NAJEEBA ta bi su har suka bacewa ganninta suka shige lungun da zai sadata da bangarenta

Bakinta ta tabe a hankali ta mike tana mai jan tasubalarta daga kanta tana kwonce daurin da ta yiwa gashinta ta nufi cikin dakinsu

Du da kallo suka bita, sannan a bayane AMMI ta saki murmushin da ita kadai ta san ko na meye, Zahrau kuwa ta mike ta bi bayanta dan tana son ta kama mata su gama hada abinda zata tafi da shi gidanta
.................................. ..........
Chapter 102 · 0% Book details