← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 138

Sashe 59

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya san da sannin cewa ba zai kubucewa auren yar gidan Mutalab ba domin an rigaya an fadi maganar, abinda yake son bakinsa ya buda ya fada shi ne" *NA ZABI UMMULKHAIR* , sai dai lamari na kasancewarsa baba a wajen na mulki ya saka shi harshensa yin nauyi
Gannin abin yake wani iri,
Ba zai iya buda baki ya furta masu zabinsa ba domin shi, shine mai danne zuciyar wasu, shine mai daukan dukan wasu, shine mai shanye damuwar wasu
Abu daya ya san zai yi shine, zai roki cewar a saka auren da za'a masa tamkar wani yaro da zabinsa shima
Mahaifinsa ya masa auren fari
Ya yi na biyun da kansa ba'a je ko'ina ba ta rasu
Gashi mahaifiyarsa zata masa auren uku da matar da shi kansa yake cikin faduwar gaban kar ta masa zabin da zai saka shi mutuwa dan bakin ciki
Yana so a bashi damar daukan mace biyu a rana daya, zabin da suka yanke da wace zai zabowa kansa ya aureta a cikin sirri
Sam Zinaria ba zata iya da lamarinsa ba, so take ta kashe masa lamari yana da karfinsa da kokarinsa haka kawai
Auren da za'a daura masa kuwa idan Ummulkhair ce itama me zata iya masa? Yarinyar da shekarunta duka duka ba zasu zarce ashirin da hudu ba,?
Sam baima kawo maganar idan kuwa Najeeba ce ba, sai dai kura masu idon da ya yi wanda hakan ya saka Anmy sanyaya muryarta ta kara kallonsa ta ce" SHAHEED, ko kaima ba zaka auri y'ata ba?

Da sauri ya kalleta, sai kuma ya maida dubansa wajen DAYABU

Kansa ya kara sadawa a hankali ya buda bakinsa ya ce" ko wani zabi kukai min, in sha Allah zan yi biyaya
Sai dai, ina da wani muradin auren wata yarinya, ina fatan za'a hada su biyun a rana daya

Namijin duniya kennan, haka Dayabu ya fada a kasan zuciyarsa

Abih kuwa murmushi ya yi a fili ya furta" wannan ai abin murna ne, Allah ya tabatar mana da alkhairi

Su duka da amen suka amsa kafin su mimike Dayabu ya nufi dakin Anmy da Nusaiba dan ya shinfideta domin ba zai kula kannen nasa ba, ya kula idan ba ya nuna masa da zafi zafinsa ba zasu kawo raini a lamarin

A lokacin da suka zo tafia gida sai Abih ya shiga motar Dayabu

Har ya tayar ya fara tafia Abih ya yi murmushi yana girgiza kansa ya ce" ina hangen rigima a wajen yan biyuna, NAJEEBA, ko UMMU? sai dai da son kai irin nawa sai nake jin bana so a kara yi masu kishiya duda na kasance ni ina balawa mata tikitin zawarci bama na basu damar yin zaman kishin

Dayabu ya yi murmushi ya ce" Abih, ka manta Ummu, sun yi zama da maman Bilkisuu fa

Sai da ya lumshe idannuwansa a lokacin da ya ji sunnan *UMMU* mahaifiya a wajen NAJEEBA, shi yakan kirata da UMMU, sauran kuwa sukan ce mata mama
Murmushi kawai ya yi yana tuna lokacin, zamanin nan ya kasance tamkar wani zaburaran doki a tsakanin matan nan biyu
Ya ga rayuwa ya yarda cewa mata sunna suka tara
Murmushi ya yi a kasan zuciyarsa kuwa fadi yake" me ya yi zafi haka da aka guje ni an matana? Na kai zuciyar cikin duhun da ta kasa yafe min?
.............................................

Ba yanda bata yi da dogaran dake tsaron kofar bangaren ZINARIA kan su barta ta shiga tana da sako wajenta mai mahinmanci, sai dai sam suka ki amoncewa domin ita da kanta ne ta nuna ba zata karbeta ba tana hutawa
Haka dole ta samu ta kwana gefen fulani domin idan dare ya yi haka ba mai fita daga fada sai da kwakwaran dalili

.............................................
Sam bata samu ta rintsa ba, sakamakon maganar yar uwarta cewar ta saka Anmy a cikin bacin rai
Idan ta juyo daga kan gadonta ta hange su sai ta ji uwa ta je ta cicije su ko zata huce, sai kawai ta ji baki daya kewar yayarta ya hana ta rintsawa domin ta tabata da ita ce da ba zata taba yi mata fushi haka ba

Suma bangarensu sun matukar yi kokarin gannin sun watsar da fushinta gefe, domin idan har suka biya tabas zata saka su a damuwar da zasu kwana sunna kuka ita kuwa da safe ta warware ta yi tafiyarta!

Kiran salar fari a kunnayenta ya sauka
Dira ta yi daga gadon ta yi bayi ta dauro alwalah
Sai da ta zo ta saka doguwar riga saman ta bacinta sanann ta yane kanta ta shiga gabatar da sallah

Tana nan zaune har aka kira sallar asuba ta kuma gabatar da ita cikin nutsuwa ta shafa fatiha da sauri ta mike ta yi bangaren Anmy bata kula yayun nata ba

Tana zuwa ta shige da salama kasa kasa kafin ta karasa da dan saurinta wanda ita ganni take sauri ne take yi ta duka gaban Anmy wace ta gama sallah tana jan carbi

Kanta a kasa tana jin hawaye na son zubo mata ta kamo hannayenta ta dora a gefen fuskarta a sanyaye ta ce" Anmyna, wai da gaske na bata maki rai wai har kin kwana baki yi baci ba?

Anmy dake jin kaunar yar a ranta ta ce" in ji wa?

Najeeba ta ce" ba aunty Ummu bace ta fada?

Dan murmushi Anmy ta yi jin ta ce da ita auntu Ummu, yau ummun ce auntyn,
Kanta ta dan girgiza tana murmushi ta ce" aa, ma baby girl ba zata bata min ran da zan riketa haka a zuciyata ba,
Me ya samu idannuwanki suka kunkumbure haka?

Murmushi ta yi ta ce" ban yi baci bane Anmy

Anmy ta kara shafa gefen fuskarta a sanyaye ta ce" tashi ki je ki kwonta cen ki huta maza

Mikewa Najeeba ta yi tana jin hankalinta ya dan fara kwonci dan yannayin da Anmy ta nuna mata ta tabata an bar maganarta

Doguwar rigar ta cire ya mata sauran wata yar rigar baci baka wace bata idasa rufe cinyoyinta ba sannan daga saman mai gidan mama ne wada ake kira rabin nono ya kasance saman a bultse suke rabin ne suka rufe

Ba abinda ya shafeta dan ta san ba mai shigowa bangaren Anmynta, kuma gaban Anmy kuwa zir ne kawai bata yi

Hayewa ta yi saman lafiyayen bed din Anmy mai sansanyen kamshin turaranta ta yi kwonciyarta tare da rungume yar kanwarta dake ta baci
.........................................
Kamar yanda ya saba da duhu duhu yake shiga dan gaisheta
Hakan ne ya faru, a lokacin da ya daga labulen dakinta ya sanyo kansa
Idannuwa masu neman fitina suka sauka a kan fitsarariyar yarinyar nan wace ya yi mata kallon shari'a daya tak ya yi gagawar cire idannuwansa yana jin wani nishi na kwace masa kamar mai cutar athsma

Da sauri ya saki ya juya ba tare da ya shigan ba, domin gani yake sam bai dace ya shiga a irin wannan lamarin da mace ke kwonce da irin wannan shigar bayan ba muharamarsa bace!

A wannan rana Najeeba bata fita saloon ba, sai da aka yi salar magariba ta fito cikin shirin abayarta lurub har kasa ta cewa Anmy zata dan leka ta dawo a tsaitsaye

Da adu'a ta bita tana mai yin dan murmushi
Irin yanda yarinyar ta fi sauran yan uwanta kulawa da ita ya saka take mata so daya tak da babu irinsa
Kwana bakwai dai suka dauka zasu sake zama su dukansu tana adu'ar Allah ya yi zabi na alkhairi

Tun da ta zauna a wajen yau ya fahimci halin da take ciki

Shima zaunen da yake hotunnan tsala tsalan yan matan da aka turo masa ne yake bibiya yana son gannin wace zata iya da shi?

Kuma dago shanyayun, lumsasun, idannuwansa masu shige da na mashaya da kuma dauke da kwali ya yi ya kai dubansa a kanta a karo na bakwai
Haushinta yake ji sosai, ta zo ta wani zauna masa a wajen da ya rigayeta kamawa a nan yake zama, bayan yana cike da haushinta na har wani ta ja mahaifiyarsa na hada sunnansa da nata, yo shi Allah ya tuba idan aka ce za'a aura masa wannan yarinyar a ranar zai cire rigar sarautar ya je da gudu ya tari katuwar mota ta murje shi da ya ga takaici! Me zai yi da masifafiya, yar balaki, balagazar mace? Ai shi auren nan da zai yi na hutu ne ba na jazawa kai balaki bane!

Sai da ya dani zuciyarsa kafin a sanyaye ya furta" *wa ya taba ki? Sai nake ga hankalinki tamkar ba a kwonce ba, hakan kuwa kwata kwata ya dauke min nutsuwata*

Dagowa ta yi tana kallonsa, yauma da alama ya yi gudu ne dan da kayan gudun a jikinsa sai mahaukacin basket din takalmin dake kafarsa wanda yannayinsa zai tsadanta maka tsadarsa
A hankali ta cire kanta ta dan daga kanta tana kallon taurarin wajen
Muryarta a sanyaye itama ta furta" *ina cikin tsaka mai wuya ne, ashe haka zaman juran amsa yake? Ina cikin gararin rayuwar da kila wa kala ne idan har zan kai labari, domin kuwa da na yarda da abinda zai iya kasancewa da ni gwara a ce bana duniyar!*

Da matsanancin mamaki yake kallonta, aurensa ne take fadin da ya kasance a kanta gwara ta rasa ranta? Ita din wacece da har take tunanin tana da girman matsayin da shi zai yarda ta amsa sunnan matarsa? Ashe aurensa zai iya kuntata mata rayuwa har haka? Tabas da ace zai iya da ya je da kansa ya roki a aura masa ita ko dan ya ringa kallon yanda zata yi har ta mutun
Sai dai ina, irin yanda yake jin kyankyaminta ba zai iya wannan kasadar ba

Sai da ya dan cije lebenta na kasa kafin ya furta" me ya yi zafi haka NAJEEBA? wani irin abu ne wannan dake damunki mai tsanani? Ki fada min ni zan yi maki maganinsa domin Najeeba ina jin ki har cikin zuciyata yanda na dauki kanwata haka na dauke ki

Juyowa ta yi tana kallonsa
Sosai ta ji dadin maganarsa, wada ta so a ce yayanta ne yake fada mata dadadan kalamai haka

Kanta ta sada a hankali ta mike tsaye
Chapter 59 · 0% Book details