← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 138

Sashe 26

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ya yi yana adu'a dan samun hutu, ya gaji walahi yawan maganar nan ta jiya ba karamin gajiyar da shi ta yi ba hakan ya sa ya takaita maganarsa daga jiyan zuwa yau a wajen gaishe da mahaifiyarsa ta hanyar sirrinsa ne kawai ya budi baki ya yi wata maganar

Bai waiwayi wayarsa ba sai da garin Allah ya waye sosai har kusan karfe goma sha biyu

Yana gama daura agogonsa ya janyo wayar nasa
Direct cikin message dinsu ya shiga ya rubuta" halayanta su zamo nata ne ita daya, ta kasance mai halayan dawissu
Ina son wace ta san kanta
Ina son wace ta rufe kanta
A yanzu ka ware daya a cikinsu ka tabatar komai ya gama a yau dan ina so nan da kwana hudu a gama komai ba zan ja ba, ba zan yi wani gangami ba dan ba aurena ne na fari ba!

Yana gama turawa ya zauna bakin bed dinsa yana jin wani haushi haushi
Ya tabata bai isa ba, komai yanda zai kiyaye tara mutane sai sun taru an masa yawan magana da tsarewa
Shi kuwa alkawari ya yiwa kansa sati ya baiwa kansa sai ya ajiye wata macen a saman bed dinsa wace zai raya sunnar ma'aiki da ita,
Wace zata cike zargin zinariya, ta faranta ran Anmynsa ta hanyar bin umarninta,

Ajiyar zuciya ya sauke duba da bata lokacinsa ne yake sannan ya mike ya koma dakin da yake hangen abubuwan dake wakana a masarautar

Kansa kan daukan caji fiye da tunanin mai karatu
Matsalolin cikin gidan marauta a gaban idannuwansa suke, da yawa sun fi karfin titsiye su tashi daya dole ta sannu yake binsu ya ruguje su, da yawa rainin hankali ne yakan yi kamar bai ji ba bai gani ba
Shi dai a matsayinsa na sarki mafi yaro a wannan karni yana iya yinsa dan gannin yana kare wasu abubuwan

Shi mutun ne mai son motsa jikinsa kamar me, motsa jiki a wajen da ba wanda zai zo kallonsa ko ya san shi waye hakan ya saka yake fita da mutun kwaya daya tak su je wani tafkeken filin LAKD ya bale a guje ya yi ta gudu son ransa
Idan ya yi ya gama ya yi pompe mai yawan gaske sannan su je wajen da yake shan dadar iskar garin ya zauna ya saje da kowa ya sha iska ba tare da ya yi aboki ko budurwa ba
Ya saba fitarsa ba yau ba, idan bai yi fitar sirrin nan ba tabata wani abu mai karfi ne ya hanna masa yin hakan......

Wannan kennan
............................................

Kallon sarkokin Abih yake daya bayan daya wa'inda Dayabu ya saka aka yi masa tun daga kansa har zuwa kannensa

Irgawa ya yi ya kuma irgawa ya kalli DAYABUn, to ko ya manta su goma sha takwas ne?
Sai abin ya so bashi dariya da ya ambaci hakan a zuciyarsa
Me zai hanna shi mantawa kai kuwa? Ya kuma tambayar kansa

Abih ya kuma daya sarkar ya kalle shi ya ce" to kaima sakawar zaka yi?

Murmushi ya yiwa abih ya ce" hum Abih rigimar y'arka ce wai yo sai na saka mana kamar wani dan daudu ko wani dan duniya

Daria Abihn nasa ya yo yana bin yan siraran sarkokin zinarin da kallo
Tabas yana godewa Allah da samun baban d'a mai hankali da nutsuwa wanda yake iya yinsa dan gannin yana gyara irin barnar da shi ke aikatawa

Koma meye dalilinsa na sakin mata bashi da kyau domin saki Allah ya halata shi aman shi kansa baya son sa
Shin y'ayansa sunna jin haushinsa ko? Irin yanda yake korara matansa haka kawai
Akoya matarsa da ya saka wace zai iya rantsewa bai kamata da laifin komai ba, ya saketa ne dan ya wayi gari da maganar cewa a kan me ita zai barta bayan ya rabu da iyayen sauran? Sai mahaifiyar NAJEEBA wace ta maka shi a kotu sai ya saketa

Murmushi ya kuma yi yana kallonsa ya ce" yayansu ka manta ku goma sha takwas ne y'ayana na cikina?

DAYABU ya dago ya kurawa fuskar Abih ido, a hankali ya ce" aa mu goma sha tara ne Abih

Gabanta Abih ne ya yi wata irin yankewa ya fadi wanda hakan ya saka shi saurin zabura yana kallonsa

Su goma sha tara ne?

Ku goma sha tara ne? Ya maimaita masa da sauri ya dora da fadin" a ina ka samo ta cikon sha taran?

Fuskarsa dai ya kuma kurewa da ido yanai masa kallon nan da ake fadin kai ka san na san da hakan
Sai ya yi gagawar basarwa yana murmushi ya ce" Abih, na manta ne, wani sa'in fa garin magana har cewa na yi mu goma sha uku ne sai da zahrau ta yi ta min daria

Wata biyayiyar ajiyar zuciiya uban ya sauke sai dai sak ya kasa sakin jikinsa su ci gaba da hirar kamar yanda suke a dazu

Sarkokin ya kuma rikewa yana fadin" ina ta NUSAIBA?

duban mahaifinsa ya yi ido cikin ido a karo na biyu ya buda bakinsa ya ce" ban yi da ita ba

Uban ya tsare shi shima da ido, kamar yaya bai yi da ita ba? Amsar ba wata a boye take ba a bayanne take cewar bai yi da ita ba
A kan me bai yi da itan ba? Mantawa ya yi ko yi ne bai yi da ita ba? Aa ai ba cewa ya yi ya manta ba, cewa ya yi sak bai yi da ita ba

Sai ya ji wani shaku da tsoron son jin abinda ya saka yaron nasa na farko a rayuwa yin wani abin kyautatawa wa kannensa banda daya a ciki
Hakan ya saka shi fadin" gaba kuke da mahaifiyarta har yanzu wanda ya shafeta ko wani abu mahaifiyarta ta yi maka ne?

DAYABU ya sauke ajiyar zuciya yana murmushi ya ce" Abih, ka san bamu taba zuwa muka kawo maka karar matarka ba
Da yawa wasu matan ka sake su ne dan kawai idannuwanka sun kama wani abinda bai dace ba a kanmu

Ban san girman laifukansu ya dame nata ya shanye ne? Ban san ita din lale gaskiyarta ne itace rayuwarka ba? Abinda na sani shine na gaji da sakin mata da kake, kuma bana so ka kuma sakin mace dan a yanzu na lura lalefa kanena sun taso har sun fara gabatar da mazajen aure wanda nake fatan idan sun shiga sai dai a fitar da gawarsu fita na har abada
Abih abin zai yi matukar wahala sai dai ikon Allah kawai zai kubutar da su
Shine nake so ka yi kokari ka yi zamanka da matarka , in sha Allah idan dai mune damuwar ba zamu kuma zama damuwa ba aman fa Abih muma a kiyaye namu rayuwar dan kai ka san cewa ba zan iya lamuncewa mutun shiga hakin yaran da nake yiwa kallon marayu
Basu rayu da baban jigo na rayuwa ba wato uwa
Hakan ya saka nake yi masu uzuri a rayuwar yau da kulun, hakan ya sa nake kara jin tausayinsu

Abih kam ba amsarsa ya samu ba, sai dai gannin yaron nasa ya daure shi da jijiyoyin jikinsa sai kawai ya yi masa shiru bai kuma tofa komai ba aman ya kuduri niyar tambayar ita natar tasa dan ya tabata bafa zasu fada masa komai ba tunda har yayansu ya hana............................

Sarkokin ya mike da su ya nufi cikin dakansa

DAYABU na zaune yana kallon ikon Allah, Abihnsa zai fito ya bashi sarkokin ko ba zai fito ba? Har ya kusan cin rabin awa karshe ya mike yana murmushi ya girgiza kai ya yi gaba dama ya yi hakan ne dan ya isar da sakon cewa ya cire y'arsa a cikinsu!

Ihu ta saka bayan ta kashe kiran da suka gama da Anmy

Da wata irin daria ta ce" jama'ar gidanku wannan karron ina gayya, ina gayya ne da kaina kuma sai na buga wasa a kofar gidan sarki

Ummulkhair ta dago daga yankan akaifunta tana yiwa kanwar nata kallon anya Najeeba baki haukace ba kuwa?

Najeeba ta ce" ke ke aunty, wallahi du jarabar da za'a yi sai na kirawo ANNABO MAWAKI ya kada min waka da orchestre na shiga na cashe domin kuwa *DUNKUM* zai kara aure inji Anky, kuma auren nan da kwana biyu ne taxe maza maza mu je wajen mai dinki ta tura sakwanninmu mu zabi kalar da muke so

Zahrau ta fito da waya tana daria itama ta ce" haka fa sannan Anmynki ta ce kar ki yarda ki dauki dinkin da bai mata ba dan ba sakashi zaki yi ba!

NAJEEBA ta waiwaya tana kallonta ta ce" wai kin san aurensa mai yake nufi? Hehehe, yana nufin za'a kawo wata yar rainin hankalin ta biyu wace zata ci min uwar wace ta raina halitar Allahn ta farko ta dane min kan banza ta daki bakin mai bakin shegun nan, zamu ga karyar zagi da takama za'a yiwa zinariya kishiya da gold🤣🤣🤣🤣

Hum a dai a slow najee
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

16

Hakan ne ta kasance abu na manya nan da nan abubuwa suka kankama cikin dan kankannin lokaci a wajen mutanen da suka iya aiki da lokacinsu

Nan da nan mutanen da anmy ta ringa fadawa suka fara halara cikin masarauta

Su Najeebama sun tare a gidan ne tun ana gobe daurin aure hakan ya sa gidan ya ringa yiwa Anmy dadi ga uwa uba irin yanda Najeebar ke ta yi masu kitso da kunshi cikin nutsuwa a daka

Idonsa cikin nata ya ce" in sha Allah gobe za'a dauran aure ZINARIA

Irin yanda maganar ta daketa ta sakata baki daya yin luuuuu zata kifa hakan ya saka shi yin taku biyu ya damki damtsen hannunta ya tareta a jikinsa ya yiwa bayanta mazauni a kirjinsa

A hankali ya kuma fadin" ki daina yi min garage da yaron cikin nan, dan shine abinda zaki yi mafi ganganci a rayuwarki wato barar min da shi da gangan

Tabas ta gama yarda cewa kwananta ne ya kare a wannan rana a irin wannan lokaci a tare da sarkinta
Chapter 26 · 0% Book details