← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 138

Sashe 78

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kanta ta kara sadawa kafin ta mike a hankali ta nufi dakin, zuciyarta kuwa cike da sake sake da son sannin abinda Nadia ta yi a bangarensa da irin tafiarta

Saurin korar abin ta yi a ranta dan gudun kar zargin ya yi yawa ta shiga dakin

Irin yanda ta yi karo da bra, da pant da rigar Najeeba ya sakata saurin shiga nemanta a cikin dakin

Idannuwanta ya sauka a fuskarta hakan ya sa ta nufeta da sauri tana kiran sunnanta a hankali

Najeeba ta buda idannuwanta da sukai mata nauyi ta sauke a fuskar yayarta

Zahrau ta yi saurin dago kanta cike da tausayi ta ce " NAJEEBA, sannu, sannu kanwata

Najeeba ta kara dora kanta a hankali saman cinyarta , a lokacin wasu hawayen suka kara balewa a idannuwanta

Muryarta a raunane ta ce" ban taba sannin Ahalin Mutalab zaku ki saurarena ku min auren nan bayan ina fadi a sannu ina fadi da ihu cewar kar a mun hatsari ne ga rayuwata ba, sai gashi a kaina an fara inda yaya ya nuna min idan na ki zai yi kuka, su ummu suka nuna min ai alkairin kennan, Anmy bata zauna mun zanta ba, Abih bai bani lokacinsa ba, ke kina nesa idan na kira bakya dagawa, sai ga bakuwar da ta zo ta wanken fuska da mari du a kan auren nan?

Zahrau ta ji zuciyarta ta karye, a hankali ta ringa shafa kanta ta ce" Najeebana, zafin ciwo ne ke damunki, idan kika shiga ruwan zafi kika sha magani zaki ji ki garas, ki yi hakuri kin ji? Ki daina fadin magangannun nan a kanmu, Najeeba ba zamu taba juya baya a wajen da zaki cutu ba, kuma iyayenmu ba zasu taba yi maki shiru da gabgan ba, sunna tsoron su saurareki ne ki ci galaba a kansu har su janye auren nan, Najeeba Ummu kuwa kin san halinta, idan tana waje ki kiyayi abinda zai kaita makura, kin mantata ne? Bata son irin halayan nan kin sani sarai a kan zumunci bata saurarawa, Ummu idan muka yi fada zata hade mu ne ta bamu punishment din da da kanmu zamu dawo nemawa junnanmu hakuri, kin manta a lokacin da yaya kan yi fushi da mu irin yanda take zaunar da shi ta ringa nuna masa mahinmancin junnanmu? Ki daina jin haushin ummunmu, domin uwa ce a wajenmu baki daya

NAJEEBA ta cije lebenta tana jin ciwo a zuciyarta ta ce" ba zaki fahimta ba, Zahrau, ba zaki fahimci abinda ke faruwa da rayuwata ba, kin ga, ashe shine muke zama a stade, kuma shine muka buga basket ball, Zahrau, ya wulakanta ni, ya nunan ba kowa bace ni, ya kawo Nadia ya kwo........

Rufe bakinta Zahrau ta yi, a hankali ta ce" ki yi hakuri

Iya kalmar da ta fada kennan kafin ta shiga kokarin kamata
Du irin abinda take Najeeba na kallonta ne kawai, domin a tunaninta wannan bacewar shinfidar da har ya bushe nata ne
Shirun ta mata dan ta lura bata so ta yi mata bayanin abinda ya faru,
Lebenta ta kara cijewa a lokacin da Zahraun ta fita dan zuwa ta samo wata suturar kafin ta tafi da ita

Aman Allah ya taimake ka, tun jiya ka bani amsar eh zan dauki abin shinfidar amaryarmu, dan me zaka hanna a yanzu bayan kai ka fada?
Muryar Zinaria ce kw bayani a sanyaye Shaheed kuwa na sauraronta

Wayarsa ta kara yin vibration din mesage
Yana dubawa ya ga sakwon eh za'a samu waje sosai a jirgin da zai shigo daga niamey sannan ya wuce agadez

Amsa ya turawa yaron nasa wanda ke kula da shagonsa na kayan gini cewar a je a ciro tiket na iya adadin mutanen da ake bukata

Dubanta ya yi yana karantarta,

A hankali ya ce" na wanke abin shinfidar, yana hankalce da ita

Da karfi ta ce" Meh? Ka wanke? Wani irin wankewa? Kai ne zaka yi wanki? Ko dai bata kawo budurcin nata ba?

Duban da ya sauke a kanta ne ya sakata saurin yin shiru da maganarta sama sama

Da sauri ta dan duka ta nemi afuwa sannan ta mike ta nufi hanyar bangarenta kamar zata fadi

Tana zuwa ta karasa da saurin jikin mahaifiyarta tana kuka ta ce" wai ya wanke, wani irin wankewa? Shine zai wanke?

Mahaifiyarta na shafa kanta tana cije lebenta, ya wanke? Idan har ba'a samu jinninta ta haka ba, bata tunanin akoy yanza zasu yi su samu
Sai dai zasu kwatanta ko yayane

Yana nan zaune har Zahra ta dawo ta shige ciki

Bata jima sosai ba ta fito sunna tafe a hankali kan Najeeba na saman wuyanta

Tsayar da ita ta yi ta karasa ta duka ta dauki alkyabarta ta dawo a hankali ta rufa mata kafin ta kara kamata su nufi hanyar fita

Idannuwansa ya dago daga kallon gefen da yake ya sauke a bayanta, wani yam yam ya ji a jikinsa hakan ya sa ya cire dubansa daga kanta yana kallonsu har suka fita sannan suka dauki hanyar coridor din da zai kaisu bangaren Anmy

Haka kawai ya dan kurawa waje daya ido, ba abinda yake gani sai abin nan da yatsarsa ta dangwalo
Nan da nan ransa ya ringa baci
Bacewa mai tsanani
A kasan zuciyarsa kuwa ya furta" *ta zo ta baka nutsuwa, shin haka ta mike a gabanka ka tana wajen da ka yi niya?* idannuwansa ya kara rintsewa da karfin gaske yana jin kansa na neman kwasan ciwo

Mikewa ya yo da sauri yana koran tunanin nan ya nufi hanyar fita

Rumfa zai je wace aka kama macizai har uku a cikinta a jiya,
Mugayen macizai ne masu baban dafi
Macizan na cikin gidan ne, a yau dai zai gansu da ransu, a yau zai dauki hannu na mai su

Tabas tun yana yaro aka koya masa harkar wasa da maciji, zai iya cewa a kusa kusan nan a cikin gidan sarautar du kalar macijin da aka yarje a shigo da shi to fa sai ya san wanda yake da damar iya kula da shi dan kar a shigo da wanda zai bace ya jiwa mutane

A kaf masarautar nan basu san cewa yanda ya lakanci abin har ya fi karfin tunaninsu, domin bayan koyon da akai masa ya kara zurfafa iliminsa ta hanyar karantarsu da komai ta computersa

Tun da ya fito ya ja turus ya tsaya sakamakon irin busar da aka kwasa

Ashe fa akoy hawa dawakai?
Irin yanda ya ga matasa na laye sun sha damara da manya manyan mutane harda datijai kowane na tsaye ne rike da linzaminsa ya saka shi sakin dan murmushi

Hannunsa ya daga ya yafito amintacensa dake tsaye kusa da wani ingarman doki ya sha kwaliya yana rike da linzaminsa, wato dokin da zai hau ne

Tunkaro wajensa yake yana karantar irin tsayuwarsa

*Hala har ya tare da mace ne a cikin matan?* shine tambayar da ya yiwa kansa

*HALA JAR YA SAMU NUTSUWAR DA YA HANA MASA SHI YA SAMU?*

yana karasowa ya kai kasa ya hade hannayensa ya sada kansa ya furta" *JA GABA KAKE JAN GWARZO, FARO KAKE MAI FARAR ZUCIYA, YA KAI MIJIN ZINARIA, MIJIN GIMBIYA NADIA DA GIMBIYA NAJEEBA, SANNUNKA DA FITOWA HASKE, HASKENKA HASKE NE MAI HASKA DUNIYARMU, SANNU DA FITOWA NAMIJIN MAZAJE, SANNU DA FITOWA MAI GIDAN RANA, SUN BUGU SUN BUGA SUN KASA, GURNANI KAKE MAI TARWATSA TARON MAZA, KAI NE DAYA TAK MAI WUKAR YANKA MAI DAMAGARAM SARKIN SARAKUNA, MATASHI NE MAI ABIN MAMAKI, MAI MOTSA ZUKATA KODA BASU SHIRYA BA*

Murmushi ya saki yana lumshe idannuwansa, kansa ya dan sada da dubansa ya sauke a kan Amintacensa
Namiji ne gabjejen gaske wanda yake ji da shi,
Wannan shine babar kyautar da masarautar Garin Agadez ta taba masa wace har gobe yake jinta har cikin ransa, kyautar Amintacensa kyauta ce da ba zai iya mantawa ba, a da soja ne, ya sadaukar da haka dan bauta masa, shi kam me zai iya bashi ne dan ya gode masa? Shi ba bawa bane, ya bashi sarautar dogaran Fada baki daya, yana da salary wace ta ninka ta sojojin har uku, yana da gida a waje da fada da mota har biyu kyautar sarki ne

Dan rage muryarsa ya yi da niyar ya tsokane shi kasa kasa ya ce" yaushe zan maka wankan ango?

Shima murmushin ya yi ya kara sada kansa hannayensa jimke bai daina yannayin kirarin da yake ciki ba

A hankali ya ringa takawa manya manyan dogaransa na yi masa kirari, da sauri amintacensa ya janyo dokin ya nufo shi da shi

Danndukawa ya yi dan ya taka ya hau kamar yanda aka saba

Sai dai ga mamakin duban jama'ar wajen wani uban tsale ya daka ya dane saman ingarman dokin nan
Ai kuwa zo ga ji wani irin busa da ihun gardawa da kirari, nan fa tsumi ya motsa aka haukace aka dane dokunna

Lalle Sarkinsu ya fito a shirye, dan haka du suka haye suka yi baban filin sukuwar Fada aka shiga gabatar da sukuwa cikin tsari da zaburar da zuciya inda wajen ya cika makil ana ta kai kawo ana murna

A hankali ta je ajiyeta saman gado, sai dai ta kasa zama ta kwala yar kara tana mikewa tana kara wara kafafuwanta da muryar kuka ta ce" Aunty, barkono a kasana, ki yiwa Allah mu je asibiti kar a je na farke

Auntynta ta juyo tana daria tana kallonta, a fili a bayane ta ce" sakaryar wofi, NADIA, kin bani mamaki, wai ki budi baki kina hauka gaban kishiya? Ni yanzu da Allah tsaya min na taimaka maki

NADIA ta kaleta da kyau ta yi murmushi ta ce" Aunty kennan, ni NAJEEBA ba kishiyata bace, kuma na rantse da Allah zan yi ta zuwa ina gaisheta ina neman afuwarta har ta sauko,
Aunty, ni ? Ba zaki turani na yi mata gaba ba, ni? Zan mayar da ita kishiya? Idan har na yarda na shiga layin kishiyarta kin ganni nan ko? Sai kin kasa gane wacece ni! , a jiya har fada kike ashe bata damu da shi ba?

Ni kuwa ina da tambaya Aunty,

*MENENE AINAHIN DASA TSANARSA A ZUCIYARTA?*
Chapter 78 · 0% Book details