Sashe 74
Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin maganar bakin Anmy ya sakata jimk'e hannayen Zahrau,
Ita? Ita fa? Zata tare a ina? D'akin wa? Turaka? Saima kalmar turaka ta b'ace mata b'at a bakinta,tabbas aurenta aka fara d'aurawa kafin a d'aura na Nadia, sannan idan maganar wace aka fara kawowa ne ita a gidan ta kwana, sai dai sam ba zata tare a turakar kowa ba!
Idanuwansa a lumshe suke a lokacin da wannan magana ta fito daga bakin Anmy.
Rintse idanuwansa kawai ya k'ara yi yana jin yanda yanzun ne zuciyarsa ta fara tafasa da abubuwan dake faruwa.
A kan me za'a ce ga wace zata fara shiga d'akinsa? Shi sam, bai ajiye wannan a gurbin wace zata zo gareshi ba, ba an d'aura ba? Su barshi ya zartar da yanda yake so aurensa ya tafi.
Anmy ta k'ara gyara zamanta tana hangen yanda Zinaria ta jinginar da kanta jikin kujerar da take zaune.
Sosai take tausayin yarinyar, tana tausaya mata da irin kishin dake damunta, irin wannan kishi, abinda ya dace ta samu wace zata ringa tausarta tana saka ta a hanya tana tarota, sai dai ga dukan alamun mahaifiyarta wace ta fi kusanci da itan ba zata taimaka mata ba, sai yanzu ta fara cire zafin reaction d'inta na jin an d'aura auren Zahrau da mahaifinta, tabbas uwar gijiyarta na bada gudunmuwa wajen k'ara tunzura zuciyarta, tatanta d'aya ne, irin zargin da ya shiga zuciyarta a kansu ya zamo k'arya, idan har ya zama gaskiya ita kam bata da abinda zata iya yi sai zuba ido, kisa? Kisa fa?
*Allah ya baku zaman lafia*
A fili aka ringa amsawa kafin ta bada damar ana iya tafia.
Talafota suka yi suka fara bi ta corridor d'in da zai kaita falonta suka fara fita.
Sai su Nadia suma suka yi b'angarenta, sannan su Zahrau suka kamata suka fita da ita, ita ko b'angaren nata bata je ba suka nufi b'angaren Anmy da ita dan su shiryata a rakata.
Suna shiga ta zame ta zube a k'asa a baki bakin shiga falon kafin ta saki kuka mai zafi mai cin rai.
Wace ta yi mamaki kad'ai kishiyar Zahrau ce, domin ita bata san wannan launin kissar da ta gabatar ta dnane abinda ya daketa a cikin zuciyarta wato wai Nadia.
Hannayenta take yarfewa a rikice ta ce" Wai Nadia? Aminiyata? Me na masa?"
Da sauri su Ummu dake jira suka yo kanta, har rige rigen tambayar me ya samu Nadiar suke?
Najeeba ta k'ara d'ago kanta ta ce" walahi basa soyaya, yaushe rabona da ita? Da sunna soyaya nice ta farkon da zata fara fad'awa domin ita rayuwar nan birgeta take, na tabbata daga baya ya saka haka dan kawai ya k'ara wulak'anta ni."
Da mamaki kishiyar Zahrau ke kallon Najeeba kamar me.
Najib dake zaune cen yana game da wayar Anmy ya dakata tun da ta fad'i yana ta kallonta, yanayinsa na nuni da hankalinsa a tashe ya ce" aunty Najeeba zaki b'ata kwaliyarki fa."
Zahrau ta kalli kishiyarta ta sakar mata murmushi ta ce" aunty, ki je ki huta kin kwaso gajiya."
Itama dacewar hakan ta gani, dan haka ta sakar mata murmushi kafin a sanyaye ta ce" Najeeba, ki yi hak'uri kin ji? Idan harma hakan ne ki d'auka hukucin Allah ne kasancewarta matarsa, ki yi hak'uri ki sanyaya zuciyarki ki rage kishinta kin ji?"
Tunda take maganar bata wani baiwa abin importante ba, sai da ta ji kalmar *kishi*,
Nimporte quoi! Ita zata yi kishi dan kawai ya yi aure? Kishi? Na me? Auren so ake yiwa kishi, mutumen da aka sani ake kishinsa, mutumen da ya gama kafa soyayarsa shi ake kishi ba wai haka kawai ba, ita ba kishi take ba, sam ba kishi take ba, tana jin haushin a mata kishiya da aminiyarta ne, me ta yi? Meye laifinta? Nadia ba abokiyar gabarta bace aman shine za'a had'ata gaba da ita?
Wani ihu ta tak'ark'are zata saki sai dai abinda ya d'auke mata shi saukar yan yatsu biyar a fuskarta.
A firgice ta d'ago dan ganin waye ya mata wannan hukunci a saman fuskar da ta gama shan gyare gyare? To mema ta yi na marin?
Sama sama ta ji muryar kamar ba tata ba tana fad'in" Zaki min shiru ko sai na b'ab'ala maki k'afa a nan? Shirme! Shirmen banza! Maza mik'e ku saketa, maza mik'e zaki fice a kimtsaki ki je ne b'angarensa idan ya so dan Allah a kawo ki gunduwa gunduwa *Najeeba MUTALAB!* Yarinya an wani shagwab'aki kina iskanci? Ke kin san wanda kika bud'i baki kika yi magana sama sama a gabansa ko uwarki da ubanki ba zasu iya yi ba aman alfarmar Gimbiya ya biki da kallo? Au ke ga marar kunya, ga isashiya ga mai bakin magana ko?" Du a wannan lokacin kamaninta ne suka dawo wa Dayabu dake tsaye ya hard'e hannayensa.
Tabbas ba'a tab'a kawo mace mai laushin da ta ringa kwana da su a saman katifa d'aya tana cencana su ba irinta , sannan ba'a tab'a kawo macen da idan ka yi abin hukunci zata hukuntaka ko a gaban ubanka ne irinta
takan kashe dukiyarta domin baki d'aya y'ayan, bata tab'a ware tata ba, idan ta tashi wanka d'aya bayan d'aya take wanke y'ayan daga shekara zuwa shekara ne, da d'an girmansa yana hankalce da ita bata tab'a dan ta zo kan tata yar ta fi wanketa ko ta fi binta a laluma ba.
Hararan da ta sakar masu ta cire d'aurin da akai mata na zarah Buhari sannan ta dakatar da Anmy ta ce" Wallahi, walahi da ba dan idan na fita na tatakata ba nima na raba rashin kunya a gaban SHAHEED ba, da sai na tataka banzar yarr nan! Ke har tunani kike dan yana son ki ya aure ki?"
"Ummu?" Anmy ta fad'a da d'an k'arfi.
Ummu ta ce" Oho shiiiiit, Anmy pls ki barni haba, wai ita uban wa ta fi zuciya ne? Ke? Ke najeeba? K'anwar bayansa zaki bud'i baki ki wani nuna baki damu ba dan an maki kishiya Nadia? To ki yiwa Allah kar ki damun idan kina so ki k'aro masa da Barirar! Aman fa ki sani, ko Ubanki MUTALAB da ya d'aure maki gindi kike iya shege, ko uwar taki gata a tsaye, ko su yayun naki nasu isa sultan Shaheed gurnanin zaki na zaune su ringa iya shege ba! Yau na ga ikon Allah! Dan an d'aura maki aure da shi ba yana nufin har kin kai wajen da zaki masa iskanci bane! Ke ko murza namiji zaki yi ki murza a k'uryar d'aki aman ba wai a gaban mutane ki nuna ke kin isa ba!"
"Zaki daina bina da idanuwa kina wik'i wik'i da su ki mik'e Najeeba ko sai na nuna maki wacece *MARIAMA BIN ABDALLAH* *UMMU?*!"
Zabura ta yi daga zaunen da take a kasa ta mike tana kara zaro idannuwan da sauri ta aniya kokarin yin wajen Anmy sai kara kallon Mahaifiyar nata take🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*Na*
*SAJIDA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
39
Har waiwayen Ummu take tana hada kafa wajen sauri
Anmy ta kamata ta juyo ta kalli Ummu ta yi kwafa ta jata suka shige ciki
Dama wace ta yi saura datijuwar nan ce kadai wace zata kimtsata wato Fadimatu
Hankali kwonce ta sakata cikin wani ruwa mai kanshin gaske da sanyaya zuciya
Tana fitar da ita ta kara bin jikinta da wani mai lalausa mai sanyin kamshi
Wasu kayan baci dake cikin kwalinsu ne ta ciro, rigar fata ce doguwa da pant dinta da bra dinta
Rigar mai shegen kyau ce abin ba'a magana, iein mai santsin nan ce hakan ya sa take bin jiki masha Allah
Cike da nutsuwa ta zauna ta kara gyara mata gyaran gashin da akai mata
Wannan uwar kwaliya baki daya an wanketa an zubar da hodar
Kamaninta natural shine a tatare da ita
Baby face dinta ta bayana, ga lebenta mai kyan tsari
Man lebe mai wani irin kanshi aka bi da lebunnanta
Kwali kawai aka saka mata kafin a rufa mata bargo wani sansanyan kanshin turaran wuta ya shiga bin jikinta baki daya
Har gashinta da kalar turaran gashin da aka mata anfani da shi
A yau dai Najeeba kanta ta san ko wa ya sameeta a haka ya samu gata mai matukar girma da tsayawa a zuci
Hijab fari kar, hade da Alkyaba wata kalar blue mai duhu sabuwa dal aka luluba mata a saman suturarta
Zaunar da ita ta yi tana kallonta
A hankali ta ce" Najeeba, ko me zaki tarar ki kasance mai yin biyaya da Hakuri
Ki sani ko me kike ji a zuciyarki ki dane shi, domin kuwa idan har kika ringa falasa shi to fa kece a matsala kin ji?
Kanta ta daga a sanyaye, domin baki daya jikinta ya gama mutuwa ne, wata faduwar gaba take ji, takan yi tunanin wai da gaske zata je dakin mutumen dake miji a gareta? Wannan shiri da ake mata shin hasashen da take ne zai faru da ita?
Wannan rakiya ba kowa ya yita ba sai Jakadiya
A lokacin da aka yi kiranta itace mafi datijantaka, ita ta raka Anmy, yau gata zata yi rakiya ta uku a matan sarki
Cike take da fargaba, ta so ta ti tambayar aa, yaya za'a raka masa mace biyu? Sai dai ba hali domin ta san idan da ba da sanninsu ba, ba za'a iya kai masa wata kuma a kara kai masa wata ba
A hankali suke takawa sunna kara kusantar dakin
Yanzu yanzu ta dawo daga rakiyar Gimbiya NADIA bisa umarnin amintace ya shaida mata umarnin mai wukar yanka ne
Ta shiga rudu, mace biyu zai tare da ita ko me?
Jiki sanyaye ta karasa da ita tafkeken falon da ya kasance shine falonsa na karshe wato na sirrinsa, wanda matayensa ke shiga, daga su sai dakinsa na baci
Ta jima tsugune kanta kasa tana jiran uban gidansu
Najeeba dake zaune saman kujerar da ta yiwa kanta masauki ta daga kanta cike da nutsuwa tana bin falon da kallo
Tabas bata taba gannin wajen da ya birgeta irin wajen nan ba