← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 138

Sashe 80

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummu ta yi murmushi dai kafin ta ce" Zahrau, sai nake gannin kamar kun so kanku da yawa, idanma wani abu ya hada su fushi da junna me zai hanna ku yi bincike dan gano kusababin wannan rashin jituwa tasu ta hanyar zama ku tambayi kanku da kanku wacece kanwar ku? Wannene Sultan Shaheed?
Bara na fada maki waye SHAHEED,.SHAHEED mutun ne mai son kare martaba da mutuncinsa da na duk wani wanda ya sani bare na dan uwansa
Shaheed a duniyarsa ya tsani mace mai rawar kai da neman fitina
Shaheed ya kasance mai son mace mai wahalar ganni ga maza
Zahrau, Shaheed fa shugaba ne
Zahrau SHAHEED yana da dama da yawa a rayuwa, sannan idan yau ya ki kallon Najeeba meye dalili?
Inaga baban dalili a nan shine yana jin haushinta, yana jin haushin halayanta, a abinda na fahimta kennan
Ke kin san wacece kanwarki a fannin tara samari
Wayarta na hannuna , labarinta na kai mini daga inda na fito

Dan shiru ta yi ta ce" bama wannan ba, zaki fita kanki tsaye ki tarbi Anmy ki nuna mata Shaheed na takura yar uwarki Zahra ko kunya bakya ji bakya jin nauyi? Kin san irin yanda ta ci burin auren nan da irin lokacin da ta jima tana son haka ya kasance kuwa? Kin san burin anmynku kennan kuwa? Kin san baban tashin hankalinta a yau ta ji wani abu na faruwa tsakaninsu ne, bare har abin ya fito daga wajenku? Zahrau idan da amana ruwa ba zai ci gwani ba, idan har da kunya ba zaku iya daga kai ku nuna wani lamarin ba, Anmy wacece a wajenku? Ko kuwa sangartar da ku da tsananin soyayar da ta nuna maku ne zaku saka mata da shirme?

Najeeba ta lumshe idannuwanta a hankali ta ja jikinta ta koma wajen wankanta

Darzar jikinta ta shiga yi cikin nutsuwa

Sai da ta gama sannan ta koma gaban madubi ta yi tsaye

*ANMY* tabas idan har su din y'ayan halal ne zasu so saka alkhairi da alkhairi,
ANMY, uwa ce a wajensu mai kuka da damuwarsu ta yi farin ciki da farin cikinsu

Ta kasance mai sadaukar da farin cikinta dominsu mai rungumesu a kowani hali
Du irin fitintinnun su bata taba gajiyawa ba , takan tarewa ta dauki jifan da akaiwa kuka

Gashin kanta ta warware ta shiga yin wanka dan ta tsaftace jikinta

Sai da ta gama ta dauko dan karamin tawul ta nade kan nata kafin ta kurawa madubi ido

Murmushi ta yi a bayane tana gannin yanda fuskarta keda kumburin kuka da rashin wadatacen barci

Lale ta yi mantuwa guda, ta manta su waye Y'yayan mutalab, ta manta idan ta tayar masu da hankali sosai ba zasu iya rikewa ba, au kuwa zasu tayarwa da Anmy ne
Lale ta manta girman alkhairin Anmy a rayuwarta

Murmushi ta yi tana dauke dan guntun hawayen da ya dan leko ta gefen idannuwanta kafin ta nuna yar yatsarta ta kausasa dubanta ta ce" NAJEEBA MUTALAB, na hana maki zubar da hawaye a gaban kowa! Daga yanzu zaki yaki du wani mai shirin yakarki da salon takun da ya zo maki ne!
Tawul ta daura a kirjinta kafin ta nufi hanyar fita

A hankali ta rufe bayin, tana juyowa ta gansu su uku zaune su Ummu sun shigo sun hadu su hudu kennan

Murmushin da ta jima bata masu irinsa ba ta sakar masu

Du sandarewa suka yi sunna gannin yanda take takowa ta karasa wajen kayanta dake dakin ta ciro na sallah ta saka ta juya ta tayar da sallah

Tana gamawa Anmy na shigowa da zazafan dahuwar dake ta tiriri da kanta a hannunta wanda ta shige kicin da kanta ta dafa da kanta ta karaso tana fadin" an yi sallah?

Da wani murmushin ta mike tana fadin" Anmy, yinwa nake ji sosai cikina

Murna, farin ciki ne ya lulube su baki daya, Ummu dake amsa waya kuwa ta yi murmushi a ranta tana furta" yanzun na yarda ni na haifo ki yarinya!

Kamar da wasa Najeeba ta zauna tsakiyarsu suka ringa cin abincin nan sunna ta raha tsakaninsu

Anmy ta kalli Zahrau ta ce" me ya sa ba zaki bi yan uwanki ku juya ba? Ita maman Zinaria an ce tace zata bi baya sai jikin Zinaria ya daidaita, ke kuma kin ce ba yanzu ba, shin akoy wata matsala dake faruwa a gidan naki ne?

Zahrau ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Najeeba dake cire rigar nan ta dauko yar yololuwa ta saka ta dawo da sauri tana fadin" kar ku cinye mai dadin

Murmushi ta yi ta kalli Ummu dake dan kallonta kafin ta sauke ajiyar zuciya ta maida dubanta kan Anmy dake nazartarta ta ce" Anmy, lafia kalau, ina so ne har Najeeba ta tare bangarenta, kin ga kin ce sai ta yo satinta sannan, kuma mun yi magana da shi ya amince

Anmy ta gyada kanta tana murmushi suka ci gaba da cin abincin

Sai cen bayan sun gama ta kalli Ummukulsum ta ce" ummu, ki yi kokarin kula yarima, ya jima a falon nan , tabas na fahimci wani abu a tatare da yaron, na kuma yarda da gaskiyarsa

Ummukulsum ta gyada kanta tana dan sadawa irin na jin kunyar nan.......

Tana gama ci sosai ta mike ta yi saman bed dinsu

Kwonciya ta yi tana warware gashin kanta

Dubanta ta maida wajen Anmy , sai da ta shagwabe fuskarta ta ce" Anmy, Saloon dina fa?

Anmy ta kaleta da sauro, ta kalli Ummu, ta kuma kalli yan uwanta

Sai da ta kikifta ido a hankali ta ce" sai bayan sati biyu zaki koma in sha Allah Najeebana, fatana ki kwontar da hankalinki Najeeba

Murmushi ta yi tana lumshe idannuwanta

Ummu kuwa ta mike ta kama hannun Anmy sukai waje

Tana dubanta ta ce" wani irin zata koma saloon? An taba yi daba?

Anmy ta ce" Ummu, ba zan iya hanata aikinta ba, kuma shima ba zai hannata ba walahi, sai dai wajen aikin ne aka cenza mata, ana gina mata wajen ne a nan cikin fada daga wancen hanyar fitar, sai a buda mata kofar a saka masu tsaro, mutanenta zasu iya zuwa nan su yi aikinsu su tafi, ranar da take sha'awa tana iya shiga ta zauna, ranar da bata sha'awa ta yi zamanta masu aikinta su mata,

Ummu ta ringa jin kaunar Anmy a ranta, ita kam bata da wani dan uwa ko wani makusancin da ya kai mata wannan baiwar Allah
Irin kaunar da take yiwa yaran daban ne, hakan ke saka mata gannin girmanta da kimarta a idannuwanta

Da yama kusan karfe biyar Najeeba ta yi salama kofar dakin Anmy

Anmy ta dago ta amsa mata cike da kulawa tana dubanta
Karasawa ta yi ta zauna kanta kasa a hankali ta ce" Anmy, a jiya sam bamu rintsa ba, sakamakon ciwon ciki da ya tashi Nadia, dole sai da aka nemi Sultan, hakan ya sa na nemi alfarmar a kawota bangaren Sultan dan ko menene shi din zai fi gagawar kulawa da ita

Dan numfasawa ta yi tana hankalce da yanda Anmy din ke kallonta kafin ta ce" karshe dai Anmy bamu rintsa ba har safia, nice ma na ringa dan barci hakan ya sa ya sakani zuwa na kwonta shi kuwa ya kwana yana kula da ita

Anmy ta ce" Subahannalah, yaya aka yi haka? Ko wani abu ta ci? Yaya aka yi bai fada min ba?

Najeeba ta kamo hannunta a sanyaye ta ce" ni ce nace kar a tashin min ke daga bacin gajiyar nan, ni na hanna a tada maki hankali dan na san kin gaji da yawa Anmy
Dan murza hannun take ta ci gaba da fadin" tana dan fama da irin hakan, lokaci zuwa lokaci, shine na nemi alfarmar ta yi satin nan, idan ya so sai na yi na gaba

Anmy ta kura mata ido ta ce" an fahimta ba, kina nufin ke kika sadaukarwa wata kwanakin ki a wajen mijinku?

Najeeba ta shagwabe fuskarta sosai ta yi raurau da idannuwanta ta ce" Anmy, Nadiata ce fa, kuma yayan kansa sai da ya nunan bai amince ba, ni na yi ta magiya har ya aminta da hakan , *ki yi hakuri Anmyna*

Anmy rasa abin fada ta yi, sai take gannin zancen kamar wani shiririta, wannan wani irin sake ne zata yi haka da gagawa? Amsa mata ta yi tana mai mata nuni kan ta je ta huta zata waiwayeta

Sai da ta kara godewa sannan ta mike ta nufi wajen yayunta cikin ranta kuwa ita ta san me take nufi da hakan.....

Sai da ya gama sallar isha'i tare da jama'a kafin ya nufi bangarensa

Cikin nutsuwa ya karasa yana tube kayan jikinsa kafin ya dauki wayarsa ya zauna ya danna kiran number amintacensa

*Macizan nan, shin sunna ina?*

Cike da rikicewa a muryarsa ya furta" abinda ya tayar min da hankali kennan, yanzu haka gamu tsaitsaye da baban liman muna ta nema, an neme su a wajen da aka ajiye su an rasa sama ko kasa

Ba tare da wani firgici ba, a nutse ya ce" kai da wa, da wa ke neman?

Kai tsaye ya furta" Ni da baban Liman, da Dogari mai rike alkur'ani

Kansa ya gyada a hankali kafin ya sauke ajiyar zuciya ya kashe kiran kittt

Hankali tashe amintacensa ya saka suka ci gaba da nema a wajen da suka boye su, Liman ya ringa fada kamar me, dogari ta rikice sai kai kawo suke baki dayansu sun hargitsa wajen ....
...............................

*AMINTACENA, LIMAN, DOGARI, MATATA*
Ya furta a kasan makoshinsa

Har zai mikr dan dauko litafinsa wayarsa ta dauki tsuwa

Hannunsa ya mika ya dauka gannin Anmy ya daga nan take

*Me ya sa zaka yarda da shawararta bayan ka san yarinya ce SHAHEED?* sunna gaisawa abinda ta fada kennan hakan ya saka shi yin tsai yana tunanin inda kalamanta suka nufa
Chapter 80 · 0% Book details