← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 138

Sashe 115

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya ce" BEEBAH ki janye hancinki daga wuyana, kin ga sai wani yannayi nake shiga kar na zo na kara kuma a ce ban kyauta ba "

Idannuwanta ta lumshe a hankali, tana mai jin yanda maganarsa ke sauka a cikin kunnayenta, sunna samun wani muhali mai tsafta a cikin kwakwaluwarta, kasancewarsu ba zafi ba ihu ba kausasa sai take jinsu wani bambarakwai harma ta kasa tuna waye mai furta su haka a sanyaye, a rashin sani ta dan matse masa wajen mararsa da hannunta na dama ke sama hakan ya saka shi rintse idannuwansa a hankali ya furta " Washhh zata kashe ni "

A dan tsorace ta dauke hannun nata, sannan ta yi gagawar janye jikinta daga irin mamukar da sukaiwa junna, cike da kunya gannin ya ki saka mata duwai ya mata wani damka ya sakata dam gyaran murya kasa kasa ta ce".......

.................🥳🥳🥳🥳🥳😎🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳

🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

58

Gannin ya ki sakar mata duwai ta dan gyara murya kasa kasa ta ce" ka sakar min nan, kana fa gannin inda kake saka hannayenka kana halaya kamar wani........."
Sai kuma ta yi shiru a lokacin da ya kara janyota da dan karfi jikinsa ya mayar da ita irin kwoncin da ta yi dazun a jikinsa sosai, sannan ya rage muryarsa sosai da sosai ya furta " kamar wani kwarto ko?"

Hannayenta duka biyu ta kai wajen bakinta tana rufewa tana zaro ido cike da tsoro da kuma mamakin furucinsa
Sai dai kafin ta kai ga farfadowa sai ta ji ya dora da fadin " Ai ke kika lalata ni, gashi sai haye min jiki kike kina wani shan mur "

" Ka ji tsoron Allah shaheed " ta fada a mugun sanyaye tamkar zata fashe masa da kuka muryarta na dan rawa rawa

Murmushi ya saki ya mayar da fuskarta wajen kirjinsa a hankali yake shafa bayanta ba tare da ya kuma furta mata koda A bane

Baki daya ta ringa kaea gyara kwonciyarta, har ta samu kwoncin da ta ji dadinsa sannan ta lumshe idannuwanta tana mai karanta adu'ar baci

Bacin ne kuwa ya yi awon gaba da ita, hakan ya saka mata sakin nauyinta a jikinsa da kuma kara sakankancewa da jikinsa

Murmushi ya yi a hankali ya juyar da ita saman bed din

Cikin nutsuwa da lalama ya cire mata rigar nan dan ta ji dadin baci
A hankali ya juyar da ita ya bale mata bras din nan ya cire baki daya

Numfashi ya ringa fuzga da sauri da sauri, sai kuma ya ja abin rufa da sauri ya rufa mata har wajen wuyanta sannan ya kara yi mata adu'a ya mike yana gyara jikinsa sannan ya fito daga dakin ya nufi bangaren AMMI

Kamar yanda ya yi tunani hakan ce ta faru, tana zaune saman abin sallah tana jan carbi aman baki daya hankalinta waje guda ta kurawa ido tana kallo hakan na nufin jan carbin ne kawai take aman damuwar da take ciki mai yawa ce

Cike da rauni, rauni irin wanda bawa baya iya boyewa gaban mahaifiyarsa ya karasa ya zauna kusa da ita sosai yana kallonta

Idannuwanta ta lumshe jin sa a kusa da ita, a hankali ta kura masa ido tana nazartarsa

Kansa ya sada kasa yana ta dane halin da yake ciki hakan ya sa a hankali ta saka hannunta ta dago kansa
Hannayenta biyu duka ta saka ta tare fuskarsa sai kuma ta janyo fuskar tasa hakan ya saka shi biyota ya dora goshinsa a kafadarta kamar yanda ta bukata

A hankali ta shiga taping din bayansa, muryarta a raunane ta ce" cry, cry, cry my boy "

Dan shiru ta yi sannan ta dora da fadin " basu kyauta ba, sun ci amanar zaman tare na shekara da shekaru bisa son zuciyarsu, ba laifi akai masu ba, ba tinzura su akai ba ta hanyar wulakanta su a zamantakewar da aka yi ba, niyarsu ne, jst cry SHAHEED , cry a jikin mahaifiyarka domin kaima mutun ne, dan kana sarki baya nufin zuciyarka bata anfani, dan kana sarki baya nufin baka jin rauni irin na kowa, ka zubar da hawaye ko zaka ji sanyi a zuciyarka sannan ka manta da lamarinsu, Allah ya gama saka maka tunda ya bayana maka komai, Allah ya gama yi maka komai tunda ya hanna su wulakanta ka a idannun duniya, CRY MY HAPPINESS "

Ai kuwa, magangannun da take tamkar tana bashi damar kara hasko irin zaman da ya yi da su, sosai ya yarda da su, sai ga rayuwa ta zo masu a haka daga shi har su, kwarai zuciyarsa ta masa nauyi , bukatarsa samun hawayen, da zai samu ma ya rushe da kuka mai tsanani kawai, sai dai rashin samun hakan ya saka shi ringa sauke tagwayen ajiyar zuciya yana ta kara yiwa komai fila fila yana mai baiwa kansa amsa cewar dan adam kennan, ka shiryawa komai daga gare shi,, a hankali ya ci gaba da jin nauyin nan na ragun masa, a fili ya furta" harda aikata kissa? Lalle shi kansa bai san karamar kiyayata da ya saka a ransa ta yi girman da zata kaishi ga halaka AMMI "

Ammi ta yi dan murmushi jin dumin abu a kafadarta, ta tabata abinda take so ya samu ne ya samun, wato zubar hawayensa dan ya ji sanyi a zuciyarsa, dan haka itama a sanyaye ta furta" Dan Adam kennan, mutun mugun ice kennan "

A hankali ya dago kansa yana kallonta, hakan ya bata damar saka hijab dinta tana goge masa fuskarsa, a sanyaye ta ce" har na tsawon wani lokaci zaka kilace ZULAIHAT a bangaren horo ? "

Sai da ya jima kamar ba zai yi bayani ba sannan ya ce " Idan aka gama bincike suka tabatar cewa laifinta kawai hada kai dan a kori kishiyoyinta ne ba dan a kashe su ba, idan aka tabatar ta hanyar vidios din da gareni a wajena cewar laifinta bai kai na aikata kissa ba, kuma kotu ta ga ba zata riketa ba ba zata yi kaso ba, zan yi kokarin turata masarautar Agadez ta gidan motar haya, zata sauka irin na kowa ta dauki abin hawan da zai kaita masarautarsu
Zan sanar da mahaifinta ya saka jakadiya ta tarbeta daga bakin gate na farko a yi wajen horo da ita zan bata damar zama tare da bayi na tsayin lokacin da zata gane rayuwa, domin kuwa tarbiyar da ta samu sai ta samu wace zata nuna mata ba zahiri aka nuna mata ba, na tabata duniya ce kawai zata ladaftar da ita ta horar da ita, domin kuwa idan ba haduwa ta yi ta kwana ta tashi ta ci abincin mutanen da take wulakantawa ba, ba zata taba gane yaren ba, gidan horon garin Agadez ya tanadi horo ne sak ba dan sarki ba bawa, zata je ta hadu da sabuwar rayuwar da zata hidimtawa kanta komai, daidai da shiga bayi sai ta bi layi kafin ta samu shiga, ba tsaftacen waje ba tsaftacen kayan zuba abinci bare dandannon da bakinta ya saba, ba waya ba tv ba wuta bare ta samu AC ko panka, daga nan zata fahimci darajar ni'imar da Allah ya bata ta yi wasa da ita, zata gane darajar masu hidimta mata, idan na gamsu cewar horo ta samu ba son kai ba zamu yi zama da ita da mahaifiyarta da mahaifinta, idan da hali sai ta dawo ta zauna a karo na biyu , aman fa AMMI sai dai a yi hakuri domin kuwa ba a matsayin uwar gidana zata dawo gidana ba, sai dai a sake dauran aure da ita dan kuwa na rubuta mata saki daya, dukan abin kunyar da take gudu zata same shi da izinin Allah sai mu ga irin daukan da zatai masa "

Ajiyar zuciya AMMI ta sauke tana kallonsa, sai kuma ta dan kawar da dubanta a hankali ta ce" mun yi magana da mahaifiyar Nadia cewar ta saka a kawo wanda zai kula da ita har kafarta ta warke, sannan ta tsorata matuka bangarenta ina ga ko a buda mata bangare na hudu, ko kuwa kawai ka mayar da matanka bangarenka Shaheed, idan Allah ya yi kun fara tara iyali sai su dawo bangarorinsu, aman a haka ni kaina na tsorata da mutun, dan kuwa su nasu ya fito, kamar yanfa ka fada ne gidan sarauta ba'a taba raba shi da ire iren abubuwan nan "

Shaheed ya gyada kansa yana sauke ajiyar zuciya

AMMI ta ce" yaya zaka yi da shi kuma sarkin bulala fa? "

Shaheed ya dan yi murmushi a hankali ya ce" Da ace haushina ne kawai yake ji, bai ji za'a cutar da ni ya yi shiru ba, harma ya bada tasa gudunmuwa ba, da sai na manta da na ji sunnansa a cikin magautana sai dai kiyaya girma take, kuma na tabata karuwa take a cikin zuciyarsa, dan haka zan yaye shi daga masarauta , zan fitar da shi cikin gari sannan na saka ido a kan lamuransa, domin kuwa koda bashi da lafiar aikata mugunta ga y'ayan mutane shi abin a zuciya yake, hanyoyin aikata mugun abun kuwa yawa ne da su, zan kai shi rayuwa cen kusa da baban gidan kaso, sannan zan saka masa ido sosai "

Cike da gamsuwa Ammi ke gyda masa kanta

Gannin sosai ya saku kan dazu sai ta ji dadi, dama ta tabata idan suka zauna zai ji sanyi sanyi a ransa, dan haka sai ta yi niyar kara saka shi nishadi ta hanyar fadin" gobe yarinyata ke gama sati gudanta, a gobe zasu yi zama ko yayane? "

Shaheed ya dan dago a hankali yana kallon AMMI, sai kuma ya yi dan murmushi ya ce" zasu yi zama aman ai sai Nadia ta samu lafia ko AMMI? "

Ammi ta ce" an fada maka ta ce ba zata iya zuwa bangaren mijinta ba dan kawai kafarta na yi mata ciwo ? "

Yanzun kam sai ya yi shiru aman fuskarsa a washe take ba a daure ba

Ammi ta ce" ina yarinyata SHAHEED?"
Chapter 115 · 0% Book details