← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 138

Sashe 56

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka kawai sai ta sauko itama ya kasance sunna zaune ne a saman cafet din zama irin na kusa da kusa kadan kafin ta rage muryarta sosai ta ce" ban san yaya aka yi ba daga nan da kwana uku lamarin wankar maza ya fara fice min a rai
Ka san wani abu?

Kansa ya girgiza yana kallonta, ta ci gaba da fadin" na fi kwarewa wajen wankar aljihunnan mazan da suka ajiye mataye a gida suka zo suke bin mu, sukan bude bakin aljihunsu su kashe mana kudaden da a shekara ba zasu iya anfanar iyalansu da su ba,
Ina matukar jin dadin karbar kudin wanda matarsa ta tarbe ni ta zageni
Shin ka san cewar sunana bashi da kyau a waje?
Dan bakinta ta yatsina ta ce" kama sani ne domin wa'inda ke zagin nawa da irin haka da yawansu matan da na zame masu tashin hankali ne, sai samarin da na raina shekarunsu irinka
Ban san yaya aka yi na raina mai kananun shekaru ba
Ni din ce mai rigima
Ina famma da fitina da yawa hakan ya sa nake tunanin anya kuwa namiji mai kananun shekaru zai'iya hakurin halayana?

Matsota ya yi sosai yana dubanta ya ce" kannanun shekarunna ba su zasu hanna na kasa hakuri da halayanki ba Najeeba
Baki san cewa babar kadara ita ke saka biyaya dole ba?

Najeeba....

Ya fada a sanyaye yana mai kara dora mata takardar nan tare da wata takardar itama ta bankin ce sannan ya hade hannayensa ya ce" ba rokona kika yi ba, ban kuma nuna zan iya da dawainiyarki dan kin kasance mai son kudi ko wani abin ba
Abinda na sani *MACE* yar gyara ce, dole a gyara mace, dole a kashe mata kudi idan ana so a ganta tsaf tsaf tsaf da ita, ba wai abinda ya fi karfina na tarka ba, kowani mutun kan yi daidai karfinsa ne
Najeeba, da kwaliyarki, da kyan tsarinki na ganki, a yanzu da nake son kasancewa da ke ina so ki zauna da ni daya kwal, hakan ya sa nake jin zan iya maye maki gurbin sauran samarinki ta kowani fani, zan iya da kowace lalura taki ta yau da kulun, ki yarda da ni ki amincewa motsina hakan zai saka na kara gyara tsayuwana na faranta maki

Murmushi ta yi har cikin ranta, itafa ta mayar masa ne dama dan ta ga iya gudun ruwansa sannan ta nuna masa kudinsa basa gabanta, aman ina ita ina nuna bata son kudi? Ta fada ta kara tana son kudi yanzu tana son su gobe
Ba wanda bai fito nema ba
Ba wanda idan aka mika masa baya karba ba
Halal take ci ba haramun ba
Domin bata je ta baza haja an kwasa an biyata ba
Da dabararta take samun kudi a wajen du wanda ya saki bakin aljihunsa
Da wayonta suke wanyewa lafia da mutun
Bata taba zina ba
Bata taba kusanta kanta da zina ba
Ko rayuwar shan minti ba'a yi da ita
Takan saka kaya wanda ranta ya so aman idan ka yi gigin tab'a jikinta zaku samu matsala kai da ita koma waye kai
aljihun gara kuwa zata wanka har zuwa lokacin da zata shige daga daka.

D'an murmushi ta masa sannan ta k'ara gabatar masa da abubuwan da aka kawo masa dan tarbarsa aman ina shi ya shagala bin motsinta yake da kallo yayama za'a yi ya shigo da wasa ne shi?
Tabas bai shigo da wasa ba, kuma sai ya daki wannan sha'ani da zafi zafi.

A hankali ya saka hannunsa yana shafa wajen hancinsa, ji yake har kamar wani hucin zafin balaki na cin k'owata gab'a ta jikinsa har zuwa cikin k'wak'waluwarsa, shin ina kunya da kawaici irin na y'a mace? Ina girman daraja da mutunci irin na y'a mace? Ita bata da su tun haihuwarta ko daga baya ta saka k'afa ta shure? Wani dalili ya sakata shurewar saboda kud'i ko dan wata buk'ata da ta kasa hakuri? Shi ya sa a rayuwarsa yana addu'ar idan Allah ya bashi y'aya mata zai aurar da su tun sunna k'ananun shekaru ba dan komai ba sai dan kar su zama gandama gandaman yan matan da ko sun je da budurcin to fa ya samu rauni.

Sai yake jin wani irin zafi a cikin zuciyarsa na lamarin, yana jin abin har cikin k'ok'on ransa, me ya sa a cikin yan uwanta ta kasance wace ta fi sauran irin wannan halayya?
Tabbas suma Dayabu ya shaida masa suna da samari, sai dai shi idanuwansa basu tab'a kama masa su da wani lamarin da zai zargesu ba, me yasa take irin shigar nan sannan take sakin jikinta da kowani k'ato ta yi hira ba damuwa ba wani d'ar? Me ya sa ta b'ata rayuwarta da yarintarta take harkar maza ido rufe? Me ya sa kika yi abinda kika yi har ya kasance na mayar da ke abinda nake harin na kama tsamo tsamo da laifi?

A bayyane sannan a sanyaye ya sada kansa muryarsa da rauni ya furta" Haba *NAJEEBAT*, me ya sa kika saka min madaukakiyar tsanarki ta hanyar zubar da mutuncinki a wajena kasancewata yayanki sannan sarkin ki?
Meye ribar da zaki ci a nan gaba cikin gidan duniya? Waye zai iya aurenki ya rik'e ki da amana bayan ya san wacece ke? Kaico da zamanin da zina ta zamo ado ga al'umma, kaico da wannan zamanin da mutane kan iya dukan k'irjinsu su taka da tink'ahon su d'in yan iska ne.

Ajiye tablette d'in ya yi ya mik'e daga wajen, domin ya had'u da b'acin ran da yake gudu, tabbas yana jin zafin irin abubuwan da take yi ba dan komai ba sai dan ta kasance yar uwarsa, y'a a wajen auntynsa aminiyar anmynsa wace take matuk'ar k'aunarsa,
taa d'in k'anwar DAYABU ce d'an uwa kuma amininsa wanda suke hirar sirri da junna harma ya haye masa, ita din y'a ce a wajen Abih d'insa, daga ita har yan uwanta yanai masu soyayya ta yan uwantaka, shi d'aya amynsa ta mallaka, yana da yan uwa yan mata wajen sauran matan mahaifinsa sai dai babu wata shak'uwa sosai a tsakaninsu ko dan sunna nesa ne?
Yana jin zafin du abinda za'a ce su suka aikata domin yana masu kallon y'ayan da Anmy ta haifa.

Hira suka sha har bayan magariba ita da aka ce ta salame shi kafin sallah magariba.

A daidai lokacin da ta zo shiga b'angarensu ta ringa jin hayaniya da kuka sama sama hakan ya saka gabanta ya yanke ya fad'i ta afka da gudu dan gannin abinda ke faruwa.

Mai martaba ne zaune a kujerar da idan ya hau kowa kan zauna a k'asa.

Yau ma Abih ne zaune, matarsa gefe tana rusa kuka da Anmy cen gefe tana jan carbi, sai yan uwanta dake zazzaune kawunansu du a k'asa kusan su dukansu.

Tunda ta afko d'akin a tsorace sai da ta bi kowa da kallo, hakan ya saka sukai ido hud'u da shi.

Gabanta ne ya kwanci kwanci ya fad'i sakamakon irin yanda idanuwansa suka kad'e sukai jajajir ya kuma b'alla mata kakausan hararan da ya sakata jin tana jin fitsari.

Da sauri ta kai k'asa a wajen da take tsaye kanta a k'asa tana jin har jikinta ya d'an fara rawa rawa dan irin fad'uwar da gabanta yayi sakamakon tsagwaron b'acin ran data gani a tattare da shi sai ta shiga taitayinta ta sadda kanta baki d'aya ta had'e hannayenta a saman cinyarta bata kuma d'agowa ba.

"Allah ya k'ara maka lafia wani irin zama ne wannan? Wace irin rayuwa ce wannan? Daga na fad'i gaskiya shikenan ya tsintsinka min mari, ya hankad'a ni na fad'i gaban goshina ya tsage bayan ya d'auki kusan kwana goma yana min gabar da ban san abinda na masa ba nice ya dace na masa gaba dan a gabansa NAJEEBA ta shak'e min wuya ta marar min fuska yar uwarta na rik'e da y'ata da na haifa, yayansu na kallo aman bai d'auki wani mataki a kansu ba bayan a ranar da ka mana shara'ar nan ne. Daga na tambaye shi inda Zahrau ta je wai da gaske ta auri sarkin agadez shine yake ce min eh Allah ya yi, ai ta Allah ba tawa ba?"

Sasautawa ta yi tana k'ara sada kanta domin ba ido da ido take maganar ba ba zata iya kallon idanuwansa tayi bayanin nan ba, cikin kuryar kukan da son lalle sai ta fasa k'won daya tsaya mata a wuya ta ce" Allah ya taimake ka, shine yau MUTALLAB zai bud'i baki ya ce min na daina sheganta masa y'aya dan ba shegu bane sai dai na nemi shege wa wajen ubana?"

D'agowa tayi tana kallon yaren daya bayan daya ta ce"
*Allah ya ja da ranka shi ya manta tasa shegiyar ne?"*

A firgice du suka dago sunna dubanta banda wa'inda ta yi hakan dan su ji sai yan uwansu da ko a ka basu damu ba , tun daga DAYABU, DA UMMU, DA UMMULKHAIR, DA NAJEEBA wa'inda suka rigaya suka mallaki hankalin kansu wa'inda ta d'aukaka rigimarsu ne dama dan tana so sai ta fasa sirrin da ya fad'a mata ya rok'eta kan ta b'oyewa y'ayansa dan yana jin matsananciyar kunyarsu, yana jin kunyar ranar da zasu ji irin abin nan su kale shi da shi, ya boyewa duniya da y'ayansa yarinyar nan ba dan komai ba sai dan gudun a goranta masu, ya san mutane da izgili da neman fitina, gashi Allah ya bashi y'aya mata har goma sha shida baya so sakamakon hakan su ringa samun matsalar rayuwa, ya fad'a mata ne dan ya d'auka ita d'in tunda ta kasance matarsa to fa sirrinsa ce.
Chapter 56 · 0% Book details