← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 138

Sashe 129

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MARDIYA da kanta ke hayaki sakamakon labarin da aka kawo mata cewar Abih ya gyarawa UMMU gidansa dake Jeune cadre ya zuba mata kayan alatu tamkar gidan zai tsage dan kaya, ga wani irin fita daban da ya yi a anguwar, bata yarda ba sai da ta je ta ganewa idannuwanta duda mai gadi ya hanna mata shiga aman daga inda take ta ga abinda ta gani shine ta koma masa ta same shi gadan gadan da tashin balagar rashin kunya, ya mata banza shine ta ce zata zo ta sammu Ummun su yita ta kare, ba zata amshe mata miji ba bata isa ba tsohuwar banza kawai

Gadan gadan ta idasa gaban Ummulkhair ta ce" Ke ina tsohhuwar guzumar uwarki take? "

Ido Ummulkhair ta zarro tana kallonta, ita dai bata da fada irin nasu, bata iya hayaniya sosai din nan ba, Ummukulsum ta fi ta iya maida martanin rigima, har solofiyo suke ce mata ita da Zahrau, hakan ya sa ta dan rike kafar NUSAIBA dake daidai cinyarta tana kallonta ta ce" Wace haka kuma Mardiya? "

Mardiya ta matso da wani irin balaki ta hankadata, bata shiryawa gannin hakan ba hakan ya sa ta je baya gaba dayanta ta fadi da bayanta saman Nusaiba jikin karfen kujerar falon

Wani irin tartsatsin ihu Nusaiba ta saki kafin ta dauke dif

Da gudu suke firfitowa daga kofa daban daban

A guje suke nufo yar uwarsu dake yashe a kasa tana ta kokowar son kwonto Nusaiba da ta kara nauyi a bayanta sannan gwuiwar hannunta na zubar da jinni

Da wani irin gudu AMMI ta idasa wajen ta shiga son kama su hankalinta tashe bakinta ya kasa furta komai
Da wani irin sauri UMMU ta ture NAJEEBA dake son karasawa itama aman sam bata iya gudu ko sauri ba hakan ya sa take wata tafia tingil tingil hankalinta tashe
Mardiya dake tsaye idannuwanta rufe ta ce" Baki dayanku bakinku a hafe ko? Bayan auren cin amanar da son zuciya kuma shine za'a kaita sabon gida tana tsohuwa ni a barni a gidan da yara suka tashi suka lalata? Walahi ban ga yar iskar da ta isa ta shigar min gidan miji ba! "

Tas , fuskarta ta amshi wani irin fitinane, mahaukaci, zazafan marin da ya sakata kwala ihu ta juyo tana kallon kantamin hannun da ya sauke mata biyar

Bai wata wata ba ya kara dauke fuskarta da wani tsadaden, wulakantace, fitinanen marin da ya sakata yin luuuuu cike da mahaukacin mamaki da al'ajabi ta kwala ihu ta ce" Kan uban cen kaya sa, ni ka mara? Ashe kuwa zaka iya marin Mutalab da MARIAM? zaka iya marin uwarka mahaifiya? "

Da wani irin hauka hauka ya shiga kunce belt din dake daure a kugunsa , gannin haka Najeeba, da Ummukulsum suka rigaye shi afka mata, kan kace meye wannan kanwarsu bakuwarsu da yake itama jinnin shuwan ne ke yawo a jijiyoyinta ta afka masu, yaren suka ringa neman wajen kai mata duka

Ummu ce ta daka masu wata irin tsawa mai hade da gunjin kuka, AMMI ta dago da NUSAIBA a hannunta wace hannayenta ke yin lagai lagai muryarta cike da kuka ta ce" Ta kashe ta, ta kashe yarinyarta ta cikinta, ta kashe Nusaiba! "

Gaba dayansu ne suka idasa juyowa wajen iyayen nasu a tare, cikinsu mutun uku ne suka zube a summe sakamakon gannin irin jinnin dake zuba daga keyar NUSAIBA,

Abih da shigowarsa kennan a hankali ya silale a wajen zaune dabas ya dora hannayensa bibiyu

Yaya Dayabu ya daga kafarsa ta hagu ya fara takawa tana masa nauyi ama a haka ya ringa janta har ya karasa wajen AMMI dake kuka ido rufe tana maimaita innalilahi wa'ina ilaihi raj'une

A hankali ya dora hannunsa wajen jinnin yana kallon yanda idannuwan yarinyar suke kakafe sannan jikinta ya dauki wani irin sanyi harta da fatar jikinta ta yi fayau

Da sauri ya saka dayan hannun nasa yana gurgusa gashin kanta , muryarsa hade da wani ihu ihun kuka yake fadin" UMMU, wayo mun shiga uku, Ummu ku tare jinninta kar ta mutu, Ummu wayo ta kashe mana kanwarmu, ku kama mana kar jinninta ya kare, wayo Nusaibata, ku tare jinnin nan ya bar zuba kar ya kare AMMI, wayo Abih, Wayo Ummulkhair, NAJEEBA, wayo Bilkissu, wayo Najeeb zo ku tare jinnin kanwarmu na zuba daga kanta"

UMMU dake kuka ta saka hannayenta tana janye nasa, muryarta a ciki dan tsabar kukan da take ta furta" innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, Allah ka yi mana maganin masifar da ta fi karfinmu, Allah ka jikan yarinyar nan, ka sa ta huta, DAYABU ka bar dannawa Nusaiba ta rasu fa baka gani ne? "

Qi kamar wada ta kara rikita dakin, gaba daya wa'inda ke jijiga wa'inda suka summanma sai suka kara rikicewa, Najeeb kam ya rukunkume mahaifinsa ya cusa kansa cikin kirjinsa yana kuka dan shi tsorata ne ya yi da gannin jinnin dake fita daga kan kanwarsa wace shekara daya ce tak tsakaninsu yanzu haka da kokowa suka rabu ta fara rigimar da ta zame mata jiki kwana biyun nan, domin haka kawai zata kama kuka tana dora kanta a jikin du wanda ke kusa da ita, kuma jikinta lafia kalau ba rashin lafia ba ba komai ba, hakan ya sa Ummulkhair ta goyata suka fito falo shi kuwa ya kwonta ya shiga baci

Wani irin ihu DAYABU ya yi, a lokacin da NAJEEBA ta fashe da wani irin kuka hannayenta duka biyu saman kanta tana nuna Mardiya da ta yi wani irin wuri quri hannayenta duka biyu a saman kanta tana maganar da ba'a jin me take fada, ama da alama ta zauce ne dan kuwa magangannu ne take ta saki tana kuma kallon du wani mahalukin dake wajen

Kukan kuran da Dayabu ya yi ya damki wuyan Mardiya ya kaita kas hannayensa bibiyu a rike da wuyanta ne ya saka Abih zabura da wani irin gudu yana kokarin bambare Najeeb daga jikinsa

Ummu da gudu itama ta yi kansa tana furta" Mun shiga uku ku kawo mana talafi, Dayabu saketa, saketa kar ka dora laifukanta a kanka "

Shi kuwa ido rufe haka yake furza yawun bacin rai yana fadin" kema sai kin bita, zan kashe ki da hannayena kowama ya huta da jarabarki, sai na halaka ki "

Ido ABIH ya zaro gannin Najeeba hannunta wuka ne ta warto daga kicin da gudun balaki, sai ya rasa inda zai nufa
Da sauri AMMI ta juya ta ajiye Nusaiba kusa da Ummulkhair da ta summe tun da aka furta Nusaiba ta rasu ga jinni na fita a hannunta itama da gudu ta yi niyar tare Najeeba

Basu ga shigowarsa ba, sai hannun Najeeba mai rike da wukar nan da ya tare

Rike hannun ya yi da dan karfi hakan ya sa ta saki wukar

Wukar ya mikawa sarkin dogarai dake tsaye jikinsa na tsuma kafin da wani irin sauri ya zagaya wajen da tuni Mardiya ta summe dan azaba ya kama hannayen Dayabu ya shiga kwalkwata da wani irin karfin da ya saka DAYABU dago da dubansa yana kuka kashirban yana kallon mai bambare shin

Irin yanda zuciyarsa ke bugawa har ana ganni ta makogwaronsa ya ringa girgizawa SULTAN SHAHEED kai, bakinsa ya buda yana cracking ya ringa fusgar magana ya ce" Ta, ta kashe min kanwata, ka barni na kasheta........dama so take du ta hahahahalaka mu, shikennan nima sai a kash...................n" kasa karasawa ya yi, jikinsa ya ringa saki a hankali ya lumshe idannuwansa ya taho zai fada mata

Tare shi SHAHEED ya yi hakan ya sa Sarkin dogarai da gudu ya karaso ya kama shi ya yi saman babar kujera da shi

Sai da ya bi falon da kallo, daya bayan daya kafin a sanyaye ya furta" Ammi ku shirya ta , Allah ya sa mutuwa hutu ce a gareta"

Ya maida dubansa wajen ABIH dake tsaye kansa sade kasa, a hankali ya karasa ya dora hannunsa na dama gefen kafadar Abij ya ce" ABIH "

ABIH ya dago da kyar yana kallonsa, a hankali ya ce" ABIH ka yi hawaye, ka zubar da hawaye ko zaka ji sanyi a cikin zuciyarka, sannan ka yi hakuro, ka yi hakuri, ka yi hakuri ABIH, taka kadarar rayuwar kennan, ka salaceta ka sakata a makwoncinta da hannayenka sannan ka yafe mata, yarinya ce duda haka kowa ya yafe mata, muma namu lokacin muke jira, ba wanda ya san musababin abinda zai kaishi kiyama sai Allah, dukan mai rai kuma mamaci ne Abih "

ABIH ya kuma busar da hucin dake cikin zuciyarsa

Zuwan likitoci ne ya saka SHAHEED ya gyara tsayuwarsa ya shiga yi masu nuni da su duba mutanen dake zube a summe, duda irin yanda suke ta kallonsa da son gaskata wai da gaske kamanin wanda suke ganni a gabansu ne SULTAN SHAHEED?

Najeeba dake tsugune kanta a jikin hannun Ummukulsum ce ta dago a hankali ta mike tsaye da niyar barin wajen, sai dai wani irin luuuuu da ta yi zata zube ne ya saka shi daga kafarsa da sauri ya karasa ya tare ta, lokaci daya kuwa Sarkin dogarai ya shiga buga tsawar kowa ya sada kansa

Da kirjinsa ya hadeta, a hankali ya karasa saman kujerar dake da girma ya zaunar da ita
Kafafuwanta ya rage tsayinsa ya dauke a hankali ya dora saman kujerar , kafin ya gyara mata kwonciyarta yana gyara mata kitson kanta
A hankali ya mika hannunsa ya dauki hijab din da ya tabata na Ammi ne ya luluba mata
Hannunta ya rike na dama, a hankali yana shafa gaban goshinta , muryarsa a sanyaye ya furta" Kar ki daga min hankali, ki karfafa min gwuiwa ta hanyar zama jarumata, ki yi mata adu'a idan ba so kike du mu kwonta ba BEEBAH "

NAJEEBA t lumshe idannuwanta, hawayen da suka bushe ne ta ji sunna harhada kawunansu, a hankali suka bale mata ta kai dubanta kan fuskarsa ta ce" Shikenan ta kashe min kanwata? Nusaiba ta rasu? "

Hannunta ya kara jimkewa ya furta" ki yi ta hailala BEEBAH "

Idannuwanta ta mayar ta lumshe

Sakin hannun nata ya yi ya mike yana kallonsu
Chapter 129 · 0% Book details