← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 138

Sashe 79

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kin san menene? Aunty zan baki mamaki idan na furta maki dalilin madaukakiyar tsanar da ta fara yi masa harma ta ringa neman makusarsa ido rufe shine daga wani fada da suka yi da matarsa ta budi baki ta ce da ita *BAK'A, MAI BAKIN ANIYA, KIN MATSAWA RAYUWATA KAMAR WATA KISHIYARKI, BAYAN MIJINA KO A KAFARSA AKA KULA BAK'A ZAI CIRE YA YAR NE, BAKYA GABANSA HAKAN YA SA NAKE TAUSAYA MAKI!*

NADIA ta yi murmushi tana kallon Auntynta ta ce" a ranar da suka suka yi fada a kan abin nan sai da ta ringa maimaita kalmar nan sai sitin da uku ina irgawa

Hannun Auntyn ta riko ta ce"

Happy juma'at🥺

*Yan uwa ina k'ara gode muku, Allah ya bar k'auna.*🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

41

Ta ce " Aunty, a kan me zai mata zafi har haka?

Bayansa, su ranar da aka ce ana taro na gidansu zaki ga ta rasa me zata saka, a saloon ta saka wannan ta cire
Mitarta daya ce" ka je ya ringa hararanka kamar wanda ka fito tsirara

Auntynta ta girgiza kai ta ce" ke dai ta baki tsoro ne, ai Nadia komai isarka da tunanin kai din wani kwaro ne ai akoy gabanka, so nake y'ata ta kasance jarumar Sarki Shaheed, so nake baki daya ki doke su! Nadia, wai kin ga fuskarsa? Yaya kamaninsa suke?

Nadia ta yi wani irin tsam kafin ta saki murmushi ta saka hannayenta ta dafe kumatunta, a bayane ta ce" tabas rabo ya kaini zama matarsa, in ba haka ba ban isa na shigo layin wace zai iya duba ba

Me kike nufi? Auntyn nata ta tambaya cike da zakuwa

Nadia ta ce" Aunty, walahi rawanin nan da yake shine rufin asirinmu, da ace buda fuskarsa yake da kirarsa da mun shiga uku da mata, Aunty, Shaheed baki ba zai fadi kamaninsa ba,

Murmushi ta yi ta mike ta nufi bayi dan tara mata ruwan wanka da gashi

Da kallo ta bi dakin a karo na biyu, Ac sai yi yake dakin sanyi sosai

Aunty na fitowa ta ce" Aunty, ba'a kashe Ac din nan ba tun jiya?

Kamata ta yi ta mike suka nufi bayi

Sunna shiga ita da kanta ta cire zanninta ta ajiye, auntyn nata na jiranta dan ta san sai sun sha kokowar zama a cikin ruwan dumin ta ce" wato Nadia bacina na jiya, wani irin baci ne na yi mai salama
Daidaya nake fada maki Nadia na yi a dakin cen
Ac na hura kofofin fatana, Nadia baci ne na yi da salaba , lokacin sallah na yo tar tar a cikin kunnayena kiran sallar tamkar a dakin nan,
Na so na ki tashi na kara juyawa sai dai cikin ikon Allah irin karatun da aka yi tamkar a azumi ya hana min rintsawa
Nice yau da bin masalaci sallah? Lalle Nadia wannan gida baban gida ne
A yanzu na daina zagin dangin kishiyarki, koda kuwa suma daga gidan sarautar suka fito aman na daina zaginsu da suka zo wajenta suka tare

Nadia, ba yinwa, ba kishirwa, ba shara, ba wanke wanke, ba wanki bare guga, Nadia ba zagi ba duka, ba zafi, Nadia wajen kwonciya a gyare ga wani kamshin turaran wuta da basa gajiya da sakawa
Nadia ina mike ina shating ina hasko kaina
Haba ina, zan je na duka na yi masu salama na dawo na taya ki zama, Nadia ni dai ko cin uwar taki Najeebar zata yi ko? Ba inda zaki, maganar tafia ki bara mata mijima bata taso ba

Nadia na daria tana dan tsoma kafarta a ruwan da ta ji ya yi zafi sosai ta ce" Aunty, ni sulhu nake nema da Najeeba, ni kaina a jiya kafin na san waye shi nake fadin na bara mata
Aunty, ni kam zaman lafia nake so da Najeeba, aman ba zan iya barin SULTAN ba

Daria ta yi ta ce" ko ke fa yar, wato kin ga maza kin kasa kawar kai ko? Wahalar bata firgitaki ba?

Nadia ta ringa daria ta ce" ta firgitani, aman kuma ta kara min kwarin gwuiwar zama a shashena...
........................................

Ruwa masu zafi ta hada itama kafin ta yi kokarin kama Najeeba

Tun daga yanda take kin son cire doguwar rigar jikinta ta dan fara kokonto

Bata kawo komai kanta ba dai har ta talafa mata ta shiga ruwan nan

Irin zaman da ta yi a cikin ruwam ya saka gaban Zahrau mumunan faduwa

Da sauri ta mayar da hannunta na hagu ta kara taba zafin ruwan dake dauke da abubuwan kamshi

Tabas yana da zafin da ko lafiarka kalau zaka ji tsoron shigarsa bale ita da take tunanin miji ya zo mawa

Da sauri ta kalli Najeebar, abubuwan da ta gani saman shinfidar a bushe fa? Sannan ita kanta a jikinta ta ga abubuwa su fa na meye?

Duban fuskar Najeebar ta ringa yi kafin a sanyaye ta ce" gardama kikai masa Najeeba ko me ya faru da ke?

Najeeba ta kai dubanta kan fuskarta
Haushi ya sakata kin yin magana a wannan lokacin sai da Zahrau ta kuma fusta"kin ga, ki rufa min asiri ki bani amsar dake min yawo a raina, ki rufa min asiri ki bani amsa yaya zan saka ki cikin ruwan zafi haka baki ji zafi ba? Bayan na ga alamun da suka nuna min mijinki ya zo gareki?

Shirun da ta kara yi ne ya saka Zahrau kara shiga yannayi na damuwa, fuskarta na rikidewa zuwa kalar wace zata fashe da kuka ta budi bakinta a hankali ta ce" meye damuwarki? Hala ba ke ya zowa ba? Hala da wata ya tara a ranarki?

Najeeba ta yi rauraurau ta budi bakinta da yannayi na bacin rai kasa kasa ta ce" me kike son ji? Yawan maganana da bacin rai na? Me kike son ji? Na kuma maimaita maki shirmen da ba yanda zaki iya yi min?

Hannayenta dake kusa da nata ta riko ta dago tana kalonsu ta ce" ban taba gannin wulakanci irin na jiya ba, tabas ya gama anfani da Nadia ya dorani saman datin jikinta

Ido Zahrau ta rintse da karfi tana kawar da kanta

A sanyaye ta lumshe idannuwanta tana jin du wani waje da harshensa ya ringa bi a jikinta kafin ta ce" Zahrau, kin san wani abu?
*NA TSANE SHI!*

Zahrau ta lumshe idannuwanta itama kafin ta janye hannunta ta mike a hankali ta ce" ina jiranki, ki gama ki fito

Da sauri ta juya ta fita, ita kuwa ido ta lumshe ta kara zama cikin ruwan nan, tabas ya ci galaba a kaina a yau,
Ya bi min jikina da kallo,
Idanma da gangan ka lashi fatar jikina SHAHEED na maka alkawarin sai na saka ka son lasarta da hauka hauka, Idanma da zumar wani lamari na zuciyarka ka hade lebena da naka Shaheed, Na maka alkawarin sai na haukata yawun bakinka
Shaheed sai na zabura mafarkin ka,
Shaheed sai na hana maka sukuni!
Na rantse matanka ba su ne abokan gabana ba! Domin na yi imanin WA MAN TASHA'UNA ILA AN YASHA ALLAHU RABUL ALAMEN.

Zahrau na fita ta ci karo da Ummu zaune tana kallon kofar

Ido hudu suka yi da junna, Zahrau ta sada kanta ta yi niyar fita a dakin

Ummu ta yi murmushi ta ce" Zahra, zo mana

Zahrau ta fasa fitar ta karasa wajen Ummu tana kallonta

Ummu ta kuma yin wani murmushin ta ce" ina zaki je ki fadi matsalar yar uwarki? Ba dai Anmy zaki fadawa ba?

Zahrau ta dago tana son goge hawayen dake cikin idannuwanta a sanyaye ta ce" Ummu, tana cikin damuwa, yaya DAYABU ya fada mana sai mun kai zuciyoyin nesa mun kawar da kawunnanmu, inaga shima dan ya kauracewa haduwa da ita ne yake iya hakurin gannin hawayenta
Ummu, meye mai karfi tsakaninsu haka? Na zata Najeeba zata iya hakuri, aman Ummu aminiyarta Nadia fa ya aura, sannan a jiya Nadiar a bangarensa ta kwana, ba abinda ya faru da Najeeba

Ummu ta lumshe idannuwanta tana kokarin murmushi a bayane, a sanyaye ta ce" Eyah, shine zaki je ki fadawa Anmy haka?

Zahrau ta bar hawayenta sauka a fuskarta sosai ta ce" na gaji ne da gannin yannayinta a haka, kanwata ta kasance macen da a wajenta nake daukan darusan kecewa da daria komai bacin raina, ita ke kara saka min kaunar na rayu a zuciyata, ita ke kara saka min nutsuwa idan har hankalina ya tashi, Ummu, na gaji da ganninta tana hawaye a kan auren nan, na ga alamun shima ba so yake ba, itama haka to a kan me zasu yi ta wahala har haka?

Murmushi ta yi ra kamota ta zaunar da ita tana hangen yan kafafuwan Najeeba daga wajen kofar da alamu ta karu tana jin me za'a ce

A hankali ta ce" shine zaki fada mata ta raba auren?

Zahrau ta kuma sauke ajiyar zuciya harda yar shashekarta ta ce" ashe shine wanda ke tafia suke haduwa a stade wajen da take zuwa shan iska? Shin bibiyarta yake yi ko menene? Ummu, idanma aurensu ba mai mutuwa bane a sama mata yancinta, ba zan iya motsawa nan da cen ba har sai na ga abinda zai faru ya faru da kanwata, Ummu, a wajen Najeeba muke koyon murmushi komai bacin ranmu, ba zan yarda farin cikinta ya gushe daga rayuwarta ba, walahi su Ummulkhair jiya kuka suka yi kamar me, Ummu yaya kwana ya yi muna mesage da shi hakan ya sa tun karfe shida yana gidan nan , mun yi niyar yau mu hadu mu duka mu sakata murmushi sai gashi ya kara bata mata?
Chapter 79 · 0% Book details