← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 138

Sashe 53

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa ya yi tsaye hakan ya bayanar da irin tsayinsa,
SHAHEED ya kasance namiji daya kwal da babu irinsa
Yana da tsayi daidai misali,
Shaheed ba shankalale bane kuma ba rubdede bane
Jikinsa ya kasance jiki kamame mai tsafta
Kirjinsa yana da fadin gaske sannan cikinsa ba a shafe bane yake luwai kamar na mace aa, a shafe yake aman da wani gida gida irin na masu daga karfen nan
Ya kasance mai hannaye masu tsayi da kauri, damatsunnan hannayensa tamkar na dan dambe wanda baka gane hakan sai ya saka irin rigunnan nan na gudu
Irin yanda ya kware wajen sarafa doki haka ya kasance tamkar doki a kowani fani, sam bashi da wasa ko laso laso
Fuskarsa dauke take da gira mai yawa wace har ta kusan hadewa da yar uwarta baka sidik,
Idannuwansa kuwa manya ne ba fici fici ba masu dauke da gashin ido mai yawa baki sidik, sannan sunna dauke da kwali mai ruwan maroon mai duhu wanda yake kyalkyali ko a cikin duhu ne
Hancinsa yana da dan girma sannan yana da karan hanci mai tsayi
Lebunansa masu fadi ne kadan sannan pink color ne yas da su ga taushin tsiya
Yana da cikar gashi irin na larabawa domin ya dauko gashin Anmy ne wanda yake yawan aske shi sai dai duda haka ya ajiye kyakyawan sajen da ya je masa har wajen habarsa ta fitar da san gemun da yake dan ragewa yana gyara shi yana kara hawa fuskar yasa das da shi ga baki ga kyalkyali
Cinyoyinsa sunna da tsayi da wani irin tauri irin na wanda ya sabawa jikinsa da sport sannan kaurinsa masu kauri ne da tauri suma a rike suke a jikinsu
Yana da manyan tafin kafafuwa irin na manyan mutanen nan na da duda basu da tuwo sosai

Cike da kasaita ya ringa takowa ya yi taku uku ya kasance tsaye kikam a gabanta hakan ya saka ta zama wata yar firit da ita tamkar wace zai yi kujera da ita

Kirjinsa ta dan kurawa ido kafin ta dan matsa kusancinsu ta dago da kanta tana kallonsa da dan mamaki ta ce" kanshin turaran nan, a ina ka samo shi?

Idannuwansa ya lumshe ainun a kanta a kasan zuciyarsa yana furta lale na yarda baki da kunya ko daya yarinyar nan, muryarsa da ta dan fara kausasa ya buda ya ce" kin san shi ne?

Fuskar tasa ta dan kurawa ido kafin ta cire dubanta daga kansa ta mayar gefe tana mai sakin ajiyar zuciyar da bata san dalili ba sannan ta ringa dan girgiza kanta

Fitowar dogarin dake tare da ita baban ya saka shi cije lebensa na kasa yana son kara kawar da fuskarsa irin na dazu don kar a je ya gane shi a hankali ya furta" na yayana ne na dan fesa, turaran ne na birge ni

Dan murmushi ta yi, bata ce komai ba, karamar eayar dake aljihunsa ya ciro ya mika mata yana kallonta ya ce" tunda yau kin aminta da abotakata, saka min number ki

Wayar ta kai dubanta sama, wata irin waya ce yar karama mai sulbi sannan fara ce kal kamar hannu bai taba tabata ba bale a yi tunnanin ana ajiyeta a wani waje

Tabas mutumen nan yana da tsafta, yana kanshi uwa uba saukin kansa ya saka eh lale zata iya zumunci da shi

Kwarai ta ji dadin da ba soyaya ya nuna mata zai yi da ita ba, domin kuwa a tsarin rayuwarta farin mutun baya cikin tsarin namijin da zata iya soyaya da shi ko na second daya

Kuma kai dubanta ta yi kansa, mutumen na tare da wani irin kwarjini, girmansa ya bata mamaki irin yanda farinsa kuwa yake har ya zarce matan nan masu karin mai a kan nasu

Wayar ta amsa ta saka numberta wace idan an kirayeta ana samunta ko wani irin time kafin ta mika masa ta juya tana daga masa hannu

Daga inda yake tsaye ya bita da kallo inda dogarin ya koma da gudu ya bude mata wajen zama ta shiga ta zauna

Wani uban tsaki ya ja yana yin kwafa ya koma ya zauna da wayar a hannunsa wada ta saka numberta

Ni SHAHEED ni ne yaro? Sam halitata ce bata yi mata ba? Wani murmushi ya saki yana dan kara cije leben nasa na kasa cike da takaicin abinda ta fada
Haka kawai ya ji yana jin haushin kalamanta

Kansa ya dan kara girgizawa yana mikewa dan karasawa ya huta a ransa kuwa fadi yake" sannu sannu bata hanna zuwa yarinya, abinda na yi niya a kanki sai na cinma burina marar kunya!

Sun hade a falo sun yi hira kamar yanda suka saba, Anmy na tare da su tana jara hankalcewa da yannayinsu baki daya, sai Ummu da ta wuni da ita tana ta kokarin gannin ta fitarwa da yarinyar abin daga ranta , ba laifi ta dan kara sakuwa kan yawan shiru da kukan da ta dauka na kwana biyu

Da sasafe wajen karfe tara, Najeeba ce tsugune kusa da kafar Anmy bayan sun kara gaisawa cikin kara sada kanta ta ce" Anmy, dama saman maganar tsayar da mutumen da aka ce din nan ne, akoy mutane biyu da muke tare nake son a rokar min alfarmar su fara zuwa a cikinsu sai a ware guda in sha Allahu

Da sauri ta dubeta, da wani yannayi mai cike da rashin jin dadi, saurayi? Zance? Kennan tana da wanda take so ko me?

A hankali ta ce" Najeeba, kina da wanda kike so ne a cikinsu?

Najeeba ta kara sada kanta irin kana jin kunyar nan ba zaka iya yin magana ba, hakan ya kara sanyaya gwuiwowin Anmy
Muryarta kasa kasa ta ce" ki basu dama

Kara sada kanta ta yi ta yi godiya kafin ta mike daga ita sai rigar bacin dake jikinta wace ta kafe a jikinta , rigar bata da shara shara sai dai kasancewar ta velour sai ta lafe a jikinta ta yi mata dass ta fitar da tsarin halitarta

Da kallo Anmy ta bita har ta shige dakinsu dan zuwa ta shirya ta fita wajen aikinta kafin take sauke wata nanauyar ajiyar zuciya
Shin da wa zata iya yin irin maganar nan wanda zai bata kyakyawar shawarar da mutane ba zasu ga ta yi son rai ba? Da wa zata zanta wanda zai dubi lamarin da duba irin na fahimta ba zai bi bayan dayan biyu ba ya bata shawarar da ta dace?
Tabas ba zata iya tauye yarinyar kai tsaye haka ba,
Waye wanda zai bata hanyar da zata bi cikin ruwan sanyi ta samu cikar burinta? (ya mama ta ce ku shige daka tana da kyakyawar shawara Anmy😆)

A yau da ta tashi sai ta yi shiga cikin wando na jins irin wanda ke dame kafar nan daga cen kasa sannan ta saka riga ruwan pink color mai dogon hannu da botira daga gaba
Da ta zo bala botiran sai ta bar daya bata bale su dukansu ba sannan ta caje gashinta da kyau ta daure shi a tsakiyar kanta

Turare ta bulbulawa jikinta kafin ta dauko wata abaya baka sidik wace sam bata da siri domin tamkar sange haka take ita dai an sakata ne dan kar a ce ba'a saka abin rufa ba ta dora abinta ta dora abin kan saman tarin gashinta mai tsayi da baki

Kusa da Ummu ta je ta rage tsayinta ta mana mata kiss a kumatunta sannan ta buda Jakarta ta ciro kudi kimanin jaka hamsin ta mika mata tana kallonta ta ce" kin rage fara'a yayar Najeeba, hakan kuma na saka ni aiki da rashin kuzari

Da murna da kuma mamakin yau ta bata kudi daga tambayarta ta dauki kudin tana kallonta ta yi yar dariya ta ce" yau nice yayar taki? Kin yarda kennan?

Najeeba ta yi daria har fararan hakoranta suka bayana ta ce" idan har zaki saki ranki, idan har zaki daina tunani kina dorawa kanki abubuwa zan yi ta kiranki aunty na rantse

Murmushi Ummukulsum ta yi tana saka kudin cikin jakarta ta mike itama ta dauko hijab dinta dogo ta saka ta ce" mu je, nima yau zan yi aikin

Ai kuwa da murna Najeeba ta kama hannunta suka fito,
Takalmi ta saka mai ruwan pink sai jakarta itama yar karama pink mai kyan gaske suka jero

Salama sukaiwa Anmy dake zaune tana neman wayar maman Najeeba ta kasa samu suka fito
A yau masu tsaron sun kasance har mutun hudu hakan ya baiwa Najeeba daria ainun
Mota biyu suka fita da ita dole, motar Najeeba da motar Ummukulsum har zuwa shago

Ta yiwa mutane kwaliya sosai, ummu na tayata hakan ya saka ta saki ranta har tana ta murmushi inda kira ya wuni shigowa a wayarta aman ta ki dauka domin Najeeba ta tare ta hanna ta ce" tabas ba zai samu lamarin da sauki ba!

Sai bayan magariba suka zauna inda suka samu indomi da kwai da kif8n gwangwani suka gwongwaje

Mikewa najeeba ta yi ta dauko masu wata gora ta dauki kofi ta cikawa ummu ta miko mata

Ummu ta amsa ta kafa kai ta shanye tass kafin ta yi yar gyatsa
Najeebama ta cika ta kwankwada sosai ta rufe ta mayar frij

Ummu ta ce" Najeeba da me da me kika hada wannan kuma ke dai akoy fitinaniya

Najeeba ta yi murmushi ta ce" baki ga hadin da maman Zahrau ta kawo mata ba? Shine na saka ta tambayeta me da meye a ciki
Ai sabuwar tatsa ce ta rakuma sabon haihuwa na hada mata karanfani mai yawa da kuma zuma sabuwar saka ke ni idan na sha dadi nake ji a zuciyata

Ummukulsum ta ce" walahi kuwa, nima ai wani sanyi na ringa ji a zuciyata sannan abin kamar yana ratsa gaban jikina

Sai da dare ya yi suka fito suka kama hanyar gida yau ba inda zata je domin sun cika dare a saloon din

Tun daga bakin kofa suka ga wani lamari, yau su da kansu sai da suka fito aka duba motarsu kafin su samu shiga ciki

Sunna shiga suka samu Anmy su take jira, sai da ta ga shigowarsu sannan hankalinta ya kwonta
Chapter 53 · 0% Book details