← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 138

Sashe 32

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Masu yi masu jagora ke amsawa da karfi karfi sunna fadin" ku shigo a hankali, Gimbiya na falo
Ku sada kanku kasa ku gaishe da mace daya tamkar da goma mama a wajen sarkin damagaram
Ku tako sannu sannu

Bakinta ta dan tabe tare da yayarta suke wace ke biye da jakadiyar dan aiwatar da abinda ake nuna masu

Sunna zuwa du suka nemi zama a kujera
Sai dai basu kai ga karasa nufinsu ba da sauri Jakadiya ta tare tana nuna masu wajen da ya dace su zauna domin idan ka ga Gimbiya na sama wani na sama toh sarki ne, sai y'ayanta dake hayewa jikinta su dora kansu a saman kafarta, su kansu idan ka ga sun layi da ita to a saman diner ne

Ko yanzu Zahrau ce kwonce kanta saman cinyarta ita kuwa tana shafa mata gashin kanta
Daga kasa kuwa Najeeba ce ke gyara mata akaifunta tana ta kankare mata su tana yanke mata duda ba wani datin dake jikinsu aman ta saba idan tana zaune ko ta dora rigimar sai ta yi mata kitso, ko ta kama gyare gyaren mata su akaifu ne da sauransu

Komawa suka yi wajen suka zauna domin wajenma waje ne mai alfarma dan ba kasa ne dabas ba aman duda haka ita ta so ta hau kan kujera dan a ganninta ai ita matar yayanta ce

Yayarta ta fara mika gaisuwa, kafin itama ta buda bakinta cike da yatsina ta ce" Fatan kun wuni lafia, yaya aka ji da hakuri?

Gimbiya ta dan dauki lokaci kafin ta lumshe idannuwanta, hakan ya sa Jakadiya fadin" Alhamdulilah, Gimbiya ta amsa Hakuri an gode Allah

Da kallo ta bi Jakadiyar sannan ta sauke kan Gimbiya
Sai ta ji shakarta ta shigeta domin irin kamalar dake tatare da fuskar gimbiya ba zaka iya takata kai tsate ba komai rashin kunyarka dan ba lalenema ka ji muryarta ba idan ba hakan ta so ba

Idannuwanta ta dago ta sauke a fuskar Zahrau wace ke iya gannin hakan

Dan mukewa Zahraun ta yi tana gyara gashin kanta ta bi kannenta da kallo baki dayansu, kallon nan da ake kallonka kuma a kalli mutun

Du yawanci sai da suka dan turo baki kafin a hankali da daidaya suka shiga gaisheta, gaisuwa kamar haka" barka da yamaci, fatan kun zo lafia?

Bakinta ta tabe tana dan jijiga yarta dake bayanta wace ke ta ihun a sauketa tun da ta ga yan uwanta aman uwar ta ki kunceta dan haka sai take kukanta irin kannanun kukan nan

Basu wani jima sosai ba, ko gaisuwar yaran ba yanda ya dace ta amsa ba yayarta dai ce ke amsawa kafin su mike su juya su fita

Sauri sauri take har suka karasa fita waje sannan suka shiga cikin motarta da suka zo da ita

Sai da ta kama hanyar gidan iyayenta dan cen suka nufa tana ta jan wani uban tsaki

Ita dai yayarta tana ta jijiga yar da ta ki yin shiru tana kiran sunnan yayanta dan saurayin

Sunna karasawa suka sauka suka shiga ciki

Mamansu dake shanya hijab din yar yarinyarta ce ta dago tana dubansu ta ce" aa, me ya samu kishiyar ne haka take wantsala kuka tun daga waje?

Yayar Mardiya ta mikawa mamansu yarinyar ta zauna tana dan tabe bakinta ta ce" mama, anya kuwa Mardiya ba tana hada mu da y'ayan mijinta da kanwar mijinta dan ta kasance mai son kanta bane?

Da sauri Mardiya ta dubeta ta ce" wani irin ina hadaku da su?

Hararanta ta yi ta ce" kwarai kin ji abinda na fada! Mardiya du irin rashin mutuncin dake tsakaninki da yaren nan sai na ga da sauki tunda har zasu budi bakinsu su gaishe ki, sannan ke maimakun ki yi masu amsa irin ta uwa ko dan idannuwan mamansu sai kike wani binsu da harara
Ke dai kece mai neman fitinar a bayane domin ni dai ba fada min aka yi ba ni na raka ki

Mardiya ta zaburowa Nusaiba tana fadin" zaki min shiru ko sai na ci uwarki a nan yarinyar nan?

Yar ta yi shiru tana kwontar da kanta saman kirjin kakarta ta kai dubanta wajen yayarta da yannayin fada ta ce" malama kar ki wani fada min haka dan ke baki san abinda nake ciki ba!
Yanzu dai a gabanki zuwa muka yi zamu hau kujera aka hanna mu aka nuna mana kasa muka zauna
Sannan kina ganni mu muka buda baki muka fara gaisheta bayan mune ya dace ta gaisar! Da kike maganar yaran ba sai da ta harari katuwar guzumar ba sannan suka gaishe mu ba?

Itama idannuwan ta ruko mata ta ce" kin fa san bana tauye gaskiya ko a gaban waye, ba zan boye gaskiya dan kina kanwata ba
Me kike so? Ki hau kujera ki layu da Gimbiyar Damagaram? Uwar sarki ce fa Mardiya baki da hankali ne? Ke ki kasance da ita a waje dayama ai arzikin arziki kika ci! Kuma maganar kujera ba a kasa aka sauke mu ba, na lura wajen saukewar an dora mu mafi karamci ne a cikin waje uku ne
Da kike maganar sai da ta harari yara sannan suka gaishe ki inaga ashema da tarbiyarsu yaran dan har an isa a sakasu ko a hanna su duda kuna cikin haki na gaba da tsanar junna?
Ke ki rufawa kanki asiri ke kin san cewa Allah ya baki dama, na rantse da Allah da ace kin sada kanki da matar nan da na tabata kun samu kusanci da fahimtar junna yanda ya dace, da ke ya dace a je a yiwa gaisuwar nan ba wai na tirsasaki na kaiki mu yi dan zama mu tashi ba
Haba Mardiya, ke kin san waye mijinki, igiyar aure daya ta tsinke tsakaninku, ke kin san kafin ki shiga gidansa da manufarki ta yin hakan, kin shiga gidansa ne dan ki rama kwace maki saurayi da y'arsa ta yi, kin shiga ne dan ki muzanta rayuwarta ki hanna mata zaman lafia da kwonciyar hankali
Baki shiga dan ki haihu ba
Baki shiga dan ki jima da shi ba,
Da biye biyen abokansa suka shunna masa ke ya aura
Ke kin san kina cin ribar baba malan ne
Ki kiyaye Mardiya, ki kiyaye dan wannan kadai ya isa ya shaida maki cewar Allab na tare da shi, kwarai kina haye masa da izgili kala kala aman Allah ya hanna rabuwarku, ke kanki nan da ya sake ki saki daya a nan kika ringa zuba mana hauka sai da muka neme shi aka mayar da ke
Kin je kin saba da rayuwar gidansa idan kika ce zaki balo ki fito kece da shan wahala
Ki duba ki ga jikina, kwoncen kayan da kika bani ne aman ni kaina na zama abar kwatance a cikin sa'a dan kina bani su ina ketawa ina shiga cikin jama'a har fadi ake kanwarta ce ke auren MUTALAB fa, me kika rasa a gidanki? Mijinki ba ke ba ko mu idan ya tashi tsokanarsa zai sako mu gaba ne sai an sha wasa da daria,
Kudi sai dai ki ba wani
A wajen kwonciya ya gaza maki ko a me? Mardiya idanma muzgunawar ne fa kin masu , ya dace ki gane cewar kece da faduwa idan kika ci gaba da rayuwa a haka domin ko a irin yanda kansu ke hade zaki gane mai shiga tsakaninsu fa walahi ba dai mutun ba sai dai Allah!

Mardiya ta zauna tana hucin maganar yayarya bayan baki daya gaskiya ta fada mata

Sai a lokacin mamansu ta kawo kujerar zama irin tayani tsegumin nan ta zauna tana kallonta ta ce" ke kuwa, rashin wayo ne ko rashin hankali ke saka ki aikata abubuwan nan?
Jiya yayarki ke ce min wai kin yiea yaren iyaka da taba Yarinyar nan
Ashe baki da hankali? Ke din kin isheta tuwo da miya ne? Ke yau ace mijinki na raye har ta kai aure yaran nan suka fita a harkarku yaya zaki ji? Ko macen nan ta isa ta yiea yarki kayan daki idan kina da hankali ai y'ayan miji abin so ne abin a jawo a jiki ne domin baka san waye wane ba, koda baka kwadayin lada ai kana kwadayin duniyar tunda ita ta rufe maki ido har kike tafka iskancin nan
Mardiya zan fada maki, ba zan kuma barin yarana shiga fadanki na iskanci ba
Da ace kece da gaskiya kin san wacece ni ko ni ba zan yarda a wulakanta min ke ba, aman na lura dadi ne ya maki yawa kike ihun Allah ya kasheki ki huta
Bana son ki yi nadamar haka,
Aman kuma dahuwar mutun mai kosai

Ita dai sauraronsu kawai take, ita ita ta san me take ganni da yaren nan
Yaren dake tunanin ita tsararsu ce? Yaren dake kiran sunnanta kai tsaye?

Muryar yayarta dake idasa shanyar mamansu ta ji da haushi haushi tana fadin" wai wani ita ya dace ta gaishe mu, matar da idan haihuwa ne ta haife ki dan kawai kina auren yayanta kuma tana matsayin shugabar garinkima sai kawai ta wani gaishe ki? Ai da na rainata kennan, ke da ko bakinta ta buda ta ringa mana zuba ni sai na raina mata wayau!

..........................................

Tsuru ne ta yi sanye da hijab baki har kasa mai hannu ta saka Anmy a gaba tamkar ta fashe da kuka tana kallonta

Muryarta na rawa ta ce" Anmy mana, dan Allah a bar tafiar nan na yafe

Anmy ta juyo da mamaki tana kallonta ta ce" NAJEEBA, a kan me za'a bar tafia gannin likita bayan zuciyarki na maki suka? Mai martaba zai yi fitar boye dan dole sai ya ga wani bincike a tsaye a gaban idannuwansa dan bai yarda da kowa ba, gashi kuma clinik din daya ne zaku je shikenan da daren nan sai na barki ki tafi ke daya ko a fasa? Ki fita a idona na rufe ba za'a fasa ba kuma tare zaku je kima dauko alkyabarki dan kin san ba zaki bi shi haka daga ke sai hijab ba ko?
Chapter 32 · 0% Book details