← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 138

Sashe 114

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kanta kawai ta sada bata iya baiwa mahaifiyarta amsa ba, a haka UMMU ta saki hannunta ta bi bayan AMMI

Ta jima nan tsaye tana saka tana kwoncewa,
Tana ta nazari ne a kan rayuwarta ita kanta, kafin ta daga kafarta da kyar ta shiga takawa ta nufi dakin da a ranar ta ga ya fito da Nadia daga ciki

A hankali ta idasa saka kafafuwanta tana bin dakin da kallo, ba sanyi domin Ac a kashe, sai dai da kamshin sansanyan turatan wuta

A haniali ta taka ta nufi bayi du kuwa da irin yanda take jin jikinta ba karfi kwata kwata

Ruwa ta tara masu zafi ta rintse idannuwanta a hankali ta fara saka kafafuwanta sannan ta rintse ido ta zauna wanda hakan sai da tmya sakata kama abin nan ta rike da karfin gaske

Idannuwanta rintse suke kakam, abubuwan rayuwa take ta tunawa, yau gata a gidan da ba saki sai ka aikata kisa ko zina, biyu daga cikin abubuwan da rana bata fitowa ta fada bata nemi da Allah ya tsareta daga mumunar kadarar da zata kaita aikatasu ba
Yau gata a matsayin matar aure, matar farin mutun,
Sai dai abinda ya ki barin kwakwaluwarta shine irin yanda yake son ya jata da dan wasa duda ba wai wani sakewa ya yi ba aman yannayin da yake nuna na kamar zai tsokaneta na bata matukar mamaki

Kafarta ta riga dan wanawa a cikin ruwan tana kara hauda shi jikinta a hankali ya ringa salabcewa har zafinsa ya ragu sosai

Wannan karron sai ta hada na sabulu mai kunfa sosai mai sansanyan kanshin da ya sakata lumshe idannuwanta,

Ta jima a cikin ruwan nan har sai da ta ji kiraye kirayen sallah sannan ta dauro alwallah ta fito daga bayin da tawul din da ta gani

Tsaye ta yi a dakin daga ita sai tawul, tunaninta kayan da zata saka

A hankali ta fara leko kanta dan so take ta je wajen wayar cen dake ajiye ta yi kira bangarwn AMMI a kawo mata kayanta, sai dai tana lekowar sai ta hangi akwatinta wace take malakinta

Da dan sauri ta fito ta kama tana janta har ta shige dakin sannan ta datse tana sauke ajiyar zuciya

Bata buda akwatin ba sai da ta je wajen turarukan dake ajiye

Ido ta buda sosai gannin turaran nan, sai kuma ta turo baki tana dan gunguni ta dauki guda ta buda ta shiga yiwa jikinta barinsa sosai har kai tana ta kara juyawa da daria a fili ta ce" Na rama cicije min nan da ka yi malan ehe"

Sai da ta gama barnar da gangan dinta sannan ta koma wajen akwatin ta shiga bubudawa
Wata doguwar riga mai hade da hijab dinta har kasa ta ciro wace ta tabata an saka mata ita ne dan sallar

Pant da bras ta ciro sababi ta ajiye
Sai da ta fesa masu tyraran nan son ranta sannan ta saka ta zira rigar ta shiga neman abin sallah
Sai dai sama ko kasa babu, tana nan tana ta zagaye kamar da wasa ta tsinkayonkiran salar isha'i, hakan ya sakata zaro idannuwanta da sauri ta fito ko kashe fitilar da ta kunna bata yi ba tana son yin saurin sosai aman har yanzu ba wai ta saku yanda ya dace bane, ta dai rage jin azabar da take ji dazun aman kuma har yanzun wajen na sukanta

Ba tare da tunanin komai ba ta tura dakin nasa da salama kasa kasa ta shiga

Tsayuwa ta yi tana kallon dakin, ba kowa ciki aman da kanshin turarrn wuta da ya garwaye da turaran daki da kuma na jikinsa da ya fesa sai abin ya bada kamshin ya hade ya cika ko'ina na fakin
Ga sansanyan sanyi dake dakin na AC din da bai kashe ba

Dan tabe bakinta ta yi ta nufi kebantacen wajen da ake sallah a dakin

Wajen a kawace yake, ga alkur'anai mai girma a saman wani dan sif fari kal a jefe da litatafan musulunci da carbunna dai masha Allah

Sallah ta kabarta a hankali ta shiga gabatarwa, tun daga Azahar da bata samu damar yi ba, la'asar da bata yi ba, magariba, sannan ta dora da isha'i

Tana salamewa ta ji muryarsa kasa kasa ya ce" du kina me kika tara sallah haka a kanki NAJEEBA? "

sai da gabanta ya fadi, domin ita dai sam bata ji shigiwarsa ba bale takun tafiarsa, uwa uba kanshin turaran nasa dake shaida mata zuwansa waje itama shi din ne ta kilkila a jikinta ya kasance har hancin nata ya daina jiyo kamshin zabar ya shaka da yawa
Sai da ta dauke numfashi kadan sannan ta dan sada kanta da carbin da ta dauka fari mai kyau a hankali ta ce" Nafiloli na yi "

Dan murmushi ne ya kwace masa a kan labansa, bai ce komai ba ya koma ya gyara zamansa saman gadon ya jinginar da bayansa a jikin kan gadon kadan sannan ya ci gaba da binta da kallo kasa kasa yana mai jan carbin dake hannunsa

Du sai ta kasa jan lokaci mai tsayi tana jan carbinta, tana ganawa ta daga hannunta a cikin zuciyarta ta yi adu'o'inta ta shafa sannan ta ajiye carbin ta mike ta dan ninka salayar ta bi wajen kur'anan nan da kallon sha'awa tana ji a zuciyarta inama ace nata ne duka? Kai da ta caba

Dan satar kallonsa ta yi, sai ta ga ashe ya yi baci, dan haka dan ta yi murmushi ta juya a hankali da niyar tafiarta wancen dakin ta kwonta

Kasa kasa ta ji ya furta " Baki ji ba? "

Har sai da ta dan tsaya ta juyo ta kale shi, gannin bai motsa a yanda ta barshi ba sai kawai ta juya ta ci gaba da tafiarta a hankali

Idannuwansa ya dan buda kadan ya ce" Najeeba idan kika fita ba zatai maki dadi ba "

Juyowa ta yi tana turo bakinta gaba tana dan magana kasa kasa , cewar haka kawai ashema ka san sunana malan

Shi dai kallon bakin nata kawai yake a yanda yake, sai kuma yanda ta tsaya masa wani kerere a tsaye a ka da yake mamaki

Dan buda idannuwan nasa ya yi ya sauke duban nasa a fuskarta, irin yanda ta turo bakinta da tsayuwar da ta masa kamar wata yar baby sai mutsu mutsu take da bakinta

Hannunsa na dama ya mika mata a hankali ya ce " Zo "

Sai da ta bi hannun da kallo , a ranta fadi take, kawai mutun sai fari uwa wani aljanni, irinsu ne kana ta kanka a gida kana faman girki da tsantsara masu kwaliya sun fita waje wasu matan na wawarsu, haka kawai kana ta kanka a jaza maka abinda ba shi ba, sai wani yanga da wani langwui salon ka kara tara matan, to dai matsalarka ce malan idan kana so tara million ma

A hankali ta dora hannunta saman nasa , tana kara shagwabe fuskar tata ita bata ki zuwa ba, ita bata yarda zata je har zuciyarta ba

A hankali ya janyota gaba dayanta jikinsa ya dorata saman jikinsa ya saka hannayen nasa ya bata kyakyawar runguma
Muryarsa sanyaye ya ce" yaya zaki gudu ki barni bayan kin ga matata ma cikin wani hali, nima ina cikin damuwar saka mai so na a wani hali? Duda na san ba so na kike ba aman idan kika zauna da ni zan rage zafi "

Bakinta dake daidai wuyansa ta turo sosai tana tabewa, a hankali ta ce" to ka yafe mata mana, ai na ga ba ita ta kashe maka mata ba, kuma ba ita ta so kashe maka mata ba, bayan wannan ai dan tana son ka ta aiwatar da hakan, kishinka take shi ya sa "

Idannuwansa dake lumshe ya dan kara lumshewa sakamakon abu biyu, gannin kamar maganarsa batai mata zafi ba, da irin hucin dake saukar masa a dokin wuyansa

Sai da ya jima tamkar ba zai yi magana ba sannan ya ce" zan duba maganarki, kafin na yafe mata zan kara aure "

A hankali take jin haushin magangannunsa, to a me wai ya dauketa ne? Ita ga wawa ko? Da dan zafi zafi ta ce " idan ka tashi ka auro farare tas tas tas bakakenma ka sake su SHAHEED "

Murmushi bayanane ya yi gannin a yanzun maganarsa kamar ta mata ciwo, dan haka ya ce" sai nake gani kamar kin ji haushi? "

Bakinta ta yatsina tana dan son tashi aman sai ya kara matseta a jikinsa hakan ya sa ta daina kiciniyar son tashin
Itama sai da ta jima tana tunani sannan ta ce" ba biya ba bege me ya kawo jin haushin maganar abokin zama ?"

"Haka ne kuma, aman ko ba komai zan duba shawararki zan kawo wata tsaleliyar fara, sai dai ni bana ajiye bayi a matsayin matan da zan ringa zagayawa, kema musulunci ai ya yi karfi yanzun ko " Shaheed ya fada yana mai kara rungumeta a jikinsa

Sai da ta datse lebenta na kasa a dan kausashe ta ce" sake ni! "

Kansa kawai ya dan girgiza mata bai sake tan ba bai kuma bata amsa ba

Huci ta furzar kafin ta ce " Allahn da ya sa nima ba ni nace ina son farin ba! "

Murmushi ya yi a bayane bai bata amsa ba, sai kawai ta ringa sauke ajiyar zuciya, sai da ta dan daga dubanta ta sauke a kan habarsa , gannin idannuwansa a rufe sai ta zabga masa harara harda murguda bakinta

Dan murmushi ya yi a hankali ya ce" Na yafe maki "

Ido ta zaro da mamakinsa, wani irin karfin gani ne da shi haka?, wai kuma me yasa ya cika son yi mata komai cikin sanyin lamari bayan shi din mutun ne mai zafi?

A hankali ya ce "BEEBAHHH?"

dagowa ta yi da sauri dan jin muryarsa a wani irin sanyaye sannan irin yanda ya ja sunnan sai ta ji da bambanci sosai kan yanda UMMU ta fada, nasa har wani irin yamyamyam ya sakata ji a jikinta, sam sai ta kasa amsawa kiransa sai wani zuru da ta yi tana kallon wuyansa domin daf take da wuyan nasa numfashinta na sauka a wuyan nasa
Chapter 114 · 0% Book details