← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 138

Sashe 89

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abih ya dan yi mata murmushi mai ciwo a hankali ya furta" haba *SIRRINA*, baki san sun san wani *Sirrin* rayuwata mai tsanani kuma suka hakura suka ci gaba da mutuntani ba? Yaya kike so ki ci gaba da fuskantar irin wannan shariya da abubuwan da y'arki kwalin kwal ke maki a kan namijin da ya kuntata maki? Kina da bukatar samun girmamawa, soyaya, kallon daraja daga wajenta, tabas kina samu daga wajen yan uwanta aman ita din ke kika haifeta fa? Dan Allah ya isa haka, ki barni na fada"

Har bakinta rawa yake ta furta" aa, ba ruwanka da abinda ke damuna, ni ban rokeka fadin wannan abin ba, ina fadawa Allah idan lokacin ta dubeni ya yi zata dubeni dan kanta"

Murmushi ya yi yana dubgure kanta ya karasa da sauri ya zauna gaban y'ayam nasa ya ce" ba ga irinta ba, ci gaba zata yi da boyewar, tana kakare laifina, ita dai a haka take so ta kare?"

Najeeba, na auri mata goma sha bakwai a rayuwata
Cikinsu ba wace ban haihu da ita ba, kuma ba wace ta ga girman y'arta take fecewa
Na birne mace uku a gidana wa'inda suka rasu a hannuna, sauran goma sha ukun nan du rabuwa muka yi, banda mardiya ta sha hudu
Najeeba, kamar yanda kuka sani, wasun dalilin na tarda su sunna dukanku ne, wasun rana tsaka zaku tubure da rigimar bakwa son su, wasun zasu nunan ba zasu iya rike y'aya birjik haka kawai bane, wasun zalamarsu ta saka, wasun kuwa sun aikata abinda ya hana min yafe masu ne ya saka ni rabuwa da su aman banda *NANA MARIAMA*

Sai da ya kalli UMMU dake kallonsa da mamakin wai da gaske bayanin zai yi ya yi murmushi ya ce" aminiyar BILKISSU ce, wato Ammi dinku, ita ta yi mata gorancen aurenta, sun kasance masu raba ayya daya, sunna rike sirrin junnansu duda BILKISSU ta bata shekara UKU a haife wanda hakan ya saka idan ta yi niyar tsokanarta ko idan tana cikin yannayi na tashin hankali takan kirayeta AUNTY domin takan ce da ita "Bani da kowa sai Allah sai ke"

Min sasanta kanmu da NANA MARIAMA a lokacin da nake amsa sunnan Yaro da kudi, ina jin wani irin tashen kudi dake daukana yana yawo da ni yana dadani da kasa

Na tara y'ayan sai dai ba wai takamaiman su din ne a gabana ba, ina dai da wani irin kaunarsu a zuciyata wada ke sakawa idan aka yi katari na dan zauna na ji damuwarsu to fa ko wace iri ce zan dage na magance masu banda zama da su da kukawa da tarbiyarsu da kuma gane irin ilar sakin iyayensu da shigowar bakin fuska a matsayin sababin iyayensu ke janyo min
Sai da na auri NANA MARIAMA na fara gane meye ma'anar zuri'a,
Tanadinta zuri'arta, burinta zuri'arta, farin cikinta zuri'arta, abokannanta zuri'arta a lokacin ta shigo ta tarda mahaifiyar Ummukulsum da tsohon cikin Ummukulsum

Zamansu bai yi nisa ba na sawake mata a lokacin da ta haifi yar jaririyarta sakamakon gannin itama ta haihu yanzun zata fara ware nata daban sauran daban wanda na kamata da hakan sau uku karshe dai na sawake mata na ci gaba da koyon rayuwa a wajen NANA Mariama

Fadace fadace, rashin zaman lafia, rigingimu na tsakanin miji da mata kan hada mu, sai dai wani ikon Allah daga lokacin da zan tabo ku zata zube a kasa gwuiwoyinta a kasa tana kuka ta ce" ka yiwa Allah ka yiwa Annabi muhamadu salalahu alaihi wa salam ka barni na huta, ka barmin yara su huta, kai baka gannin yarintarsu, soyayarsu, karfin zuciyarsu? Kar ka hargitsa min tarbiyarsu ko ka birkita min zaman lafiyarsu, yaren nan sune farin cikina, kai ka san ba dukiyarka ko kyanka ya saka nake hakurin zama da kai ba sai dan yaren nan"
Abinku da wanda shedan ya rigaya ya buga min ganga sai na sheke da daria sai na kalleta a kaikaice na ce" ku ji shishigi malan, yara ina ruwanki da su? Su tashi a tashama mana na san tarbiya ta Allah ce ba ta wani ba, dan haka idan kin gaji da zama da ni ki kama gabanki!"

Zata kawar da kanta, ra mike ta tatara ku ta yi vangarenku da ku, ta hanna yan aiki zuwa inda kuke da cikinta a jikinta ta yi ta kulawa da ku, har sai na kasa jurewa dan kaina na dawo na lalabata domin du abuna nakan kasa nutsuwa idan muka yi fadan da ta min fushi har ta kaurace min, zaku ga na dawo ina lalabata mu shirya"

Dan murmushi ya yi ya ce" har zuwa lokacinda yar uwarta wace ta kasance yar mahaifinta ce ta bayanna,
Wannan itace rayuwar da na yi mafi muni a cikin rayuwar da giyar kudi ta kaini ta baro ni"

Kallonsu ya yi da kyau ya ce" a lokacin bata fi wata hudu da cikin Najeeba a jikinta ba, murna farin ciki haka take bugawa mutane tana fada masu ashe tana da yar uwa? Kuma itama yar uwar nata da danginta bangaren mahaifiyarta, wato dai ta samu dangi

Sosai ake shige da fice ana tayata murna, harta da dangin na yar uwar tata sun zo sun taya murna, inda yar uwar tata ta tare a gidanmu suke zaune kalau

A hankali yau da gobe, kadara da haduwa da wata irina wace ta sako duniya a gaba muka shiga fandarew, munna watsewa, munna aikata alfasha a boye a cikin gidanta na aure cikin du dakin da hakan ta kama"

Subahannalah, Ummu ta fada da karfi ta ce" wai wa ya tambayeka?"

Hararanta ya yi ya ce" ko dai bakin ciki kike na huta da nauyin dake kaina ne?"

Ci gaba ya yi da fadin" tun bata sani ba, har Allah ya sanar da ita,
Ta ci kuka, ta yi dana sanni harma ta so bara min gidan sai dai a lokacin da DAYABU ya riki kafarta yana ihun UMMU UMMU, sai kawai ta fashe da kuka ta rungume shi ta bara mana wajen wato gamu ga duniyar"

Kunya ta hanna min zama sai na bara masu gidan na tsayin sati, ashe aikin gama ya gama har ta dauki ciki na tsayin wata uku, UMMU kuwa na dauke da nata wata bakwai

Dole na waiwayo iyalaina, dole na waiwayo matata da y'ayana,
Sai dai kash bayanuwar cikin ya kara hadasa mata tashin hankali

Na takaice maku, ni da kaina sannu a hankali na ringa haifar da dalilan da suka ringa kara nisanta ni da matata ta rufin asiri wace du abubuwan nan da nake mata ko kanwata daya kwal wace ta ragen a duniya kuma aminiyarta bata sanarwa ba, sai dai ta rufe daki ta ci kuka ta fito a yi abinda za'a yi

Akoy ranar da ta tasheni tsakiyar dare ta ce da ni" MUTALAB, na aureka ne domin Allah, ina zaune da kai dan Allah ya saka min kaunar y'ayanka, Mutalab a da ina tunanin ina iya hadiye komai dan yarenka, aman a yanzu na gane harta NAJEEBA dake da shekara uku ina iya bara maka na tafiata idan har baka bar rayuwar nan da kake ba, idan har baka takawa zuwan uwar yarinyar nan da take takenta birki ba zan wanke kafa na je na daki mamanta na daketa na yi kason haka, MUTALAB idan ka kai zuciyata makura zan halaka ka na halaka kaina, dan walahi walahi irin yanda nake maka magiyar ka aureta idan sonta kake ka nuna min yaya zaka kuma iya auro bara gurbi a cikin gidanka to fa ka kiyayi du wata mu'amala da ita, idan ba haka ba MUTALAB zan halakamu baki daya mu shiga uku, na roke ka ka sawake min na yi tafiata"

Sai kawai na fi ta hawa dokin zuciya, na rufe na ringa shiga ina fita ina fadin" Mariama, kin jima baki halakani ba, ki gwada idan kina yiwa Allah ki gani! Ni zaki nunawa zuciya? Kin san ni gaba da baya ko waye, kuma idan takamarki kina da kudi kin san na dame ki na shanye, ki zubar min da y'ayan mana, sai na auro wata ta zo ta kularmin ai kin san ba ke na fara aure ba, kai ni banma yarda da rashin aurena har yanzu ba, na tabata kin asirceni ne malama"

To fa ranta ya bace, muka ringa sakawa muna fidawa wannan karron har gaban sarki da kuma BILKISSU,
Ko a nan kin fadin dalilin fadanmu ta yi, Sarki na mata nasiha sai da aka tambayi musababi ba kunya na fadi dalilin kai tsaye wanda ban taba jin kunyar abinda nake aikatawar ba sai da ya ringa yi min nasiha yana tino min rayuwa da mutuwa, a lokacin na furta walahi walahi walahi sau daya tak ne, yarinyar ce ta cika neman fitina har take nuna kamar wani dinkewa muka yi da ita,

Sai da aka shirya mu da *SIRRINA* kafin muka dawo gida

Shekara kamar uku tsakani kamar komai ya wuce, ba wai yan mata na daina yi ba, ba kuma take taken masu kudin zamani na daina ba kaina sama da isata da komai gefena ga hajiata tana kawar da kai ga jiginiyar y'ayana da suke dauke da wata irin tarbiya ta shakuwa da junna da soyayar junnansu bale DAYABU da ya kasance ya iya tafiar da tarbiyarsu daidai gwargwadon iyawarsa,
Wata ranar asabar, wace ta kasance ranar da ta kai bango, ina katon shagona na buga madara suka kawo mata ziyara da yar da aka haifa min da siyaya rigijib dan neman fitina

A lokacin tana da saurin rama mari, dan haka a gabansu ta masu dan karamin hauka, ta nuna masu halaya na mata, suka ringa raba haki har hayaniyar ta kawo inda nake

Kafin na mike sai da wani abokina elhaji Saley ya ce" lale kura ta yi lafia, yo ni mace ta isa ta ringa yi min abinda matar ELHAJ MUTALAB ke yi masa ban lakada mata duka ba na nuna mata ita ke kasa da ni na koya mata hankali ko dan gaba ba?
Chapter 89 · 0% Book details