← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 138

Sashe 108

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsayuwa ya yi kasan shower ya sada kansa
Lebensa ya yi masa jajajir sai dan rawa yake masa sanadiyar irin halin da yake ciki
Hannunsa na dama ne ya jimke ya kai duka jikin garun nan yana kara taune leben nasa dan so yake ruwan nan mai sanyi dake zubar masa ya bashi yar nutsuwa ko yayane

" *ALLAH NE YA TSARE MIN ITA* " ya furta a hankali muryarsa a cinkushe,

" *ya Allah ka kara tsare min ita* " ya idasa fada a saman labansa

Baki daya mararsa ce ta kama ciwo, cikinsa ya aniya kulewa waje guda ya kasa kwakwaran motsi

Bai saba da irin wannan matsalar har haka ba, idan ba dan ita ba ba zai taba sannin wannan maysalar ba, dan jarabar idannuwansa du ranar da ya ganta sai ya kurewa kallonta, haka zai zo ya yi ta fama

Ajiyar zuciyar da ya ringa saukewa ce ta fahimtar da shi idan fa ya yi da wasa yana iya kwonciya rashin lafia

Rausar zuciyarsa ya yi ta yi kan tinasar da shi abinda yake yawan fadawa kansa dan ya rarashi kansa koda a xen baya

Sai da ya tabatar da ya rage bacin ran sannan ya juya a hankali ya fito mata hakansa

Bata ga fitowarsa ba, bata san da ya nufota ba, sai ji da ta yi an kuma fara taba mata jikinta
Sai dai a wannan karron a sanyaye ake taba mata jikin, ga sanyin ruwan dake haduwa da fatar jikinta, ga ji da take kamar za'a cinyeta ya sakata kasa buda idannuwanta sai barkewa da ta yi da wani sangartacen kuka

Hancinsa yake ta kai kawo a wajen jigidar nan mai sansanyan kanshin sirri

Kasancewar a yanzu yana mai binta a hankali, yana kokarin gannin ya baiwa komai hakinsa duda kasantuwarsa a yannayi na bacin rai da mugun bukatuwa da ita aman sai ya ringa bin du wajen da ya yiwa muguwar damka a hankali yana mai hura wajen da lalabashi

Tsoronta, da zafin da guraren ke mata ya hanna mata karbar sakonsa yanda ya dace, duda haka nan da nan lamari ya kwace a jikinta domin kuwa a shirye yake da karbar sakon ko yayane

Lokaci daya komai ya kwonkwonce masa, lema lemar da ya ringa ji ya saka shi kai dubansa, a fili ya furta" *Wayo ALLAHNA*, a hankali yannayinsa na son ya bita a sanyaye ya yi masa kaura wanda shi kansa bai san hakan ya bar kwakwaluwarsa da aikinsa ba, a yauma ya zo mata, zuwan da ya kusan sumar da su baki daya, ita kam ta gama sarewa duniya da abinda ke cikinta, ta yi dana sannin karbar abubuwan da auty Zahrau ke dudura mata , sannan ta yi dana sannin guje masa na kwanaki hudu domin kuwa a kalaman dake dan kwace masa idan ya juya kai ya kuma juyar da kansa zai ce" Me ya sa kikai nesa da ni har tsayin lokaci?"
Wasa wasa cikinta ba komai, ta karbi kari mai sanya juwa idan ba'a karya ba, ta amshi bulaliyar da ta gwamace duka da ita, ta amshi wani irin horon da ta gama sakawa zuciyarta ba zata anfanu ba daga nan, ta kasa mugayen kalaman da ta yi a wancen ranar domin maganar da ta fi yi shine neman ya barta kar ya tsagata gida biyu, ya barta kar ta mutu, ya sasauta mata ba zata iya ba

Har sai da ya kasance ya yi niya dan kansa sannan ya saki kansa ya samu nutsuwa

Wata irin murya cen kasa mai nuni da mai dauke da ita na tsikin matsanancin hali Najeeba ta ja numfashinta da karshi sannan a wahalce ta ce" da ka halakani gwara ka sawake min SHAHEED, aikinka na nuni da burinka ka kasarani bayan nima BA SON KA NAKE BA"

Shi kam bai iya bata amsa ba, hasalima gefe ya koma bayan ya yi irin kwonciyar da aka koyar dan gudun komawar lamari jikinsu, sai ya samu kansa da tsurawa fuskarta ido, kallonta kawai yake yana jin tsigar jikinsa na kuma tashi, baki daya lamura na son kara bijiro masa...............

Farin ciki ne madaukaki ya dira a zuciyar ABIH a lokacin da ya ji wannan sako na UMMU, gashi dai a zaune so yake ya zabura ya je ya ganta ido da ido ta shaida masa da bakinsa aman ya kasa domin yaransa sun zagaye shi sai neman afuwar fadan da suka yi suke

Da wani murmushi ya shafi gefen kumatunsu ya ce" kun ga, ku je dakunnanku kun ji? Yanda ta yi da mu maman naku nima idan harda ni a hukuncin ba laifi zan karba ne"

AMMI dai daria kawai take sosai, dan Walahi irin yanda yayan nata ya yin ne ya bata daria, sai kawai take hango da cen,

Kiran da Zahrau ta yi a wayar AMMI ta shaida mata ta isa ne tana falonta yanzu haka ya sakata sakin murmushi tana fatan alkhairi sannan ta shaida mata kayanta zasu zo Agadez gobe in sha Allah za'a kai a auna mata su a tura su

Shi dai Abih kara buda idannuwansa kawai yake dan gannin UMMU wace da gangan ta yi zamanta a daki ta rufe tun da ta ji ya cewa AMMI gashi nan zuwa

......................
"Haba Nadia, yaya kike son ki saka ni asarar kudina, ki saka ni asarar likacina da tunanina ta hanyar mayar da kanki wawa kamar ba ke ba? Na ji na sanni mijin Najeeba kika aura wanda yake mijinki kema a yanzun sai me? Ina ce aure kika ce, kuma auren nan ba wai kin san za'a yi shi bane kika yarda, kuma ba tashi kika yi kika je kika auri mijin kawarki ba dan cin amana aman shine sai ki ringa irin abinnan kamar wata sokuwa? Me kike so yanzun? Da kike baya baya bakya anfani da koyarwar da akai maki dan mijinki ya san da ke so kike ki zama ta karshe a cikin matayensa? Kin san dai ba saki idan har ba kama ki aka yi da laifin zuna ko kisan kai ba, a kan me zaki ringa irin wannan abin?" Mahaifiyar Nadia ta karasa mata magana ta waya tana yi kamar ta shiga cikin wayar ta ganta gata ga ita

Nadia dake cikin hali na tsoro, tun dazu da safe ta budi muryarta dake rawa rawa ta ce" Mama, ba wannan ne damuwata ba, ina tsoron a je na kawo kaina gidan halaka domin kuwa a dazu da safe na ga abinda bai dace a ce na gani ba, baban tashin hankalina zan je na samu sarki da maganar ne ko zan yi shiru ne? Wanda na gannin ya ganni ne? Idan ya ganni me zai min? Mama na shiga uku na lalace ana neman rayuwar sarkina ido rufe na je bangarensa na yi na yi wajen ya ki buduwa ban san dalili ba, ina tsoron wani abin ya same shi ko ni ya sameni, una tsoron ace wanda na kama shima ya kama ni? Magangannun da na ji dole sarkina ya sani ya kuma ji daga inda na ji su

Hankalin mahaifiyarta ne ta ji ya tashi, dan kuwa a muryar yar tata kana iya gannin tsantsan tsoro da tashin hankali da kaka naka yi, da sauri ta mike tsaye tana kallon agogo ta ce"

Kuka ce na baku shi a haka ko? To gashi☹️ ni dai oh sunna sai ya kare a bakin maman abdul,
[3/31, 11:30 PM] BAK'A CE: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

55

Baki daya a rikice mahaifiyarta ta ce" kina ji na? Kar ki kashe wayarki, ki barta a haka Nadia gani nan zuwa"

Nadia ta ce a sanyaye" mama, idan kin zo zaki samu shigowa ne? Ina tsoron ki rasa hanyar bi idan har magautan Sultan sun san da na san abinda ke faruwa, mama ina jin tsoro sosai"

Ai kuwa hakan ya sa ta kara rikita mamanta, da gudu gudu ta fito da kys din motarta da wata wayar tana kiran number mijinta haka kuma dayar wayar bata kashe lasge ba, sannan sai maimaitawa Nadia take cewar kar ta kashe kar ta kashe

Kira kan kira a irin wannan yamaci aman ta kasa samun mijinta, hakan ya sa ta nufi ma'aikatarsa duda bata da tabacin samunsa

Sha'ani da waya, a lokacin da ta kusa karasawa kampanin wayar suka shiga shaida mata kudinta sun kare bai fi yan second a yanke layin ba, hakan kuma ya yi daidai da lokacin da Nadia ta zabura hankali tashe ta shiga furta" innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, muryarta sama sama, wanda hakan ya saka mahaifiyarta maimakun ta take birki kusan office din mijinta sai ta take accelerator motar ta je ta daki abin dake kafe da sunnan mijinta goshinta ya daki sitoyarin motar ta koma ta kuma dakar kujerar
Goshinta ne ya fashe a lokacin ne kuma mutane du suka taso a guje ana ta fadin Subahannalah, ciki kuwa harda mijinta baban juju datijon da ya rike datijantakarsa

Gabansa ne ya fadi gannin motar matarsa, uwa uba kafarta da ta fitar waje tana son karasa fitowa
hankali tashe ya nufeta yana matsa mutanen dake son taimaka mata ta fito
A rude yake tambayarta lafia, bata ji ciwo ba, me je faruwa ta fito haka daga ita sai dan kwali da doguwar rigar shan iska?

A rikicen itama ta kama hannunsa, ido rufe fadi take" Nadia, Nadia, Nadia ce sun kashe min ita, Nadiata ta mutu, shikenan sun kashe min ita, dama tun da aka ce min auren gidan nan ba na Nadiata bane na nuna ta hakura, aman tsabar son sarauta da sarkin nan ya saka ta nuna ta ji ta gani, shikenan sun kashe ta"

Gannin kamar bata cikin hayacinta ya saka mijinta kama damatsunnan hannayenta da hannayensa bibiyu ya shiga jijigata ya ce" ke Hawau ki nutsu, me kike son fada min haka? Waye ya kashe Nadiar?"

Wani irin kuka take, ta shiga labarta masa abinda Nadia ta fada sannan tana ta nuna hanyar da ya dace a bi dan zuwa gidan Sarki, fadi take" sun kashe min ita "
Chapter 108 · 0% Book details