Sashe 44
Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kansa ya sada kafin ya dago yana dubansu
Sun yi masa wani irin kyau mai birgewa sannan sun yi masa girman da sai yau ya yarda y'ayan nasa masha Allah sun fa girma
Su dukansu sunna cikin wani danyen lesh ne, wanda ya tabata da kudinsa zai tambaya sai ya kalli Anmynsu a firgice hakan ya saka shi kin tambayar kudin domin abinda ya saka ya gansu da shi ya tabata ya kece kudin shada!
Tun daga yan kunnayensu kuwa har zuwa sarkar wuyansu zinari ne da abin hannayensu, ta zahrau ce kawai ta banbanta ta kasance baba sosai da wani irin kira mai ban tsoro domin ba karama bace a girma da tsayi da fadi da kuma kyan fasali
Alkyabobin dake jikinsu kadai abin kallo ne, ta Najeeba ce ta kasance shara shara mai shegen kyau
A hankali ya ce" ban san da wace kalma zan yi anfani dan nuna maku irin tsananin farin cikin da nake ciki gannin Allah ya fitarwa da daya cikin miji nagartace mai daraja a doron kasa a lokacin da na fara shiga rudanin anya irin rikon da na yiwa iyayenku Allah ba zai jarabceni ta fannin zamanku a gabana haka ba?, sai na ringa kai kukana wajensa ina fada masa cewar kar ya kunyatamin ku, kar ya jarabeku da laifukana, ya dora min jarabawar a kaina komai girmanta ya sanyaya maku domin ku din baku ji ba baku gani ba hasalima halayana sun kasance masu saka ku fita a hayacinku lokuta da dama
Murmushi ya saki ya dora da fadin" ina fatan yanda na ga naki, na ga na sauran har zuwa kan Nusaiba
Ina adu'ar gidan aurenki ya kasance gidan da idan kin shiga in sha Allahu ba za'a fitar da ke ba har sai dai idan gawarki ce zata fito
Da sauri Ummulkhair ta kalle shi da mamakinsa, sai kuma ta mayar da kanta ta sada
Murmushi hakan ya bashi har ya kasance ya furta" ummu, dole na so kaina, ban san haka iyayen matan da na ringa yankawa tikiten zawarci suke ringa ji ba sai da na ji an shafa fatiyar daurin auren y'ata, sai abu biyu suka diro min lokaci daya tarin girmamen farin ciki da matsanancin faduwar gaban idanfa aka maido min ita? Sai na samu kaina da kebancewa na kai sujada na godewa Allah sannan na roke shi aa, ni kam kar na ga haka a ahalina
Ya kara tausasa muryarsa ya ci gaba da fadin" Zahrau, kina da saukin hali da biyaya, ki kara jajircewa dan gannin kin kai ga ci a gidan mijinki, ki rike adininki, kar ki yi wasa da ibadarki in sha Allahu komai zai zo da sauki
Kar ki yarda ki yi sake da su azkhar dinki duda na san dama ba mai wasan bace aman ki kara a kan na da, ke kin san rayuwar gidan sarauta daban take da rayuwar da ba ta gidan sarauta ba, yau ko dan zaki kebance a wajen da ba yan uwanki ba ni ba anmy dinku dole abin ya zo maki da wahala
Aman idan kika kwontar da hankalinki haka ne aure ya gaji haka ba inda baya kai mutun
Kanta ta ringa gyadawa kafin ya miko masu hannayensa
Baki daya suka karasa jikinsa suka dodora kawunansu a jikinsa shi kuwa ya lumshe idannuwansa yana hangen abubuwa a gabansa masu yawa, da farko dai yana jin wani abu na kayar masa da gaba haka kawai, sai kuma burin da ya ci dan gannin ya gyara rayuwarsa shi kansa kafin a kai ga y'ayan nasa, dan kuwa ya dauki hanyar da zai gyara irin zamansa da kowama , in sha Allahu zai je ya kara bibiyar matan da ya saka idan ya samu wa'inda basu yi aure ba har yanzu ya kasance sunna da kyawawan halaya zai nemi aurensu ya dawo da su cikin ahalinsa su zauna
Tabas ba zai saki Mardiya ba domin ya tabata Mardiya kam kadararsa ce
A haka Anmy ta idasa fitar da abubuwan da ta tanada sannan suka mike du suka dadauka
Kuka ne ya kwacewa Zahrau ta jimke hannayen Anmy
Anmy bata hannata ba sai kara sakata a jikinta da ta yi, a hankali ta shiga rada mata" mamanki na agadez, tana anguwar kara kara na saka an binciko min cewar a cen ta yi aure tana zaune da y'ayanta uku, abin farin cikin mutumen da take aure jajirtacen mutun ne mai tsoron Allah sannan shi ke bada karatu a fada, in sha Allahu kin fita daga cikin dangi zaki je wajen dangi ne, mun gama magana da uta yanzun dan ta fadan tana ta kiran Abihnki ya ki yarda ya daga , na gama bincikena in sha Allahu ba komai ku je kawai
Sai ta samu kanta da jin sasauci duda ba wata uwar shakuwa bace suka yi da mahaifiyar tata, aman sukan dan gaisa lokaci zuwa lokaci, bata san inda take aure ba sai yanzu hakan kuma ya mata dadi dan ko ba komai ta san ba zata rasa wasu yan uwan a cen ba duda family MUTALAB ba wanda zai kai zuciyarta irinsu
Mota daya tal ce, ba tambarin shaida ko su waye a cikinta kamar yanda motocin suke dauke da tamburan gidan sarki da farin sunnansa
Motar baka ce wulik sai sheki take sannan madubanta bakake ne wulik ba'a gannin na ciki ko kadan
Bayan motar suka bude aka sakata a tsakiya yan uwanta du suka shige gefe da gefe
Hannun Najeeba Anmy ta damko a sanyaye ta ce" na zuba masu tarbanku, na zuba datijan da nake baiwa amana sun bazu a cikin gidan
Kar ku manta gidan sarauta na dauke da hatsari, kar ku manta inda zaku je ku din baki ne sannan bakin dake tafe da abinda kila wa kala ne idan ana so
Ku kasance masu saka ido da adu'a, NAJEEBA kar na ji labarin fada a cikin tafiar
Kanta ta ringa gyadawa tana ta murmushi har Anmy ta gama fada mata abinda ta tabata Ummu ce ya dace a fadawa aman da yake utane uwar fada sai ake fada mata
Tana juyi kanta dan rufo motar sai da gabanta ya tsinke ya fadi
Wanda ke zaune wajen direba ne idannuwansu suka hadu , a ranta ta furta: *DUNKUM*
Gefensa kuwa sarkin garin Agadez ne
Da sauri ta sada kanta tana mai kara nutsuwa, lalle a yanzun ta yarda akoy gagarumin abinda ya saka Dunkum biye wannan aure da tarin taka tsantsan
Sai ta kara rike hannun yar uwarta tana mai tofa adu'a
Wayar Ummu ce ta yi kuka DAYABU ne da ya rigayesu zuwa aeroport din dan tabatar da wajen zamansu a jirgin da zai tashi nan da yan mintuna ne ke tambayarta sun fito ne?
Ta tabatar masa da sun fito sannan ya kali shugabar wajen dake tsaye dan hanya za'a buda sai sun dangana da cikin wajen da baban wajen ne ke zuwa da motarsa kafin su fito sannan sai an zuba dukan passinger sannan su shiga VIP dan gudun ido da daukan hankali kansu
Tun da ya dauki hanya ya shiga falfala gudu da motar kamar wani gagarumin direba
Sarafata ya yi cikin kwarewar da zai iya sarafa kujerar mulkinsa har ya sada su da wajen shiga jirgin
Sun kai minti ashirin a zaune kafin suke fitowa
Kukan dai take du sun damu da kukan nata sosai shi dai gaba ya yi sarki na biye da shi suka gama magana da Dayabu sannan suka shiga hawa
Dayabu kasa tsayawa ya yi su yi salama domin shi dama mai rauni ne a kan yan kannen nasa sai kawai ya yi masu nuni da zasu yi waya ya gudu wajen motar da sarkin ya zo da ita yana hangensu sai da suka shige aka dan samu minti goma sannan kofar ta daga ta rufe sai fatan sauka lafia
Basu wani jima ba suka sauka lafia a garin Agadez
Nanma a wata motar suka nufi masarautar wace sunna karasawa aka basu damar shiga dan da waya ya shaida masu a bude hanya
Direct bangarensa ya nufa da motar da su baki daya a ciki
Sai da suka gama zama su dukansu zama irin na hutu a tafkeken falonsa mai adon Abzinawa sannan ya aika sako wa matansa biyu kan yana falo su same shi
Mahaifiyar Zinaria ce ta fara zuwa da kuyanginta tana tambayar yaya aka yi ya dawo bata sani ba a cikin zuciyarta domin zinaria dai bata iya fada mata abinda ke faruwa ba hasalima tana cen ta gama shiryawa nufinta da ita za'a juya dan ta rantsewa mahaifiyar tata cewar bata san da maganar auren ba, tana cen tana jiran jin za'a tafi kai amarya ne
Turus ta yi a lokacin da ta karaso falon da salama a hankali tana kallon yan matan dake jere saman kujera mai tsayi daya da kujerar mijinta wanda ta tabata wanda ya yi wannan gangancin to fa ba karami bane a wajen mijin nata
Sai hakimtacen, nutsatsen, zakaran sirikinta dake zaune a dayar kujerar sarakan da idan sun zo sukan zama , sai mijinta gefensa sunna zaune tamkar abokai
Dan murmushi ta saki, nan da nan jakadiya ta shiga miko gaisuwa da gaisuwar sarki ta musaman kafin ta karasa saman babar kujerar uwar gidan sarki ta haye ta hakimce ita ga hajia baba
Sai ga mai dakin tsakiya itama ta shigo cikin shigarta ta alfarma
Ita kam bata tsaya turus din ba saima gagawar karasawa ta zauna da take dan bin umarnin maman Zinaria cewar ta kiyayi neman waje a wajen mijinsu!
Sai da suka gama zama kafin da hannunsa ya salami mutanen dake tare da su
Sai da ya sha iska irin ta sarakai sannan ya budi bakinsa cikin tausasawa ya ce" ina farin cikin dawowata gareku iyalaina,
Ina fatan na sameku lafia,
Kawunansu suke amsawa sai irin kurema yan matan ido da ta yi ta kasa kwakwaran motsi
Ci gaba ya yi da fadin" Alhamdulilah, tafia ta yi kyau, ina mai gabatar maku da kanwarku, abokiyar zamanku, yar uwarku GIMBIYA ZAHRAU a matsayin matata ta uku wace aka dauran aure da ita yau yau din nan a masarautar DAMAGARAM