← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 138

Sashe 8

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya sauke huci ya dago kafcecen bakin hannunsa ya ce" isa, yarinyar idan ka ganta tama dauke da idannuwan mage
Ka san yaya idannuwan mage suke? Sunna da girma da wani irin lu.u lu.u a cikinsu wanda idan har ka shagala zaka iya zubar da salabe tsabar kyansu da dukan zuciyarsu
Bakinta madaidaici ne, lebenta na kasa ya dan fi na sama girma sannan lebenta yanda ka ga ruwan kasa haka yake yana sheki kamar wani diamonds
Fuskarta yar doguwa ce, mai dauke da gashin gira wadatace wanda yake gyare kamar na yar tsana
Hancinta dogo ne sosai sannan da dan fadinsa kadan
Gashinn idannuwanta dogaye ne sannan bakake ne sidik ga cika wa'inda suka karawa fuskar nata wani irin kyau da haske
Gashin kanta wanda ya leko sosai ta kasan dan kwalinta baki ne sidik yana wani irin kyalkyali
Wani kanshi da take shi ya kara fuzgata zuwa gareta
A zaune take a cikin mota ba zan iya fadin yannayin jikinta ba aman abinda na sani ta tara hips domin irin yanda cinyoyinta suka baje a cikin bakar doguwar rigar dake jikinta
Fatarta kalar bak'a ce, bakin nan mai hasken gaske, ta shafa mai mai dan maski wanda ya saka fatar nata yin wani mus mus tana kara fitar da sirrin kyanta

Da mamaki ya ce" oga bak'ar mace fa kace? Aman oga ina ce ka tsani bak'ar fata domin ka sha fadin kai ko haukacewa ka yi ba abinda zaka ci da bakar mace dan ba zaka iya kayan haushi ba

Murmushi yana girgiza kansa ya ce" to ka dauka na sheka maka karya a wancen karon, ka dauka du da nake fadin hakan ban hadu da ainahin mace bak'a wace ta san darajar bakinta harma ta saka min sha'awarsa daga kallo daya
Ka dauka cewa wannan yarinyar ko nawa zan biya dan ta zama malakina zan iya biya
Ba soyayar shan minti ko na dare daya nake so da ita ba
So nake na kawota gidana ta sama min iri irinta na hada da jajayen buzayena na cika gidana da jarina

Shiru ya yi yana tunanin irin kukan shagwabar da ta dan sakar masa hakan ya sa tsigar jikinsa baki daya tashi da karfi karfi ya ce" rashin bani cikaken numberta kuwa ya nuna min cewa ita din mai tsada ce, kuma na yarda na siya

Shi dai baki daya ogan nasa yau ya rikita shi, dan haka ya ce" Oga na ji kace a mota take ko? Wace irin mota ce?

Juyowa ya yi ya ce" hilux ce baka sidik, sabuwa ce mai number Nigeria dan ko awo bata mata ba

Da sauri ya kale shi, ido ya zaro ya ce" Oga, ko dai *NAJEEBA* kake magana a kai?

Ogan nasa ya ce" wacece haka?

Ya ce" Najeeba mai saloon NAJEEBA MUTALAB, wannan baban saloon din da ake magana baki daya garin nan
Da kace mota baka Hilux sabuwa na tuna ba'a yi sati biyu ba da zakariya ke fadin ta dauko sabuwa domin budurwar uban gidansa ce

Da sauri ya ce" kana nufin yarinyar da na gama zana maka ce budurwar csp Jibril?

Da sauro ya ce" oga ai idan dai *NAJEEBA* ce, ita da kanta *MAGE BA, MAI KWONCIYAR DAUKAN RAI* wannan shine kirarinta
Budurwar juju isma'il ce,
Budurwar Elhaj razak ce wannan baban dan kasuwan

Shiru ya yi sakamakon irin yanda ogan nasa ke kokarin bige shi

Bakinsa mai dauke da hakora mai tsawargna ya hade da kishin NAJEEBA cikin zuciyarsa ya ce" kana nufin yar hannu ce? To koma yar hannu ce ni zan kwasheta
Ai allura ce cikin ruwa
Ka je ka samo min asalin numberta ni kuwa zan nuna masu su kauce idan basa iyawa

Wata daria ya yi ya ce" zan yi mata bulala da tarin kudina
Zan wanketa wankin da zai haukatata
Zan gabatar mata da maganar aure na shinfide mata sadakin millions goma
Zata gigice ne ta amshi aurena ta kawo kanta dakina

Da sauri ya juya ya fita , shifa nan take ya ji tausayin ogan nasa ya kama shi
Sai kuma ya daga kafadunsa yana fadin" mai yiwuwa y'ayan mutane da kake lalatawa ne kaima zaka hadu da ciwon zuciyarka, dan na tabata baka taba haduwa da mai wanke aljihunka a lokacin da kai kanka baka ankara ba sai yanzun dan tas zata cinye maka tanadinka

Wuni ya yi yana yawo yana bin kama daga yan matan garin masu ji da kansu har zuwa yan daudu
Aman du wace ta santama bata bada number sai dai ta fada masa ya je ya amsa

Cike da gajiya ya dawo yana tunanin yanda zai yi

Yama na yi ya shirya da wuri ya fita wajen gudu, wajen da ake basket ball, da hand ball, da dai sauransu

Ya jima zaune, harma an fara buga kwallon har an tafi sallar magariba an dawo
Har ya cire rai da zuwanta sai hango bak'ar motarta ya yi ta danni kai

Hamdallah ya yi ya kara gyara zamansa

Daga cikin motar bayan ta kashe ta ziro kafarta guda

A hankali ta ziro dayar kafafuwanta dauke da wani takalmin basket fari tas mai nike ja
Kana gannin takalmin ka san babar harka ne zai kai dubu tamanin a kadan

Karasa fitowa ta yi daga cikin motar hannunta dauke da ball dinta ta rufe marfin ta shiga takawa

Yawancin samari da kuma yan matan wajen sun bada hankakinsu kanta wasun kuwa satar kallonta suke
Da yawa samarin sunna jin inama ace budurwarsu ce?
Wasun kuwa sunna mangarin irin kayanta na sport wa'inda ko wace rana zata zo da sabin yayi masu motsi
Da yawan yan matan wajen sunna mangarin irin yanda idan ta saka kaya ke mata kyau, wasu na son yin kawance da ita wasu kuwa na matukar jin haushinta da kishinta duba da irin yanda take dauke hankalin manyan mazan dake wajen manyan ma'aikatan dake fitowa motsa jiki da yawansu sum girmeta girma ba na wasa ba aman kuma ta fi su farin jinni
Idan kudin ne akoy wa'inda suka dameta suka shanye aman an fi hangota kansu

Da tarin nutsuwa ta karasa jikinta sanye da dogon wando wanda ya kama duwawunta dan irin girmansu sai dai ya saki daga kasa
Sai rigarta ta gudu mai dogon hannu wace tana zuwa ta cireta sai ta kasa ja wace ke dauke da karamin hannu

Baki daya kalar fatarta iri daya ce kama daga wuyanta, fuskarta, hamatarta idan ta daga dan amsar ball din a aske tas kuma ba wani baki kirin ko yannayi mai nuna rashin kula tas tas tas haka take

A hankali ta shiga gudu dan ka'idane idan ka zo sai ka zagaya terrain din sau hamsin kafin a raba da kai a hau buga basket din

Tana gudun ne tana dan buga hannunta da du wanda ta tarda dan gaisuwar ne haka, sai dai idan ta tardo namiji bata hade hannunta da shi sai dai ta daga masa hannun kamar zasu hade sai ta wayance ta kauce tana daria

Sai da ta gama aka raba da ita ta hau saman filin basket din

Sun kora da bugawa, ball din na hannunta tana gudu tana dokata da kasa ball din na dawowa tana neman wanda zata ba kawai sai ji ta yi an rukunkumeta daga bayanta wanda sam ba haka a basket idanma amsar ball ne zaka yi sai dai ka tinkari mutun idan ka yi sa'a ka amshe halas idan kuwa ka kasa wani ya kuma tarbansa ko ta gefen mutun aman sai gashin an rukunkumeta kuma namiji ne domin daga hannunsa da irin rikon da kuma warin zufar da yake ya shaida mata hakan

Da wani irin firgici ta saki ball din, tana juyowa ga mamakinta dan wajensu ne bama dan dayan bangaren bane
Wato ya yi haka da gaya ko?

Ranta ne ya yi kololuear baci duba da yau itace wannan bakon ba'adaren ya tabawa jiki harda kwonto mata a jikinta ya dora hannunsa afatar jikinta harma saman hannunsa ya goge kasan mamanta

Baki daya jikinta ne ya dauki rawa....ka ku manta NAJEEBA nada rashin ji, aman fa ba ta inda ake zato ba

Ba zato ba tsamani ta daga hannunta ta.......

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

6

Ba zato ba tsamani ta daga hannunta ta sauke saman fuskar garjejen ba'adaren da ya rungumota jikinsa

Bako ne, shi bako ne sannan dan baba da rai ne
Ya saba life, yana gannin NAJEEBA ya yi tunanin yar life din ce hakan ya sa ya fara isar da sakonsa ta haka dan ta gane ta yi sabon kamu
Sai dai abinda ko ubansa bai taba yi masa ba ya ziyarce shi a lokacin da bai shirya ba

Idannuwansa ya waro da karfi da mamaki wanda sakamakon marin ya saka baki daya hankali ya yo kansu

Bata taba tunani ba, bata taba shiryawa ba sai ta yi ya daga dafkekiyar kafarsa ya daga mata bugu a cikinta

Wata irin razananiya kara ta saki kafin ta tafi luuuuuuu a sume

Gaba daya wajen hautsinewa ya yi ya hargitse

Zaratan mazan dake son malakarta suka hayayako inda zaratan yan matan dake hasada da ita suke kokarin tare masa

Shima cike da sangarta ya kara fitar da idannuwansa yana fadin" ni bani da rai da ta mare ni ne?

Da wani irin sauri wani baban soja dake wajen Captain ne ya daka tsawar da ta saka du suka fara shiga taitayinsu harma wasu suka shiga silalewa dan kar abinda basu taka ba su kwashe

Hannawa ya yi a tabata, ya kirayi ambulance sannan ya tsare wanda ya yi dukan ya yi kiran police dan shi soja ne baya kamu sai police

Nan fa wajen ya hargitse aka shiga yada maganar ta waya da kuma wa'inda suka rigaya suka silale

A lokacin DAYABU na zaune a katon falon SARKI , sun gama cin dadadan abincin da aka gabatar masu , ya kwontar da muryarsa yana kokarin kara bashi hakuri kan ya manta marin da NAJEEBA ta yiwa Zinariya
Chapter 8 · 0% Book details