← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 138

Sashe 29

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adu'ar neman tsari ta ringa yi da miyagu
Kasancewar ya saka shada marron sai gaba daya hasken fatarsa ta kara fitowa
Daga sajensa zaka gane mai summa ne sosai sannan baka ce sidik summar
Kwalin idannuwansa dake nuna kansu ko a cikin dare ne sun kuwa nuna kan nasu da taimakon fitilun dake kukune

Karasawa ta yi ta zauna a wajen da take zama hakan ya sa suke facing din junna

Shima bai yi tunaninta a wajen nan a irin wannan lokacin ba kasancewar ya san cewa ita din kirjin biki ce du inda ta ji da maganar biki ko ba na gidansu ba zuwa take bale yau nasu?

Kura mata ido ya yi gannin ta kasa bude abinda ke ledar sai dan jujuya cokalin hannunta take
Shin dama tana da kunyar cin abu a gaban bakon ido ko cikin salon yaudararta ne da neman janyo hankalin namiji a kanta?

Basarwa ya yi ya ki yi mata magana a yau din ya daga kansa sama yana gannin yanda farin wata ke kara haske

Kasancewar ta rasa nutsuwar hutawar ya sakata kallon wajensa

Sai da ta yatsina bakinta a hankali ta ce" hi

Dagowa ya yi daga kallon saman ya sauke a saman kanta

Da sauri ya cire idannuwansa domin dinkin lesh din nata daga gaban kirjinta an yi kata wani heart ne an cire wajen an zagaye shi da kyalkyali aman kuma an baiwa mararabar kirjinta damar bayannuwa sosai

Kai kam ina ne gidanku kake zama a nan koda yaushe? Ko a saman bishiya ne?
Ta fada tana nuna masa bishiyar dake wajen

Shima bishiyar ya kalla, sai ya ji murmushi na zo masa, wato da alama a tsoracema take da shi ko?

Kafadunsa ya dan daga a hankali ya ce" daga wajen auren sarkin garinnan nake, na gaji shine na zo nan na huta

Bakinta ta dan tabe ta daga kafadunta

Muryarsa mai sanyi ta kuma jin ya ce" daga ina kike haka? Me kike zuwa yi nan? Ko kema daga wajen auren sarkin kike ne?

Dago idannuwanta ta yi ta sauke saman kansa a hankali ta ce" ban san shi bama ni sarkin nan, sannan wajen nan wajena ne ban san dalilin da zaka tambayen me na zo yi ba

Wajenta ne? To ka ji ya fada a ransa

Mikewa ya yi cike da isa ya dawo kusa da ita ya zauna inda take binsa da kallo har zamansa

A hankali ya ce" freind?

Hannun nasa dai ya miko mata yauma, shi kam ko a inda ya fito haka yake gaishe gaishe da mata? Duda yanzu abin ya zama ruwan dare dan gaisawa da mace ba wani abu bane da namijin da ba muharaminta ba bayan ba kyau

Murmushi ta yi tana hararan hannun nasa a hankali itama ta ce" zan yi tunani

Haka yauma ta bara masa hannun sakaye yana binta da kallo har ta shige motarta sannan yauma bata dauke abin cikin ledar nata ba nan ta bara masa su ta yi tafiarta

Kansa ya gyada yana ayanna" du salonki, sai na ga ainahin wacece ke! Du iya tsare tsarenki na kwana da sannin ke din *MAGE CE MAI KWONCIYAR D'AUKAN RAI*

da wani irin sauri amintacen dogarinsa ya karaso wajen da yake zaune ya zube kasa kansa kasa jikinsa na rawa ya ce" Allah ya ja da kwananka, Allah ya taimaki mai damagaram kiran gagawa ya samu daga wajen Gimbiya Allah ja da rai

Da sauri ya kalle shi ya waiwaya baya ya ga har ta tafi
Kira daga wajen gimbiya da gagawa?

N
Mikewa ya yi yana takawa ya nufi motar
Bai shiga ba sai da ya mayar da rawanin kansa ya dora alkyabarsa ya cenza takalminsa ya rige sandar girmansa sannan ya shige baya ya lafe

Jan motar yake gabansa na faduwa duba da irin abinda aka fara fada masa

A haka suka samu shiga ta baya suka shige suka karasa wajen da Gimbiya ta umarci a kawo shi

Du mutannen wajen dukawa suka yi a lokacin da aka shiga shelar shine

Cikin taku irin na kasaita ya ringa daga kafarsa daya na korar daya har ya karasa wajen da GIMBIYA ke tsaye tare da y'ayan yan matanta
Yannayin tashin hankalin da yake karanta a fuskarta shi ya saka shi kara rage hanzarin tafiarsa

Motar da ya bada dan kawo amaryar nasa ce ya ganni a bubude
Wasu mata ne ya ganni a duke nesa kadan aman kuma kuka suke

A hankali ya kai dubansa wajen motar

Idannuwansa ne suka sauka kan wasu fararan kafafuwa da aka fitar
Irin yanda kafafuwan suke ajiye ne zai shaida maka mai su idan dai ba barci yake ba to yana cikin halin rashin lafiar da baya iya motsa su

Da alama kuma mutumen dake ciki ahi daya ne

Haka kawai ya ji zuciyarsa ta doka da wani irin duka mai tsanani
A hankali ya karasa gaban mahaifiyarsa

Kansa ya dula sosai ya ce" Allah ya ja da ran Anmy

Anmy ta dago tana dubansa cike da fargabar abinda zata fada masa da tausayin yarinyar dama shi kansa da iyayen yarinyar

Me zata ce masa ne?
Ce masa zata yi su kansu yan rakiyar yarinyar basu san cewa ta rasu a cikin kotar ba har sai da aka zo aka kamo hannunta dan fitar da ita a sadar da ita da dakin mijinta? Ko kawai ta ce da shi SHAHEED ALLAH YA YIWA YARINYAR DA KA AURA YAU RASUWA?

SAI TA RASA KALMAR DA ZATA IYA HADAWA DAN SAMUN WANNAN BAYANI

BAKINTA NE YA SHIGA RAWA A LOKACIN DA TA BUDA TA CE"
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

17

A hankali yan matan suka marmatsa bayan sunna dan dukawa sunna nan afuwa suka barshi tsaye gaban Anmy

A hankali ya jinginar da sandar hannunsa ya saka hannayensa biyu ya dago fuskar mahaifiyarsa

Irin yanda kwayar idannuwanta ke cikowa da kwallah ne idan wani abu mai rikitar da zuciya ya faru ya ganni

Kwonce kwalar take a kurmin idannuwanta hakan ya sa fuskarta yin wani iri

Sauran matan tsohon sarki biyun ne suka karaso suma da yannayin juyayi a fuskokinsu

Fulani ce ta dora hannunta saman na sarkin dake gefen fuskar mahaifiyarsa

A hankali ta girgiza masa kai wanda hakan ya saka shi saurin rintse idannuwansa domin wannan lamari shi ya faru a lokacin da ya rasa mahaifinsa
Sun ringa dafa hannunsa ne sunna girgiza masa kai

Da sauri ya maida dubansa wajen motar nan

Kafarsa ya daga zuwa wajen motar nan bai ko dauki sandar ba ya karasa kusa da kafafuwan dake sanye cikin wani fari kar din silifas irin shirin da ake yiwa amare dai
hakan ya saka Gimbiya saurin rike hannun Fulani ta lumshe idannuwanta tana tunanin irin abinda yaron nata zai iya ji, dan ta tabata yarinyar nan yana sonta duba da har aka ji kamshin turaranta a tufafinsa kuma bai musa ba har aka bashi damar aurenta ya amsa da murna ta zama matarsa a dan kankannin lokaci ashe ba zasu raya zaman auren tare ba?

Fararan hannayensa ya saka da suke dake ya dora saman fararan kafafuwan nata

A hankali ya idasa saka hannunsa ya saka kansa cikin motar baki dayansa
Daidai lokacin da kunnayensa ke jiyo masa kukan tsofafin da suka rakota dakinta kamar haka" ashe ba zaki ga dakinki ba Bintu, Allah ya jikanki da rahama Binta, Allah ya haskaka makwoncinki salihar yarinya mai hakuro da nagarta

Zuciyarsa ce ta doka da sauri ya saka hannun nasa ya yaye rufar da akaiwa fuskarta

Fuskar nata ya tsurawa ido
Fara ce sal, sannan fuskar nata ya amshi mahaukaciyar makup mai iya doka zuciya ta saka a ji an kamu da son mai dauke da ita
Irin gashin idon nan natural ta saka mata shi ya yi mata wani irin gazar gazar duda idannuwanta a rufe suke ruf domin Anmy ta rigaya da ta shafe mata ido

Dagowa ya yi a karo na farko ya bi mutanen sake wajen baki daya da kallo

Muryarsa a saukake ya ce" ku je

Daga ku je din bai dora komai ba, sai dogarai dake faman aikinsu
Ya rage daga Anmy sai y'ayanta sai manyan datijan dake wajen

Kansa a kasa ya furta" iyayenta sun ji?

Anmy ta gyada kanta ta ce" yaya ya tafi wajen mahaifinta dan na jima ina kiran layinka bana samu, sai daga baya na kirayi amintacenka

Kansa ya gyada a hankali ya kuma fadin" zan kimtsata da kaina, zamu kwana yi mata adu'a, Anmy in sha Allahu zata samu sutura nagartaciya zata yi makotaka da Abih da kuma Aliyu, ina fatan da kuma adu'ar ta kasance a fadar ma'aiki

Salalahu alaihi wa salam suka amsa a hankali

Anmy ta ce" a ina zaku yiwa gawar karatun? A ina zaka kimtsata?

Ajiyar zuciya ya kuma saukewa mai zafin gaske ya ce" a bangarenta

Hannunsa ya kara mikawa ya kamo na mahaifiyarsa ya ce" Anmy, ku je bangarenki, ba komai ku yi ta adu'a

Kanta take gyadawa ta maida dubanta wajen motar ta kuma kallo

So take ta fashe da kuka, so take itama ta saki zafin da take ji ta yi kuka sosai, sai dai ba halin hakan, an jima da horar hawayenta da tsayawa a lokacin da ya dace ta zubo su, an jima da horar zuciyarta da wata irin dakiya wace ke ritsa zuciyar ta yiwa zuciya lahani
Hakama yaronta ya taso da horo wanda ya fi wannan tauri a matsayinsa na d'a namiji kwalin kwal a wajen mahaifinsa wanda ya rayu, ba wai ba'a taba haihuwar wssu mazan bane, no, an haifa du basu zauna ba sai mata da suke yayunsa du ba a nijer din bama suke aure hakan ya sa basu halarci auren kannin nasu ba bama kowace ta ji zai kara aure ba dan shi din ba mai magana bane kuma basu yi waya da anmy ba, shirye shiryen zuwansu da suke na su yi jajen rasa Aliyu ne

Baki dayansu suka rankaya suka tafi bangaren Anmy

Yana nan tsaye da dogaran yana ta dube duben cikin motar da komai mahaifinta ya karaso da mahaifiyarta
Chapter 29 · 0% Book details