Sashe 105
Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
DAU kake jin karar wani mahaukacin marin da ya saka NAJEEBA dauke wuta lokaci daya , domin gaba daya hayaniyar nan ce ta dauke mata ta daina jin maganar kowa, sai kuma fatar idannuwanta sukai mata nauyin tsiya a saman lebenta take son furta kalmar nan kwaya hudu wato *yaya ka mare ni?*
Aman fir maganar ta ki fitowa a lokacin da ya warci hannunta dake cikin na Police din nan ya yi mata wani irin ja ya karasa kusan yayunta da du suka aniya kare fuskokinsu sai dai cikin ikon ALLAH da hannun nasa na hagu ya shiga sauke masu tankadeta mareta ciki kuwa harda bakuwar yau tau, wace yau yau ta fara irin haduwar nan da su haka, hakan ya sa ta kwala wata kara idannuwanta waje ta dafe kuncin nata tana zazaro ido cike da mamaki da tsoro da tashin hankali harma ta ringa jin zata saki fitsari
Luuu take yi daga bayan DAYABU wanda bai cika hannunta ba ya aniya zazaga masifa, sai dai lokaci daya ya yi tsittt sakamakon irin yanda jibga jibgan dogaran Fadar suka shiga cika wajen da wani irin bulaloli a hannayensu sunna dakatar da du wanda bai rigaya ya baiwa kafarsa mai ya kara gaba ba, sunna gurfanar da su
Lokaci daya Amintace ya ware babar muryarsa fuskar nan tasa a hade ya furta" ku zube a kasa, ga MAI DAMAGARAM zai karaso, kowa ya kai gwuiwarsa kasa ya sanda dubansa ko kuwa na rantse da wanda raina ke hannunsa zan saka babarbara na yanke kafafuwan mutun sannan na kwakwale idannuwan shege domin ga MAI WUKAR YANKA NAN TAFE
Cikin ikon ALLAH tun daga kan polisan, har zuwa su yaya DAYABU da sauran mutanen dake wajen du suka zube kan gwuiwoyinsu, a nan ne NAJEEBA ta tafi luuuuu ta kusan faduwa kasa, sai dai Yaya Dayabu bai bari ba ya saka hannunsa ya tarota jikinsa yana kallon fuskarta gabansa ya fadi, a hankali ya dora kansa saman goshinta hawayen da yake ta rikewa dan marin kannen nasa da ya yi suka samu damar fitowa, Zahrau kuwa hannunta na rawa kasa kasa ta kara tauke kullin hannun NAJEEBA kafin ta saci kallon dogaran nan da baki dayansu suka yi wani irin gurfanawa hannayensu a jijimke sunna masu kawo gaisuwa sai dai ba magana, wajen kuwa ya yi wani irin dif ba magana sai ajiyar zuciya kala daban daban dake tashi, sai kuma takun tafiyar dake shaida koma waye ke yinta yana yinta ne da fushi, da kuma karfi
Zuciyoyi ne suka shiga tsintsinkewa a lokacin da Amintacen sarki ya kai gwuiwarsa guda kasa dayar a tankwashe ya dago jimkaken hannunsa kansa a kasa muryarsa sama sama ya ce""""""
Hello mutanen yaya ne😊, sorry walahi yarinya ne ba lafia, godia nake da sauki yanzun Alhamdulilah🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*Na*
*SAJIDA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
53
Sai da ya ware murya, wanda hakan zai iya tsoratar da wanda bai saba ji ba, ya nutsar da wanda ya saba ji, jikin mutun ya kwashi tsuma ba tare da shi aka koda ba amintacen sarki ya ce" Gagara badau kake dan sarki jikan sarki, takawarka lafia jarumi hamshaki barde, kai ne namu kai ne nasu kai din na kowa ne, tafiyarka ke shaida sahunka Mai wukar yanka, kai ne usulin Babarbara ba itace usulinka ba, daga kasa kake dagowa sai ka nuna sama ka saki, baka fito ba sai da ka shirya *SULTAN SHAHEED ABDUL MALIK ALI BUZU* Takawarka lafia miji a wajen *ZINARIA, NADIA DA NAJEEBA,*
Idannuwansa da suka cenza launi ya daga a hankali ya sauke dubansa a kanta, gashin kanta da ta daure ribom din ya kunce gaba daya gashin ya sauko sosai yana walagigi
Hannayenta a fili, dama dama rigar bata yaye ba sannan da safa a kafafuwanta
Dan gyaran murya ya yi a sanyaye hakan ya sa amintacensa mikewa da sauri tsaye
Da idannuwansa ya kai dubansa kan Habu dake ta rawar jiki ya dan dantse gefen lebensa sannan ya kuma duban police din nan
Ba magana ya yi ba, aman irin kwatancen ya yi ya saka amintacensa fahimta
Nan da nan aka shiga salamar mutanen banda su biyun nan
Du kawunnansu a sasade suke ba wanda ya dago har aka fitar da mutanen nan baki daya sannan ya sauke dubansa kan bakuwar fuskar dake cikinsu
Bai ce komai ba sai takawa da ya ringa yi har ya karasa wajen da suke tsugune
Hannayensa ya saka ya dan rage tsayinsa
Hannunsa dake talabe da ita ya cire sannan ya dauketa da hannayensa
Muryarsa ciki ciki ya ce" ka kai Bilkissu aeroport yanzu
Daga haka ya juya da NAJEEBA a hannunsa ba tare da ya kuma bi ta kan kowa ba har ya bacewa ganninsu
Sai da Amintace ya basu damar dago kansu sannan du suka dadago a tsorace, dogaran nan ne suka kara korar kowa suka rurufe sannan suka dora gadi a wajen
Kuka Zahrau ke yi bilhaki, domin ko gidan fir an hanna mata komawa , DAYABU ya dubeta yana tuki zasu karasa aeroport murya da fada fada ya ce" Zahrau, ko ki min shiru ko kuwa na baki mamaki a nan, aman kin ban mamaki, kin bani mamaki Zahrau, kina tsaye kina kallo? Da darajarku da komai ku zubar da wannan rashin mutuncin? Zahrau kin san waye SHAHEED a kan NAJEEBA? Lalle ina mai adu'ar Allah ya sanyaya fushinsa, ina rokon Allah ya sasauta masa damuwarsa, Zahrau SHAHEED ne ya fito da kansa a irin wannan lokacin ya dauki NAJEEBA da hannayensa a gaban dogaransa, Zahrau kun bani kunya"
Wani kukan ta saka tana yarfe hannayenta ta ce" yaya dan Allah ka yi hakuri, ni kaina sai da na ga abin ya idasa rikicewa, yaya ban gane ban san SHAHEED a kan NAJEEBA ba?"
DAYABU ya girgiza kansa kawai ya yi mata shiru, har sai da suka karasa gidan jirgin sunna zaune dan bai saura minti ashirin su daga ba a hankali ya ce" Harda dan daudu, ga maza nan sunna son rungumota a jikinsu, shin sake na yi da tarbiyarku har haka ko menene?"
Sai kawai wasu hawaye masu zafi suka shiga bin gefen kumatunsa, hakan ya mugu mugun kara daga hankalin Zahrau dan haka ta ririke hannayensa tana ta girgiza masa kai hankali tashe muryarta a rikice take fadin" Dan Allah kar ka yi mana kuka, ka dakemu, ka yi mana komai dan Allah kar ka tuhumi irin tarbiyar da ka bamu domin kuwa mu mun san kai din ubanmu ne"
Kansa ya girgiza a hankali ya ce" Zahrau, Allah ya yi rayuwarmu wata iri, tabas na san ba wanda zai iya raba NAJEEBA da fada, aman ban yi tunanin a yanzu da take amsa kiran matar SHAHEED zata cike mayafinta ta nemi dakuwa da wata matar da bata kama darajarta ba, ZAHRAU kema dake dauke da taki darajar kika tsaya a matsayinki da kasancewarki yayarta kuke danbatuwa, to bara ki ji, wace aka turo din AMMI ta kama wayarta dazu kafin mu iso tana fadin ta tabata idan har aka tsokani NAJEEBA sai ta rama, idan kuwa ta zubar da hauka a cikin masarauta ga kishiyoyi ga mijinta mai zafi ana iya kilaceta a dakin horo, daga nan ko uban me take takama da shi an karya saura uwarta, Zahrau wato maradinku ba zai ji kunya ba? Me zai faru, me zai yi mata, Allah masani, aman kun cutar da zuciyata"
Kanta ta dora gefen hannunsa tana hawaye, ita kanta zuciyar tata ta mugun raunana, shin Najeeba wace irin zuciya ne da ita mai karfi fada haka? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une idanfa aka sakata dakin horon? Idan labari ya kaiwa zinaria fa?"
Motar shiru ta dauka a haka har lokacin tafia ya yi, nasiha ya kuma yi mata mai ratsa zuciya kafin su rabu tana ta hawaye, sai da ta shiga ta ga GIMBIYA hakimce a wajen VIP din, dama nan suke zama hakan ya bata mamaki matuka, ta gaisheta da mutuntawa aman ita sai ta cire kai kamar bata santa ba.
Zaune yake ya cire rawanin, kansa sade kasa ya dafe kan nasa da hannayensa biyu biyu yana kallon kasa
Da wani irin sauri AMMI ta nufi wajen NAJEEBA dake shinfide saman doguwar kujera, UMMU kuwa ta yi wajensa hankali tashe ta saka hannunta ta cire nasa tana kallon fuskarsa har sai da gabanta ya yanke ya fadi
Idannuwanta ta lumshe tana jin wani irin daci a zuciyarta, tabas AMMI ta fada mata komai dangane da wayar Mardiya, ita ta hanna a shaida masu dan tana son gannin yaya zasu tafiyar da abin, sai gashi cikin sauki sun tafka rashin hankalin da abu daya take jira shine gannin farkawarta ta nadi jikinta tamkar an aikota
A hankali ta ce da SULTAN" ka yi hakuri "
Idannuwansa ya lumshe, ya kuma budewa a kan UMMU, ya kama hannun nata na dama ya rike a cikin tafukan hannayensa, a hankali ya kai wajen zuciyarsa ya dora yana kara cije lebensa na kasa
Sosai ta kara tsorata tana kallonsa da dan saurin magana ta ce" subahannalah, menene wannan bugawar da zuciyarka ke yi? BILKISSU zo kama min" ta karashe tana azamar mikewa tana kara tataba jikinsa
AMMI ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Dukanta ka yi ne Shaheed? A summe fa take ka barta kwonce haka? Menene ya yi zafi haka Shaheed, dan Allah ka yi hakuri ka sasauta, NAJEEBA yarinya ce sannan ka san rigimarta a hankali du zata daina"
Idannuwansa da sukai masa mugun nauyi ya cire ya dora kanta, shimatt a kwonce take yar baby face dinta ta fito radau, AMMI na kokarin cire mata rigarta har sai da ta cire mata ita ta kai mata ita wajen cikinta hakan ya bayanar da bras din dake cikin rigar fara tas da lafafen cikinta Ammi na tofa mata adu'a bayan ta gama waya da likitan masarautar