← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 138

Sashe 104

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da Habu ya kaleta sama da kasa ya ce" ke kuwa baki san inda suke ina nan ba? Ai a jikinsu nake ci, sannan da kike cewa a bar haka kin taba gannin gidan kitso ba runguntsumi?, dubansa ya maida wajen NAJEEBA dake kallonsa, ita kanta a kasan zuciyarta uban mamakin ta inda ya shigo a yaushe ya shigo take, idan bata manta ba tun da aka dora masu zama da dogarai aka hanna masa shiga shagonta, Habu yana yi mata aiki ne ta hanyar kawo mata mutane sosai da sosai, idan ya zo waje kuwa zai zauna a sha hira da shi ne ya yi tafiarsa, bayan wannan ba wata alaka tsakaninta da shi domin ko irin biki nasu na yan daudu bai taba fada mata dan ta fada masa gaskiya itafa wannan abin baya bata sha'awa nema kwata kwata shima tana masa fatan shiriya

Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta ce" to in bama gagawa irin ta dan adam ba, MUTALAB fa goma sha shida ya kyankyashe mata, ciki kuma biyu kawai ya kilace a dakin miji, suka san ko na tausayawa wahalar yan tsofafin mazajensu na mika masu wata jinnin MUTALAB din? Kun san abinda ya yi yaya shi ya yi kanwa"

Daya daga cikin kawayen Mardiya, wace ta bata wannan rana takanas tare da fada mata sirrin nan, bama kawarta bace kawar kanwarta ce wace ta turota takanas dan a kunna masu , rikakiyar yar bariki ce kana ganninta ka ga wace ta auri duniya auren zobe ta yi kas kas kas da cingan ta ce" kwarai kuwa hajiyata, ai MUTALAB ya iya haihuwa, aman ba ku goma sha shida babe matan, ku goma sha Bakwai ne ko kin manta wace aka samu *KYAUTA?* (irin sararsu ne, zaka ji an cewa yaron da Allah ya yi aka same shi haka KYAUTA)

Sai da Zahrau ta kusan faduwa daga tsayen da take, a tsorace ta kai dubanta wsjen wace ta yi maganar hakama su UMMUKULSUM ,
Najeeba kanta sai da ta rintse ido, aman kuma dama walahi ta shiryawa irin ranar nan, ta san da a irin yanda ta tarawa kanta neman magana sai an binciko sirikan rayuwarta dan a nemi tozartata, tama yi mamakin sirrin gidansu da ya jima haka ba tare da an jima da bankado shi ba, shi yasa ko ba komai take gannin ba laifi Mardiya fa ta yi hakuri, domin tsayin lokacin nan bata fada ba sai yanzu ai kuwa ta yi kokari

Kannanun magangannu ne suka shiga girmama, harma wasun na neman karin haske da maganar KYAUTA

Najeeba ta girgiza kanta ta ce" kai dan duniya, dan duniya bai yi ba, wato shi ko yaya ka yi da shi hakan take gareshi, kwarai kuwa mu goma sha shida ne kamar yanda na fada hakan ne, domin duniya ta san MUTALAB ya haihi y'aya goma sha bakwai ne, maza biyu, mata goma sha biyar, a yanzu da na gano munada yar uwa sai nake fadin sha shida, abin farin cikin alfahari nake da Ubana da bai zubar da yar kanwata ba, ya haifo abinsa santala sannan ta samu kilacewa wace zata yi min wuf da mijin daya a wajen nan alkawari ne........ta karashe tana mai sakin murmushi ta kai dubanta wajen Aida ta ce" ina take?"
Da sauri Aida ta shiga dakin hutun NAJEEBA ta fito da wata budurwa kyakyawa mai tsayi irin na yan uwanta, kamarsu daya sai dai ita din fara ce, sannan hijab ne jikinta yannayinta ya nuna tana da dan tsoro domin sai rarabewa take

Su kansu yayunta sun sha mamaki, a hoto suka san yarinyar yaushe Najeeba ta santa har ta kawota?

Da sauri Najeeba ta fincike hannunta da take jijimkewa ta ce" Jinnin Mutalab Allah kawai yake tsoro, jinnin Mutalab dokokin Allah yake karewa, haduwa da shi kawai yake tunani, idan ba dan haka ba da ya yanka dan mutun sai dai uwarsa ta haifo wani ba shi ba! Sakar min hannunki ki kalli du wace ta bi ki da kallo daidai misalin wanda ta yi maki, idan yar mutunci ce ki yi mutunci da ita, idan ba yar mutunci bace kika daga mata kafa walahi sai na tsinka maki mari, kema ganninki kika yi, suma wa'inda suka same ki daga ke basu kara wata ba hakan na nufin kadara ce ta afka masu wace ba yar shegiyar da ta fi karfinta, ina alfahari da ke, ZAHRAU na Alfahari da ke, Ummulkhair na alfahari da ke, Ummukulsum na alfahari da ke, mu kam muna alfahari da ke a ahalinmu"

Zahrau ta matso kusa da su su hudun, tana kallonsu ta lumshe idannuwanta ta ji wani dadi a kasan zuciyarta, burinta dama itama ta dawo cikinsu ashe yar rigimarsu har ta kawota gidan nan? Hannunta ta kama a hankali ta dan murza sannan ta sakar mata murmushi wanda ya sakata fashewa da kuka ta shiga rungumarsu cike da wani irin farin ciki, ashe zasu karbeta? Ta sha labewa ta kalle su tana son su a ranta aman kuma tarin tsoron ta kusance su ya saka kulun take kara hangensu daga nesa, tunaninta kar ta kusance su, su fatataketa dan ta kasance ba da aure aka haifeta ba, ko a message din da suke da NAJEEBA walahi gani take wasa ne, ashe dai da gaske ne? Ita kam ina zata saka ranta dan murna da farin ciki?

Habu ne ya ringa kikifta ido yana gannin yanda wajen yake kara daukan haramar rikicewa a fili ya ce" toh fa"

Zahrau ta dan zunguri keyar NAJEEBA a hankali ta ce" itace surprise din da kika ce min kin adana mana?"

Najeeba na satar kallon budurwar nan tana kokarin fita ta gyada kanta da wani irin sauri ta saki hannun yan uwanta ta finciko hannun budurwar da ta kasance karya uwar fada, domin dai ita sanadiyar fada du an yayage mata fuskarta da reza an yi mata dinkunna hakama a wuyanta tafka tafkan dinkunna ne na ciwo ga kuma wajen girarta

Ai kuwa a shirye take, ita ta fara kokarin kaima NAJEEBA bugu, cikin ikon Allah wajen ya nemi harfitsewa domin kuwa da kyau NAJEEBA ta ware take rama rigimar da bata yi ba na satitika dan kuwa har ta tsigewa budurwar nan kitson kanta jinni ya fara zuba hakan ya sa itama cike da bacin rai ta ciro rezarta ta nemi yanke mata jiki, daidai polisan nan sun shigo da gudu dan Zahrau ta kirasu tana ihun su taimaka, Najeeba kuwa ta saka hannunta ta tare rezar sai aka yanketa a hannunta yanka mai girman da jinni ya bale mata

Yanda suka ringa hankado du wani mai rigimar waje ne ya saka shi kara tsaida abin a kansu yana kallo
Su kansu sai a nan suka ankara da Habu, shima sukai waje da shi

Kokowa ce ake tsakanin NAJEEBA da yayunta, ihu take su saketa sun tatare sun riketa sai tirjiya take ja hakan ke sakawa suke kara matsowa waje ga hannunta da Ummulkhair ke ta kokarin daurewa sunna mata ihun ta tsaya ta tsaya aman firrr ta ki idonta ya rufe ji take baki faya zuciyarta ke son tsayawa idan har bata janyo makoloton yarinyar cen ba

Police din ne ya umarci su saketa, dan kuwa su sunna wajen nan dan su hanna du wata fitina da shigar du wani fitinane ko namiji, sai gashi yau ranar farko an fara a haka? Sunna tunanin hutu ne ya same su ashe dai zasu motsi motsi na arziki?

Zahrau ta ce" ba zaka gane ba, ka bamu hanya mu koma gida da ita idan muka saketa mu muka san wa muka saki"

Irin jarumin nan, sannan yana so su gane shi ko zuwa gaba dan idan ana son tsaro su nemi sunnansa a masarautar ya ce" Gimbiya ki yi hakuri ku saketa , mun san aikinmu zamu iya da komai"

Zahrau gannin Yaya Dayabu yana tahowa da wani irin sauri sai ta saki Najeeba, domin kuwa ta tabata a irin yanda yake jefa kafar nan tasa idan ya iso su kansu sai sun sha mari dan haka ta shirya karbar nata, ita dai kam ta shiga uku, dama Najeeba sai da ta fada mata yau ta tabata sai an yi rigima domin haka ne idan ta jima bata fito ba takan tarar da an shiryawa fitowarta, shine harda fadin ita kuwa ba zata kula kowa ba

Sunna sasauta mata rikon da wani irin karfi ta yi ciki da police din nan, wanda hakan ya saka SUKTAN kara rintse idannuwansa yana jin bugun zuciyarsa ya karu kashi casa'in, numfashinsa ne ya ringa doka masa da karfi yana fita da sauri, idannuwansa suka kara yin ja a lokacin da ya ga ta daki police din nan da hannayenta uwa uba ciki ta yi da shi wanda hakan ya zo masa a ba zata ya nemi riketa ta damki damtsen hannunta da karfi dan ya samu ya hanna mata ficewa,
Dan daudun nan na nesa kadan yana ta dira yana ihun a saketa ya tare mata matsiyaciyar nan shegiya busashiyar karuwa

Juwa ke daukan NAJEEBA dan da gaske jinni take zubarwa mai mugun yawa aman zuciyar ta shuwa ta tashi, idannuwanta sun gama rufewa sai ta cire makwogwaron karuwar cen

Baki dayansa ya mike tsaye, jikinsa har rawa yake tablette din a hannunsa ya saketa sakamakon gannin da gaske Police din nan so yake ya rungume masa mata ta baya dan ya ci karfinta ya hannata zuwa wajen fadan ita kuwa tana son fin karfinsa, gashi dayan kuwa du yana ta fitar da kutane yana fadin kar wanda ya dawo sai da katin gidan sarautar da za'a buga a rarabawa du wani client dinta
Chapter 104 · 0% Book details