← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 138

Sashe 16

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabanta ne ya fadi jin wai zasu je su yiwa sarki salama, to ita yanzu tsakani da Allah ina ita ina zuwa yiwa sarki salama? Taga dai Zahrau yake so, me zai hana a turata da jakadiyoyi? Walahi tana tsoron haduwarsu da wannan bawan Allahn da ta dasawa sunnan dunkum!

Sai da ta kusan fita ta juyi ta ce" karamar wayarki tana wajen SHAHEED

Wani irin kululu cikinta ya yi kamar wace ta sha abinda zai sakar mata ciki daga jin cewa karamar wayarta na wajen SHAHEED

Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une
Ta fada a fili tana mikewa da gudu ta yi bayi

Bata zane ko'ina ba sai saman WC tana rike cikinta dake juya mata
Bil haki ta shiga gudawa tsabar faduwa da gabanta ya yi da kuma irin yanda cikinta ya juya daga jin wayarta na hannun SHAHEED

Me hadinsa da wayata? Me ya kai wayata wajensa? Na shiga uku Anmy kin kashe ni kin kare, da ya amshi wayar nan gwara ya amshi babar ya rotsara da kas, Anmy kin san neman shari yake a kaina shine kika bashi hanya, wannan tsanata da nake hangowa a idannuwansa shine kika bashi abinda zai idasa tsanar tawa?

Sai da ta gama gudawar zufa na karyo mata ta tsaftace jikinta ta wanke ta fito ta zauna kasa ta kunna babar wayar nata

Wayar na kunnuwa kamar jira ake network ya hau sai ga message rututu

Bata tsaya dubawa ba ta shige wajen Call
Da sauri ta ringa tura message cewar kar a nemeta a numberta airtel ta yarda wayar ne a kirayeta a numberta MOOV

Da sauri take ta tura message din sai da ta gama ta fara sauke ajiyar zuciya a tunaninta ta toshe hanyar kiranta

Wajen message din ta shiga, nan ta fara cin karo da message din samarinta kala daban daban
Ciki kuwa harda masu shaida kata sun kasa hakura sun je gidan ake shaida masu rasuwar yarima ashe dan yayanta ne
Wasu sun tsaya iya gaisuwa
Wasun kuwa cikin ikon Allah ta ringa bin message dinsu tana zaro ido jin sun je har fadar gaisuwa

Bata san lokacin da ta furta" uban wa ya aike ku? Da sunnan wa? Kuka ce wajen wa kuka zo?

Kafafuwanta ta mike ta mayar da kanta baya, gashin kanta du ya bazu saman bed din tana kikifta ido

Cen ta yi tsai da ranta, a hankali ta ce" NAJEEBA shin ubankine da zaki ringa rikicewa dan kawai ya amsar maki waya ko dan kawai ya samu ribar an zo an masa gaisuwa?
Nan Abih ya san kinada samari, Dayabuma haka sun yanka ki ne?

Dago kanta ta yi da irin duban nan na basawa ta juya kwayar idannuwanta masu girman gaske kafin ta furta" ke allura kike cikin ruwa, dole sai kin yi samari zaki iya fitar da gwaninki, bai huce yace ya hada kananun wayoyinmu zai yi bibcike kamar yanda ya saba lokaci zuwa lokaci
Ko kuma dan sirikinsa na son aunty Zahrau zai hada dan ya goge du wata alakarta da wani?

Huci ta furzar ta ce" ke koma menene bashi da hurumi da tarin samarinki! Idan kuwa yauma zai bi ki da kallon kyama da tsanar ne halas kema ai kina da idannuwan!

Haka ta yi ta zama har kusan magarib
Lokacin ne Zahrau ta shigo ta karsa inda take zaune itama ta zauna jikinta a sanyaye

Dubanta ta yi, sai ta ji itama jikin nata ya yi sanyi
A hankali ta dora hannunta saman hannunta na dama ta kara sanyaya muryarta ta ce" idan har kin san bakya so, idan har kin ji bai maki ba, idan har bakya ra'ayin aure ki zauna a gidan sarauta, idan har maganar yanada mata biyu ke kayar maki da gaba har ya kai kina jin ba zaki iya jurewa ba
Dan shiru ta yi kafin ta tsareta da ido ta ce" *Kar ki amince*

Ajiyar zuciya Zahrau ta sauke ta ce" aman sai na ga su Abih sunna murna da hakan, idan na tashi kai tsaye na nuna bana so yaya kike gannin zasu ji a ransu?

NAJEEBA ta yi kara fuskantarta ta ce" kwarai ba zasu ji dadi ba duba da yanzu abinda suka sako gaba burinsu su yi mana aure da daidaya

Hannunta dayan ta riko tana dan murzawa ta ce" to aman ina anfanin ki je ki kasa zama ki dawo? Koda hakuri kikai kika zauna kina shan wahala kina tunanin zasu ci gaba da jin dadin hadin nasu ne?
Hannunta ta kai wajen habarta ta dan dago ta ce" Aunty, baki dayanmu ina mana fatan mu auri mazan da muke so kuma suke son mu
Na tabata su ne zasu fi gannin darajarmu, zasu ji tsoron rasa mu, zasu kula da lamarinmu
Mu kuma na tabata tare da su ne zamu yi hakuri mai inganci, zamu yi biyaya ke aunty mu bautu ba tare da mu kanmu mun ankara cewa vautuwar muke ba cike da farin ciki da nutsuwar zuciya

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" abin ne akiy gigita
Kin ga zinaria yanda take a hakama ta tsane mu ina da na auri ubanta? Kin dai taba gannin mahaifiyarta matar kyankyamin bakin mutun take ita kanta ta cenza daga buzuwa ta koma balaraba dan ta tsanu jinsin baki

Murmushi NAJEEBA ta yi tana lakatar mata hanci ta ce" wannan du bana so su zamo damuwar da zasu hanna ki auren Mai martaba sarkin Agadez
ZULAIHAT da kike magana a gaban idannuwanki idan ubanta na magana tana iya daga kanta ne? To da izinin Allah idan kika auri ubanta ta nuna ba zaku yi zaman lafiya ba dolenta zata yiwa uwarta biyaya dan ba ke ba ko ni nan na zama auntynta
Ta karashe tana dage mata gira guda hakan ya saka Zahrau sakin yar daria tana jan kuncin Najeeba

Najeeba ta yi murmushi ta ce" matarsa kuwa meye hadinki da ita? Idan ita tana kyankyaminki, mijinta kuwa ya ga abin so kuma sai ta yi mamakin bakar fatar nan jinnin shuwa arab ta firgitata a lokacin da mijinta ya zama baya iya yi sai da yar duma dumar Abih
Ta karashe tana mai shigar Zahraun da cakulkuli

Ai kuwa nan suka cakule sunna cakulkuli sunna kyakyata daria kamar ba su ba

Sai da sukai sallah suka ringa shiga wanka

Kayan mak up ta baje saman cafet din dakin Anmy
Cikin nutsuwa ta ringa gyarawa yayun nata fuskokinsa cikin simple mak up mai tafe da tsarin kalar fatarsu daidai da kowace

Nan da nan sirrin tsarin kyansu ya fito
Baki dayansu Lafayar ce suka nanada wace ta sha turaran wuta mai balakin kanshi

Wajen saka alkyabar kuwa NAJEEBA ta yi tsaki ya fi a irga sannan ta dora nata

Yan matan fitowa sukai reras su hudu da su kamar ka sace su ka gudu
Tsayinsu ya kasance da kadan kadan suka fi junna,
Yannayin jikinsu ne ya bambanta da kalar fatarsu dan wata ta fi wata haske, bakin wata ya fi na wata fizga aman fuskarsu kamarsu daya ciki kuwa har irin lebunnansu daya

Jeruwa sukai NAJEEBA ta kashe masu hoto da Iphone dinta suka fito das da su a hoton kamar wasu amaren sarakuna wato gimbiyoyi

Zahrau jinta take cikin nutsuwa cikin alkyabar, dadinta take ji sosai

A haka suka firfito sukaiwa Anmy salama

Message din Ambassador din Niger wanda ke zaune a kani ne ya shigo wayarta cewa ya zo fadar yana zaune da mutane ita kawai yake jura yau ba zai iya baci ba sai sun hadu

Murmushi ta yi bayan ta karanta bata bashi amsa ba, sannan sam ta sha'afa shi din bata masa kashedin kar ya kirayi numberta na Airtel ba, hasalima saka wayar ta yi a jirgi dan bata so a gaban manya ta yi ta samun kira dan ta tabata tana dagawa abin zai zama magana

Sunna tsakar FADA ne, wajen ya dauki hasken fitilu ne ga kuma hasken sarakunnan dake walwali
Wajen a zagaye yake su kuwa su biyu sun tsaya dan nesa sunna zantawa

Tun daga nesa dogarai ke sanar da zuwansu da kirari da komai tamkat su dinma y'ayan sarautar

A hankali ya juyo dubansa wajensu dan gannin shin sun saka alkyabar yanzu ko basu saka din ba?

Gannin sun saka ya saka shi maida dubansa wajen mai martaba
Ga mamakinsa sai ya ga ya fi shi bada hankali kansu
Murmushi ya yi a ransa yana furta ikon Allah

A dazu karara Abih ya nuna masa irin rigimar da ta faru tsakanin Zahraun da tsoron manemin aurenta
Cikin ikon Allah yana buda baki sai ya yi murmushi ya ce" dama ba mijinta babe shi yasa Allah ya kawar da shi daga rayuwarta kafin mai wajen ya iso

Kuma dubansu ya yo kadan gannin sun dakata , sai da ya sha iska ya dan dago hannayensa ya yafito su

NAJEEBA ta tabe baminta a ranta fadi take" irin ga yan gidansan nan, ahi ba zai yi mana magana ba mai dunkum kawai!

Irin yanda suka nemi zubewa kasa dan gaishe da su ya kara birge sarkin garin Agadez
Sai dai sam bai barsu ba ya hanna hakan

Irin yanda du suka layu suka sada kansu daga tsayen da suke ya saka SHAHEED lumshe idannuwansa yana murmushi fadi yake" yanzu mutun yanzu ba mutun ba, dan ya tabata a wajen nan aka jata fada walahi zata kwabe alkyabar nan ne ta nuna hali , shi dai mutun marar kamun kai me ake da shi?

Itama baki take yatsinawa daga kasa tana fadin" na tsani raini, na tsani Raini!

Tun da suka tsayan yake kallon Zahrau,
A hankali ta dago dubanta ta sauke saman fuskarsa
Irin murmushin da ya sakar mata a bayanne yake shi ya sakata dan saka idannuwanta cikin nasa kafin ta lumshe su ta kawar da su a hankali tana jin zuciyarta na dokawa
Ko ba komai ya iya kallo
Ta furta a kasan zuciyarta

Dogarin dake cen nesa rike da sakonsu ya yafito
Yana karasowa cike da bada umarni a tausashe ya furta" idan su gimbiya sun koma bangaren GIMBIYA uwa, ka bi su da sakon nan

A hankali ya yi maganar dogarin ne ya ringa takadi yana furta su Gimbiya sun gode da sauransu
Chapter 16 · 0% Book details